Ticker

6/recent/ticker-posts

Wace Sallah Ce Ta Fi Yawan Lada?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam Wai wace sallah ce ta fi yawan lada?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Dukkan ayyukan ibada da Allaah ya yi umurni da su suna da falala da lada idan aka yi su a bisa ƙaidojinsu da sharuɗɗansu. Amma a bayan Tawheed da kyautata Aqeedah, sallah ita ce mafificiya daga cikin dukkan ayyukan da ake yi da gaɓoɓi. Shiyasa aka fara ambaton ta a cikin Hadisin Rukunnan Musulunci.

Sallah ita ce kaɗai aikin da malaman Salaf suka yi ittifaƙi a kan cewa: Duk wanda ya bar yin ta haka nan kawai da gangar saboda lalaci, ko da ba tare da jayayya ko musu a kan wajibcin ta ba, ya kafirta. Domin ita ce bambanci a tsakanin musulunci da kafirci da mushirikanci.

Sallolin Farillar nan guda biyar da Allaah ya ɗora wa bayinsa a cikin kowane yini da dare sun fi falala da lada a kan duk waɗanda ba su ba daga cikin sallolin nafiloli na ‘rawaatib’ da waɗanda ba ‘rawaatib’ ɗin ba, kuma daga cikin waɗanda akwai dalilin da ya sa ake yin su da waɗanda ba su ba.

A cikin sallolin farilla guda biyar kuma Sallolin Asubah da La’asar sun fi sauran alkhairi da falala, saboda Hadisai da suka zo musamman a kan su. Sannan kuma Sallar La’asar tana da fifiko na musamman ita ma saboda ya tabbata a cikin Hadisai Sahihai cewa ita ce ‘As-Salaatul-Wustaa.’

Ita ma Sallar Jumma’ah da ake yi a ranar Jumma’a tare da jama’a a bayan kammala sauraron huɗubobi guda biyu daga liman tana da falala a matsayinta da falalarta na idin mako-mako. Musamman kuma ga wanda ya kula da ƙaidoji da ladubbanta, bai tozarta komai daga cikin hakan ba.

Sallar Farilla a masallaci tare da jama’a a bayan liman ta fi falala a kan wacce aka yi ta a inda ba masallacin ba, ko da kuwa tare da jama’a ne. Kuma sallar da jama’a suka fi yawa a cikinta ta fi wacce jama’a suka yi kaɗan a cikinta. Haka ma wacce aka yi ta a masallacin da ya ke nesa ta fi wacce aka yi a masallaci na-kusa, sai in da wani dalili.

A cikin Nafiloli kuwa Sallolin Nafila na ‘Rawaatib’ sun fi waɗanda ba su ba, saboda Hadisai da suka zo masu yawa a kan bayanin falalarsu cewa: Suna zama dalilin samun ginin gida na musamman a cikin Aljannah. Baya da kasantuwar suna da alaƙa da Sallolin Farilla ko dai kafin su, ko kuma a bayan su.

Ta wata fuskar kuma Salloli irinsu Sallar Janaza ko Sallar Idi ko Sallar Khusufi ko Sallar Roƙon Ruwa da makamantansu suna da falala da lada fiye da waɗanda ba su ba. Domin yadda aka keɓance su da wani yanayi ko hali na musamman, baya ga zuwan Hadisai Sahihai da suke nuna wajibcin waɗansu daga cikinsu.

Amma sauran Nafiloli na ganin-dama da neman ƙarin lada kuwa, sallolin da aka yi a cikin gida sun fi waɗanda aka yi su a cikin masallaci nesa ba kusa ba. In ban da Sallar Tarawihi ko Asham da ake yi a dararen watan Azumin Ramadan mai albarka, saboda riwayoyin Hadisai Sahihai da suka zo a kan ta.

Haka nan dai Sallolin Nafila na dare sun fi na rana falala, saboda an fi samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali da nisantar sharrori irin na riya a cikin su. Kuma waɗanda aka yi su a ƙarshen dare sun fi waɗanda aka yi su a farkon daren falala, saboda dacewar su da lokacin saukowar Ubangiji Ta’aala zuwa saman duniya, da kuma dacewa da lokacin halartowan Mala’iku.

Sannan kuma Sallar Wutri da mutum yake cike adadin raka’o’in sallar darensa da ita ta fi dukkan sallolin falala, musamman dayake Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya damu da ita sosai, kuma bai taɓa barin yin ta ba, ko a halin tafiya ma balle a halin zaman gida. Shiyasa waɗansu malamai suke ganin ita ma farilla ce!

Ta wata fuskar kuma, sallar da aka daɗe a tsaye ana karatu a cikinta ta fi falala a kan wacce ba haka ba. Shiyasa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake daɗewa a tsaye a cikin sallarsa da dare har ƙafafunsa su kumbura, domin kawai ya nuna godiya ga Ubangijinsa (Tabaaraka Wa Taaala) da ya yi masa gafarar dukkan zunubansa na-gaba da na-baya!

Amma kuma bai ɗora wa sauran musulmi yin hakan ba. Sai dai ya umurce su da yin iya abin da suke iyawa kawai daga cikin waɗannan ayyukan. Saboda kasantuwar shi kamar yadda Allaah Maɗaukakin Sarki ya siffata shi ne:

لَقَدۡ جَاۤءَكُمۡ رَسُولࣱ مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ عَزِیزٌ عَلَیۡهِ مَا عَنِتُّمۡ حَرِیصٌ عَلَیۡكُم بِٱلۡمُؤۡمِنِینَ رَءُوفࣱ رَّحِیمࣱ

Duk abin da ke ƙuntata muku yana yi masa tsananin wahala, mai kwaɗayin alkhairi ne gare ku, kuma ga muminai mai tsananin tausasawa ne mai tausayawa. (Surah At-Taubah: 128).

Allaah ya ƙara mana ƙoƙari da kafewa a kan ɗa’a.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaah Assalafiy

08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments