𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salam, Ina Rokon Allah ya kare mana malam tare da iyalansa
malam Allah yasa daga cikin yayanka a samo wanda zai gaji taimakon da kake
amin. Malam nine nayi karyar mafarkin Annabi shin meye hukuncina kuma zan iya
tuba? Allah ya bada ikon ansawa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaykumus Salam, Ina rokon Allah ya shirya mana zuri'armu
duka, babu shakkah Karya tana daga cikin manyan aibukan harshe, it ace kuma
matattarar kowane sharri.
Har ma Allah (swt) a cikin Alqur'ani Yana Cewa
إِنَّمَا
يَفْتَرِي الْكَذِبَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْكَاذِبُونَ
Abin sani kawai waɗanda
ba su yin ĩmani da ayoyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata. (Suratul Nahl aya ta 105).
Bayan Haka Imamu Bukhari da Imamu Muslin sun Ruwaito wani
hadisi wanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Ke gaya mana cewa karya takan
kai mutum a wuta.
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa, “Ku kiyayi
karya, domin ita karya tana jan mutum zuwa Saɓon
Allah, shikuwa Saɓon
Allah yana kai mutum zuwa ga wuta, hakika mutum ba zai gushe ba
yana karya har sai an rubuta shi a wajen Allah cewa shi
makaryaci ne”. (Imamu Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Qarya babban zunubi ce wadda ayoyi da hadisai sukayi magana
akan haramcinta da kuma narkon azabar da za ayiwa makaryaci. Musamman ma yiwa
Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) Qarya.
An Ruwaito hadisi Cewa, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam)
yana Cewa, “Duk wanda ya yi mini karya da gangan, to ya tanadi mazauninsa a
cikin wuta” (Bukhari da Muslim).
A wani hadisin kuwa Cewa, yayi “Duk wanda ya fadi mafarkin
karya, to za a tilasta masa daya
daura tsakanin siraran gashi guda biyu, kuma ba zai taɓa iyawa ba”, (Bukhari ne
ya ruwaito shi).
Hakika ka aikata babban kuskure wanda kuma da ka mutu a
Cikin wannan halin da zaka tarar da abinda baka so a gobe qiyama.
Don haka ka tashi tsaye wajen tuba ga Allah (swt) domin
Allah yana Cewa
وَمَا
كَانَ اللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنتَ فِيهِمْ وَمَا كَانَ اللَّهُ مُعَذِّبَهُمْ
وَهُمْ يَسْتَغْفِرُونَ
Kuma Allah bai kasance Yana yi musu azaba ba alhali kuwa kai
kana cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azaba ba alhali kuwa suna yin
istigfari. (Suratul Anfal ayata 33).
Ina Rokon Allah ya yafema ya yafe mana.
Daga karshe, muna jan hankalin Masu ganin Rubutu game da
Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) suna haɗawa
ba tare da sanin sahihancin sa ba. Domin Shima Yiwa Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam) Karyane.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.