𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, Malam don Allah mutum ne ya saki matarsa
har saki (3) a lokuta daban-daban, to sai wani bawan Allah yazo ya aureta,
bayan ya aureta sai wata matsala ta shiga tsakaninsu kuma ya saketa amma kuma
ko sau ɗaya bai sadu
da ita ba, to, yanzu malam ko wancan tsohon mijin nata zai iya mayar da ita,
tunda ga shi ta yi aure amma saduwa ce kawai ba ayi da ita ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam, in har basu sadu ba, to bai halatta ta
auri tsohon mijin nata ba, saboda lokacin da matar Rifa'ata ta auri wani bayan
mijinta ya sake ta, ta so ta rabu da mijinta na biyun domin ta koma wajan na
farkon kafin su sadu, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya hanata, inda yace
mata: "Dole sai kin ɗanɗana daɗinsa, shima ya ɗanɗana daɗinki"_,
kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba (5372), wannan sai ya nuna
cewa aya ta (230) a Suratul Bakara ba aure kawai take nufi ba, tana nufin aure
haɗe da saduwa su ne
suke halatta mace ga mijinta na farko, saboda aikin Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam) da maganarsa su ne suke fassara Alkur'ani.
فَإِن
طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُ مِن بَعْدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُ فَإِن
طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَن يَتَرَاجَعَا إِن ظَنَّا أَن يُقِيمَا حُدُودَ
اللَّهِ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, ba ta halatta a gare
shi, daga baya, sai ta yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sabon
mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, babu laifi a kansu ga su koma wa (auren)
jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa za su tsayar da iyakokin Allah, kuma
waɗancan dokokin
Allah ne Yana bayyana su ga mutane waɗanda
suke sani. (Suratul Bakara aya 230)
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀��𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.