𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Kafin na fara Al'adata, nakan
lura da zubar jini/ruwa mai launin kalar kasa (brown discharge) Kuma Yana kaiwa
tsawon kwanaki biyar, Bayan nan kuma sai jinin Al'ada ya biyo. Jinin Al'adar
yana daukar tsawon kwanaki takwas bayan kwanaki biyar na farko. Nakan yi Sallah
cikin kwanaki biyar ɗin
amma sai nake shakkun yin azumi da sallah cikin wa'ennan kwanaki biyar ɗin na farko ko a'a? Don
Allah ka bani shawara, Allah ya saka da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan cikin kwanaki biyar ɗin da kike ganin ruwa mai
launin kasa (brownish discharge) ba haɗe
yake da kwanakin da kike ganin jini hailar ki ba, toh ba ya ɗaukar hukuncin jinin
Al'ada, don haka zaki yi sallah cikin wa'ennan kwanakin biyar da azumi.
Amma kuma zaki jaddada alwala ga
ko wani sallah idan zaki yi. Saboda ya na ɗaukar
hukunci ne daidai da na fitsari, amma ba na Al'ada ba.
Kenan haƙan baya nufin cewa
bazaki iya yin sallah ba ko azumi, amma zaki rika yin alwala duk sanda kika
tashi yin sallah, har sai lokacin da wannan ruwan ya yanke, kamar yadda
hukuncin jinin istihaadah (jinin cuta/non-menstrual bleeding) yake ɗauka.
Amma idan wa'ennan kwanaki biyar ɗin haɗe suke (bima'ana babu
wani tazaran lokaci a tsakani) da kwanaki takwas da kike yin al'ada, toh
hukuncin wannan ruwa mai launin kasa-kasa (brownish discharge) ɗin, daidai yake da na
jinin al'ada, don haka bazaki yi sallah ba ko azumi cikin wa'ennan kwanakin.
Haka zalika, a karshen Al'adar
ki, fitar ruwa mai launin kasa (brownish), ko me fatsi-fatsi (yellowish
discharge), baya ɗaukar
hukuncin jinin Al'ada, amma ya na zuwa ne karkashin hukuncin istihaadah (jinin
cuta), don haka zaki rika yin tsarki ki jaddada alwala akan ko wani sallah idan
zaki yi.
Sannan zaki yi sallah da azumi da
kuma rayuwar aure da mai gida. Dalili kuwa shi ne hadithin Ummu Atiyyah
كنا لا نعد الكدرة والصفرة بعد الطهر شيئا
" أخرجه البخاري في صحيحه وأبو داود وهذا لفظه).
Ki duba: Majmoo’ Fataawa na
Shaykh Ibn Baaz, 10/207
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.