Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Dan Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene hukuncin shayar da Ɗan da aka samesa ba ta hanyar shari'a ba - wato Ɗan Zina ga ijtima'in (haduwar musulmai)? Kuma ga wa ake danganta sa kuma waye yake zamantowa waliyyinsa? Za'a iya naɗa shi alkalanci idan ya cancanci hakan? Shin zai aura daga musulma (wacce take 'ya da aka same ta ta hanyar Shari'a)? A ina za'a binne shi idan ya mutu? Shin (bayan mutuwarsa) za'a yi masa Sallah? A wasu lokuta akwai masu kashe 'ya 'ya lokacin haihuwa, to shin Menene hukuncin masu aikata hakan?

𝐀��𝐒𝐀❗️

Yaron da aka Haifa ta hanyar zina idan mahaifiyarsa ta kasance musulma ce hukuncinsa kamar hukuncin sauran yaran musulmai ne, musulmai za su tarbiyyantar dashi za su kyautata gare shi, Domin akansa bashi da wani zunubi na mahaifiyarsa ko kuma zunubin Wanda yayi zina da mahaifiyarsa: Wata rai bata ɗaukar laifin wata rai

قُلْ أَغَيْرَ اللَّهِ أَبْغِي رَبًّا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيْءٍ وَلَا تَكْسِبُ كُلُّ نَفْسٍ إِلَّا عَلَيْهَا وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ

Ka ce: ''Shin wanin Allah nake nma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?'' (Suratul An'am aya ta 164).

Laifin zinar da sukayi yana kansu ba shi ba. Domin shi amana ne tsakanin musulmai, yana kansu su tarbiyyantar dashi tarbiyyar musulunci, kuma su kyautata masa har ya kai lokacin samartakarsa ya girma, Idan ya balaga hukuncinsa kamar hukuncin sauran musulmai ne, yana ga daular musulunci ta tsayu da wannan al'amari kuma ta taimaka akan wannan al'amari har sai an baiwa waɗannan yara kariya har su tsaru daga cutarwa da kisa.

Amma kasancewarsa kashe shi bayan haihuwa ko kuma yunkurin kashe sa yayin haihuwa, aikata hakan yana daga cikin munanan ayyuka kuma baya halatta, Duk Wanda ya aikata hakan kuwa to ya dorawa kansa laifuka biyu wato laifin zina ga kuma laifin kisa ba tare da hakki ba. Muna neman tsari daga wajen Allah.

Abinda yake wajibi shine kada a kashesa sai dai ma abasu kariya ta hanyar damka su a gidan raino ko kuma asamu mace musulma da za ta iya daukar nauyin shayar dashi, da kyautata masa da tarbiyyantar dashi, zayyi karatu tare da sauran yaran musulmai kuma a garin musulmai. Za'a yi kokarin fuskantar dashi izuwa ga aikata Alkhairi, a duk lokacin da ya tsayu da kafarsa yakai lokacin balaga, kuma ya dabi'antu da kyawawan dabi'un mutanen kirki, to ya halatta ya zamo cikin masu kira ga Addinin ALLAH.

To ya inganta ya kasance alkali, ya kasance tsarki, kuma ya kasance miji ga ragowar wanda zai iya ɗaukar nauyin su daga cikin musulmai, bayi da wani zunubi, zunubin sa yana akan wanin sa bashi ba, abunda ke akansa kawai tsayuwa idan ya kai ya tsayu akan umurnin ALLAH, kuma yaji tsoron abunda ALLAH ya haramta, duk lokacin da ya gyaru (Ya daidaitu akansa) ya tsayu akan sa, hukuncin sa ya zamo irin na sauran musulmai, yana gare shi abunda ke gare shi, yana akansu abunda ke akansu na hakkoki.

Idan ya mutu yana karami za'a abinne shi a makabartar musulmai, matukar dai mahaifiyar sa musulma ce, za'a binne shi a makabartar musulmai, za'a yi masa wanka ayi masa sallah kamar sauran yaran musulmai, ba ya halatta ayi sakaci da shi, ko tozartar da shi, za'a ambace sa da sunan da ya dace kamar, Abdullahi, abdurrahman, ko Abdul Malik, da kuma sauran sunaye, Muhammadu, Zaidu, babu laifi a sanya masa Muhammadu, Zaidu ai sunaye ne daga sunayen da suka dace, ko ace masa Ibnu Abdullahi, za'a jinginar zuwa ga Abdullahi ko Abdul Malik, dukkan mutane bayin ALLAH ne !

Tambaya zai auri waye?

zai aure daga musulmai shi musulmi idan ya shiryu (ko da ɗan zinah ne) mahaifiyar sa ba ta cutar da shi ko wanda yayi zina da ita !

Tambaya, daidai ne shin in wannan yaron ya mutu kuma gashi an jahilci ba'a san waye ba?

za'a rufe shi tare da musulmai, godiya ta tabbata ga ALLAH, ALLAH shi zai jiɓinci sakamakon hisabin sa

Tambaya zai iya jiɓintar alkalanci?

Amsa eh zai iya alkalanci da wasun sa.

Sheikh Bin Baz (ALLAH yayi masa Rahma)

📒المصدر

📙الشيخ ابن باز رحمه الله.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments