Ticker

6/recent/ticker-posts

Video Call Na Tsaraici

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaikum, Malam idan na Yi tafiya zan iya Kiran matata ta WhatsApp ta cire kayanta mu Yi waya, na ganta, saboda na samu saukin sha'awar da take damuna?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda kamfanin WhatsApp da hackers da Injiniyoyi in sun so za su iya ganinku, Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa: "Ka kiyaye al'aurarka in ba ga matarka ba da kuma abin da damarka ta mallaka", Kamar yadda Abu dawud ya rawaito a hadisi ingantacce.

Kasancewar What'sapp babu sirri, Video call na tsaraici ya zama haramun, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance ko bukata zai biya yana yin nesa da sahabbansa, da inda mutane ba za su gan shi ba, Kamar yadda Ibnulkayyim ya ambata a Zadul ma'ad 1/171.

An rawaito cewa Yana cikin damuwar Nana Fadima ranar da za a dauke ta a Makara, saboda maza za su iya hangarta a rufe cikin likafani, Kamar yadda Hakim ya rawaito a Mustadrak da Abu Nu'aim a Hilya.

Dalilan da suka gabata suna nuna cewa Haramun ne mutum ya cusa kansa wurin da za a iya tsikayo a al'aurarsa in ba wuraren lalurar da Sharia ta togace ba.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments