𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah...
Malam muna godiya Allah ya sa a mizani... Tambayata ita ce dan Allah wanne
alamomi mace za ta duba ta gane jinin haila da na cuta... Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salámu Wa Rahmatullah.
Amin na gode. 'yar'uwa jinin cuta shi ne jinin da ke zubowa mace ba a lokutan
da ta saba ganin al'adarta ba, saboda wani rashin lafiya, ko kuma daga wata
jijiya. Amma shi kuwa jinin haila jini ne na ɗabi'a
da ke zubowa mace a cikin ranakun al'adarta na wata-wata.
Ana iya bambance tsakanin jiinin
haila da na cuta ta hanyoyi kamar haka
Jinin Haila jini ne mai duhu,
kuma yana da shinshine maras daɗi
ko bashi-bashi, a wasu lokutan yana yi wa mace raɗaɗi a farkon lokacin
zuwansa.
Shi kuwa jinin cuta ba shi da
duhu, kalarsa jazur ne, kuma shin-shinensa ba ya bashi-bashi .
Haila tana wajabta hana yin
sallah da azumi, da saduwa da iyali, kuma tana wajabta yin wankan tsarki idan
mace ta tabbatar ta sami tsarki. Saboda faɗin
Allah Maɗaukakin
sarki a Alqur'ani cewa
وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ
أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ
فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ
التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ
Kuma suna tambayar ka game da
haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma
kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga
inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu
tsarkakẽwa.
(Suratul Baqara aya ta 222).
Da kuma maganar Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam ga Faɗima
'yar Abu Hubaish cewa: "Idan haila ta zo maki, to sai ki dakatar da yin
sallah, idan kuma hailar ta ɗauke
sai ki yi wanka kuma ki yi sallah". Albukhariy (320), Muslim(333).
Amma shi kuwa jinin cuta, jini ne
gurɓatacce da ba ya
hana yin dukkan ibadoji, kuma ba ya wajabta yin wankan tsarki idan ya ɗauke. Duk wanda jinin
cuta ke zuwa mata ana hukunta ta ne a matsayin mai tsarki, sai dai dole ne sai
ta riqa yin alwala a lokacin kowace sallah, ba za ta yi alwalar ba sai lokacin
sallar ya shiga.
Allah Ta'ala ne mafi sanin
dai-dai.
Dr. Jamila zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.