Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Idan Mijin Ya Rungume Matarsa Tana Cikin Idda Za A Iya Ɗaukar Wannan A Matsayin Kome?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. An yi mana sihiri ne aka raba ni da mijina. Ina cikin idda bayan na yi jini biyu sai ya riƙa zuwa wurina, saboda a gidansa nake yin iddar. Yau da gobe sai muka fara rungumar juna (romance) amma ba mu kai ga saduwa ba. To, wai shin da wannan ɗin auren ya dawo, ko sai ya furta da bakinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam. Da farko, miji yana da damar ya dawo da matarsa wacce ya sake ta da sharuɗɗa guda uku

1. Ya zama sakin ba na ƙarshe ba ne, watau ya zama saki na-ɗaya ne ko kuma na-biyu.

2. Ya zama matar ba ta gama iddarta ba, watau ba ta yi wanka daga hailarta ta-uku ba a bayan sakin.

3. Ya zama manufarsa na dawo da ita shi ne: Kyautata zamantakewa, ba wai cutar da ita ta hanyar tsawaita lokacin iddarta ba.

A asali yana dawo da ita ne da magana, kamar yadda aka ɗaura masa aure da ita, kuma ya iya sakin ta da magana. Watau kamar ya ce: ‘Na dawo da ke.’ Ko: ‘Daga yau kin dawo ƙarƙashin iko na, ko dai wata magana makamanciyar wannan.

Amma idan mijin ya rungume ta, ko ya sumbance ta, ko ya tara da ita a halin tana cikin iddar, to ko za a iya ɗaukar wannan a matsayin kome? Malamai sun saɓawa juna akan haka.

Abin da Al-Imaam Maalik da Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah da Al-Allaamah Al-Uthaimeen (Rahimahumul Laah) suka zaɓa shi ne: Ya halatta a yi kome ta hanyar aiki kamar yadda ake iya yin sa ta hanyar magana. Saboda Allaah Ta’aala a cikin Alqur’ani ko Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba su ƙayyade shi da magana kaɗai ba. Baya kuma da samun Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) masu yawa da suka ga halaccin yin komen ta hanyar aiki. Don haka, idan miji ya tara da matarsa wadda take cikin iddan sakin da yake akwai kome a cikinsa tare da nufin kome, to wannan ya nuna cewa ya dawo da ita ke nan, ko da kuwa bai furta da bakinsa ba.

A taƙaice dai abin da ya kamaci wannan baiwar Allaah mai wannan tambayar shi ne ta yi ƙoƙarin sanin manufarsa da wannan haɗuwar, don kar ta zama abar morewa da jin daɗi kawai ba tare da ya yi nufin dawo da ita ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments