𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Tana ta tsammanin zuwan hailarta har kusan minti goma kafin a sha-ruwa amma ba ta gan shi ba. Sai da ta gama shan ruwa kawai sai ga shi! To, yaya matsayin azuminta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Al-Bukhaariy da Muslim da
As-Haabus Sunan Al-Arba’ah da sauran malaman hadisi duk sun riwaito da lafuzza
makusanta da juna - wannan lafazin At-Tirmiziy ne, kuma ya hassana shi - daga
A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce
كُنَّا نَحِيضُ عَلَى عَهْدِ
رَسُولِ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - ثُمَّ نَطْهُرُ فَيَأْمُرُنَا
بِقَضَاءِ الصِّيَامِ وَلاَ يَأْمُرُنَا بِقَضَاءِ الصَّلاَةِ.
Mun kasance muna yin haila sannan muna samun
tsarki a zamanin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sai
kuma ya umurce mu da rama Azumin, amma ba ya umurtan mu da rama sallar.
Daga wannan hadisin da masu kama
da shi ne malamai suka fitar da hukunce-hukunce kamar waɗannan
1. Bai halatta mace mai haila ko
mai nifasi (jinin haihuwa) ta yi azumi ko sallah ba a lokacin da jinin ke zubo
mata, kamar yadda bai halatta ta yi sallah a wannan halin ba.
2. Idan kuma ta yi azumin ko
sallar a haka to ta yi laifin da za a rubuta mata zunubi a kansa, kuma azumin
ko sallar ba su inganta ba, kuma ba za a karɓe
su daga gare ta ba.
3. Wajibi ne matar da haila ta zo
mata a cikin yinin azumi ta dakatar da cigaba da azumi da sallah, kuma ta rama
azumin a bayan Ramadan, amma ba za ta rama sallah ba.
4. Wacce ta samu tsarki daga
haila da ranar azumi, to bai zama dole a kanta ta kame baki daga cin abinci ko
abin sha ba, amma dai wajibi ne ta rama wannan yinin.
5. Idan mace ta yi tsarki kafin
fitowar alfijir na-gaskiya ko da kuwa da ƙiftawar ido ne, to wajibi ne ta yi niyyar
azumin wannan yinin, ko da ba ta yi wanka ba sai a bayan alfijir ɗin.
6. Haka kuma idan haila ta zo wa
mace kafin faɗuwar
rana ko da da ƙiftawar ido ne, to azuminta na wannan yinin ya ɓaci, kuma dole sai ta rama
shi.
7. Idan ta ji motsi ko alamun
fitowar hailar amma dai jinin bai fito ba sai a bayan faɗuwar rana, to azuminta ya yi. Babu ramuwa a
kanta.
(A duba: Tamaamul Minnah: 2/168-169)
Allaah ya ƙara mana fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Turo tambayar ka ta WhatsApp
number, banda kira ko tambayar gaggawa. 08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.