Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Auri Wadda Ba Ya Iya Jima'i Har Suka Rabu, Shin Za Ta Yi Idda?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam, wani bawan Allah ne ya auri ƙanwata, sai daga baya muka gane ya ha'ince mu sakamakon rashin mazantaka da ba ya dashi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya sake ta, shin malam za ta yi idda ne? Don babu wata mu'amalar aure da ta taɓa shiga tsakaninsu.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, mutuƙar ba su taɓa kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta (49) a Suratul Ahzab ta yi bayanin hakan

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا

Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! idan kun auri mũminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi kuma ku sake su saki mai kyau. (Suratul Ahzab aya 49)

Amma in har yankar kaciyarsa ya ɓuya a farjinta ya wajaba ta yi idda, zai yi kyau kuje wajen Alƙali saboda ya tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments