Ticker

6/recent/ticker-posts

Kiss Ta Hanyar Waya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalam alaikum. Malam shin ya halatta mutun yayiwa budurwarsa kiss yayin da suke waya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Wannan yana daga cikin ire iren abubuwan da fitsararrun samari da 'yan matan zamani suka Qirkiro. Kuma yana daga cikin abubuwan da suke cire musu kunya, kuma yake afkar dasu acikin zina.

Misali saurayi da budurwar da suka saba yiwa Junansu Kiss ta waya, da zarar sun Haɗu FACE TO FACE, babu abinda zasuyi tunani illa su aiwatar da Kiss din azahiri.

Irin wadannan al'adun turawa ne, bai dace da dabi'unmu da addininmu ba..

Mu a addininmu ba'ayin kowanne irin Kiss sai bayan an daura muku aure da juna.

bawai haka kawai Allah s.w.a yace kada akusanci zinaba saidai kasancewar Qanqanin abu zai iya kaiwa ga zinar, Kamar yadda nassi ya tabbatar akwai zinar ido akwai ta baki, ruwan Al'aurane ya gasgata ko akasin haka, dan haka bai halattaba Sam Sam Allahumma saidai idan ma'auratane wannan babu laifi duk da shima akwai haɗari saboda Sabbin hanyoyin technology nazamani zaka iyayin komi akan Idon wani.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa: ''Kunya tana daga Imani. Duk wanda bashi da kunya, to bashi da Imani.." kuma yace "duk wanda yayi kama da wasu mutane, to tabbas yana cikinsu".

Don haka duk wanda yake so ya haifi 'ya'ya masu albarka, to wajibi ne ya nuna dabi'u masu kyau irin na Musulunci tun alokacin neman auren mahaifiyarsu.

Allah ya shirye mu baki daya, Yasa masu yi su daina. Ameen

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments