𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya
sai ya biyo ta gidanmu wai yana so ya sadu dani, yayi ta kawo min
kabli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga munyi aure, ni dai gaskiya malam na qi
yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria
cewa: baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne
saboda hujjoji kamar haka
1. Abin da aka sani shi ne kuɗin
da ake bayarwa yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna
dunqulewa su bayar gaba ɗaya,
kin ga kuwa inhaka ne, to ai dukkan ayyukan ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar
yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito.
2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa
da kuɗinsa, kin ga
wannan yana nuna ba aure ba ne.
3. Hakan zai iya buɗe
hanyoyin ɓarna, don
dukkan wani ashararu zai iya kai kuɗi
a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya
haramta duk abin da yake kaiwa zuwa ɓarna.
4. Yana daga cikin sharuɗan
auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai
kuɗin da za a yi
baiko, zai iya zama mutum ɗaya,
kin ga akwai nakasu ke nan.
5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko,
ake sanya ranar ɗaurin
aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban.
6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado
tsakanin waɗanda
akayiwa, idan ɗaya
daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin
ma'aurata suna gadon junansu.
Allah shi ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.