Zan Iya Yi Ma Mijina Karya Dan Na Samu Saukin Saduwa Da Shi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalama alaikum Shin Inada laifi Dan na yi karya wa miji na bani da Lfy Dan karda Ya kusanceni kullum yana zuwa da bukatarsa baya tausayamin?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa,alaikumussalam.

    Yana daga cikin riqe alqawarin aure, shi ne biyawa miji buqatansa, a duk lokacin da ya nemeki, koda kina al-ada, za ki biyamar buqata amma banda saduwa ta farji ko dubura domin haramun ne!!!

    Sedai kinemi shawaran shi, idan yanada hali ya qara aure! Idan kuma baida hali, kekuma baza ki iya juran yadda yake miki ba, za ki iya neman ya sauqaqe miki. Seki biyashi sadaki yayi wani Auran.

    Amma idan kikayi Qarya tofa mala'iku zasu hau aikin su na tsinuwa. Ina dai baki shawara ki jure kiyi hakuri da yanayin sa, kiriqa mar fatan samun kuɗin Qara aure, idan kika quntata har zina ze fara idan ba ALLAH ne ya shirye shi ba, daganan seya ebo muku cuta.

    Sannan karki biye Shaiɗan,  soyake ya rabaki da mijin ki. Sannan alheri ne dan ya nemeki alamar kinsamu karbuwa a wajen sa, kuma muna miki tsammanin samun yardan ALLAH. Sedai hakan baze hana ki dan shawarceshi daya riqa dan sassautamiki, amma kinema a yayin yadda ya dace, kada kiyi yadda ze fusata, har ya Qaurace miki sama da yadda baza ki iya jura ba!!!

    sannan mazaje yanada kyau ku gane cewa, yawaita jima'i batare da sauran bautan ubangiji ba, hakan yana nuna alamace irin ta rayuwan dabbobi, dan suma aikin su ke nan, suci suyi jima,'i su kwanta..... Yawaita Jima'a yakan iya Rage qarfin ma'aurata, idan ka kasance muzakkari to kadage ka Qara Aure matuqar kanada hali!! ida bakadashi kuma ka riqa hikima, wajen saduwan kar-ka yawaita saduwa da ita ta farji, ka riqa biya buqatunka ta sauran Sassan jikinta banda Dubura dan haramun ne!

    Allah ta'ala yasa mudace.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.