Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Daina Son Amaryasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam akwai wani ya kira ni yake cewa: Yayi aure ne asali suna son juna da matar, amma iyayenta kuma ba sa son abun, to itama yarinyar tana masa wasu halaye, har yakai idan yana mata faɗa tana ramawa, ko ta masa tsaki ma. Ana hakan ne sai ya wayi gari yaji gaba ɗaya ya daina sonta ko kaɗan. Malam mene ne mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan'uwa, zai yi kyau su bi matakan da Allah ya faɗa a Suratun-Nisa'i na matar da ta butsare, ta yadda zai yi mata wa'azi, idan taƙi ya ƙaurace mata, idan hakan bai yi amfani ba sai a kira zaman sulhu, a samu wakilai daga ɓangaren matar, wasu daga bangaren mijin, idan har sun yi nufin gyara Allah zai datar dasu.

Idan har waɗannan matakan ba suyi amfani ba, suna iya rabuwa, Allah kuma mai iko ne ya azurta kowa daga falalarsa, ya bata wadda za suyi daidai, shi ma ya samu wadda za ta iya zama dashi, kamar yadda aya ta 130 a Suratun-Nisa'i ta tabbatar da hakan

وَإِن يَتَفَرَّقَا يُغْنِ اللَّهُ كُلًّا مِّن سَعَتِهِ وَكَانَ اللَّهُ وَاسِعًا حَكِيمًا

Kuma idan sun rabu, Allah zai wadatar da kowanne daga yalwarSa. Kuma Allah Ya kasance Mayalwaci, Mai hikima. (Suratul Nisa'I aya 130)

Hakuri shi ne ginshiqin zaman aure, sai dai idan mushkiloli suka yi yawa, aka kasa yi musu hanci, to babu zaman doya-da-manja a Musulunci. Allah ya shar'anta saki ne domin tunkuɗe cuta daga ɗaya daga cikin ma'aurata, ko kuma su duka.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments