Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Rike Hannun Budurwata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ya hukuncin wanda ya rike hannun wata mace kuma ba matarsa bace, amma budurwarsa ce?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam, bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance ba ya Musafaha (haɗa hannu) da mata yayin da zai yi mubaya'a dasu, yana yi musu mubaya'a ne da magana kamar yadda ya tabbata a hadisi. Taɓa hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga zina saboda yana tayar da sha'awa. Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a aya ta (32) a Suratul Isra'i

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta mũnana ga zama hanya.

Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya bi son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments