Ticker

6/recent/ticker-posts

Wacce Mace Ya Kamata Na Aura?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, ina neman shawara, wacce mace ya kamata na aura a matsayina na ɗan shekara 28, ƴar shekara nawa tafi dacewa da ni a yanzu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, ka auri mai addini, wacce idan ka kalleta za ta burge ka, mai sonka, mai nutsuwa da sanin ya kamata. Yana da kyau ka sami matar da ka fi ta kuɗi da ilimi, ta fi sonka, ta kuma fi ka ƙananan shekaru, ka tsaya ka kalleta da kyau kafin ka aureta, kada kayi gaggawa.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments