𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Don Allah tambaya nake yi, mu biyar
mamanmu ta haifa amma biyu daga cikinmu ta hanyar aure aka same su, uku kuma ba
ta hanyar aure aka same su ba, shin suna da gadonta ko ba su da shi? Kuma gashi
ta rasu da bashi da yawa a kanta kuma ba mu da hanyar biya mata shi, domin kuɗin yana da yawa akalla
yakai dubu ɗari
biyu. Don Allah mafita muke nema.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam. Idan mace tayi cikin shege kuma ta haifi
ɗa, daga baya ta
rasu, ɗan zinar da
ta haifa zai gaje ta, saboda Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratun Nisa'i aya
ta (10) ya yi wasiyya a bawa ƴaƴaye gado, ɗan
zina kuma yana cikin jerin ƴaƴayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje
ta, don haka babu bambanci a cikinku tsakanin waɗanda
aka haifa ta hanyar aure da kuma waɗanda
aka samu ta hanyar zina a wajen rabon gadon mahaifiyarku.
إِنَّ
الَّذِينَ يَأْكُلُونَ أَمْوَالَ الْيَتَامَىٰ ظُلْمًا إِنَّمَا يَأْكُلُونَ فِي بُطُونِهِمْ
نَارًا وَسَيَصْلَوْنَ سَعِيرًا
Lalle ne, waɗanda
suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu,
kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani. (Suratul Nisa'i aya ta 10)
Ba'a raba gado sai an fara biyawa mamaci bashinsa, don haka
koda duk abinda ta bari zai ƙare dole ku biya bashin kafin a raba
dukiyar, kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Suratun Nisa'i aya ta (11).
يُوصِيكُمُ
اللَّهُ فِي أَوْلَادِكُمْ لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنثَيَيْنِ فَإِن كُنَّ نِسَاءً
فَوْقَ اثْنَتَيْنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَ وَإِن كَانَتْ وَاحِدَةً فَلَهَا
النِّصْفُ وَلِأَبَوَيْهِ لِكُلِّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا السُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن
كَانَ لَهُ وَلَدٌ فَإِن لَّمْ يَكُن لَّهُ وَلَدٌ وَوَرِثَهُ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ
الثُّلُثُ فَإِن كَانَ لَهُ إِخْوَةٌ فَلِأُمِّهِ السُّدُسُ مِن بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصِي
بِهَا أَوْ دَيْنٍ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ لَا تَدْرُونَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ لَكُمْ
نَفْعًا فَرِيضَةً مِّنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا
Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da
rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu
daga kashi uku ɗin
abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma
iyãyensa biyu kõwane ɗaya
daga cikinsu yanã da ɗaya
daga kashi shida ɗin
abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe
bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã
da sulusi (ɗaya daga
cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana
da sudusi (ɗaya daga
cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da
'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa
daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima. (Suratul Nisa'i aya
ta 11)
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.