Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Tana Halatta Ga Namiji Idan Ya Biya Sadaki Ba'a Riga An Ɗaura Aure Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Malam Barka da kwana ya gida ya iyali ya kokarin hakuri da hidimar jama'a. Allah SWT ya Saka da alkhairi ya Kara lafiya. Malam don Allah Ina son ayi mana Karin bayani shin mace tana Halatta ga namiji idan ya ba iyayenta kuɗin sadaki Amma ba'a tara mutane an ɗaura masu aure ba?

Jazakumullahu khairan kaseeran 🙏

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Bisa gaskiyar magana, lamarin yadda ake Qulla aure yana da bambanci tsakanin al'ummah daban daban. Kuma addini ma yana la'akari da duk wata al'adar da mutane suke da ita mutukar bata saɓa da addini ba.

Misali su a Qasashen larabawa, idan mutum ya biya sadaqi kuma an karɓa, to fa shike nan aure ya Qullu. Kuma dashi da budurwar ko bazawarar tasa sun zamto miji da mata ke nan.

Amma mu anan yankin Qasashen hausa/Kanuri/Fulani yadda mukeyi kuma muka saɓa dashi shi ne harkar Qulla aure muna rabata ne zuwa kashi uku kamar haka

1. Neman izinin iyayen yarinya tare da neman yardarta daga baya. (wato hira ke nan tsakanin saurayi da budurwa ko bazawari da bazawara).

2. Baiko: Shi ne yarjejeniyar nuna amincewa atsakanin waliyyan angon dana amaryar. Kuma awasu wuraren tun asannan ake biyan sadaqi kuma waliyyan amaryar suke karɓa amadadinta.

3. Taron ɗaurin aure: Awasu lokutan sai awannan ranar ake bayar da sadaqin da aka yanke tun lokacin baiko. Awasu lokutan kuma ɗaurin auren kawai akeyi Wanda a Qalla ana bukatar Waliyyin matar da za a aura ɗin, tare da shaidu koda kuwa mutum biyu ne rak.

Yayin da su ayankunan larabawa suke ɗaukar duk matar da aka biya sadaqinta amatsayin matar aure, kuma tana da ikon cin gadon wannan da ya biya sadaqin nata da ace zai mutu kafin tarewarta agidansa, to mu fa anan Qasar hausa bamu ɗaukar biyan sadaqi a irin wancan matsayin. Mu awajenmu bai wuce yarjejeniyar Qulla aure ba.

Bamu ganin cewa wace matar wane ce, har sai bayan anje mataki na uku kuma na karshe. Wato bayan an ɗaura musu aure ke nan agaban shaidu.

Kuma sau da yawa yarjejeniyar takan watse tun akan mataki na farko ko na biyu. Kuma ba'a ɗaukar wannan matar amatsayin wacce aka saketa, sai dai ace kawai saurayinta ya janye.

Don haka kada ki yarda ki amince ya rika taɓa jikinki mutukar ba'a ɗaura muku aure ba. Sau da yawa tsofin mazinata da shaiɗanun samari suna amfani da wannan shubuhar wajen lalata 'ya'yan mutane.

Hakanan idan malamai suka buɗe musu wannan Qofar, tofa sun samu yadda suke so ke nan. Domin mafiya yawansu zasu iya bayar da sadakin dubu ɗari ko fiye da haka, mutukar yin hakan zai basu damar yin zina da yarinya har tsawon watanni suna sharholiyarsu. Idan sun gama lalata rayuwarta sai su tada husuma yadda daga karshe zasu tsallaketa su koma kan wata.

Ki lura daga lokacin da kika fara amince masa yana taɓa jikinki, daga nan zai fara neman aikata zina dake. Daga sanda ya sanki amatsayin 'Ya mace, shike nan kuma zai fara zullewa yana neman hanyar da zaku rabu.

Idan kuma ciki (wato juna biyu) ya bayyana ajikinki, idan yaga dama yana iya cewa bai san dashi ba. Yace ba nashi bane. Ke kuma daga nan shike nan rayuwarki ta duniya har ta lahira ma ta kama hanyar lalacewa ke nan. Idan kika barshi, kin bar wa kanki da danginki babban abun kunyan da za a rika nunasu agari. Idan kuma kika zubar dashi, kin haɗa manyan laifuka biyu ke nan. Ga na zina, ga kuma kisan rai ba tare da hakki ba.

Don haka hanya mafi sauki kuma mafi tsafta mafi dacewa ita ce kada ki yarda dashi ya taɓa jikinki ballantana har ya aikata wani abu dake. Kuma wata hujjar ma anan ita ce: kice masa iyayenki da suka karba sadakinsa ai basu karɓi da niyyar sun halatta masa yayi mu'amalar aure dake ba. a'a sun karɓa ne da niyyar qulla yarjejeniyar cewa zasu bashi aurenki, amma basu riga sun bashi ba, sai bayan AN ɗaura aurenku.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments