Fasa Neman Aure Ba Tare Da Wani Dalili Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mutum ne yake neman yarinya da aure, amma kafin a kai ga sanya musu rana sai kawai ya ji ta fita a ransa, ba kuma don wani laifi da ta yi ba. To wai idan ya daina cigaba da neman za a ce ya cuce ta? Kuma ko zai iya sake samun wata irinta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Bai kamata wani daga cikin masu neman auren juna ya jawo abin da zai sa a fasa cigaba da neman auren da aka fara ba, sai fa in da wani ƙwaƙƙwaran dalili ne da sharia ta yarda. Saboda yin hakan yana daga cikin siffofin munafukai ne. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce:

    Alamomin munafuƙi guda uku ne:

    إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ ، وَإِذَا ائْتُمِنَ خَانَ ، وَإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ

    Idan ya zo bayar da labari sai ya yi ƙarya, kuma idan aka amince masa sai ya yi yaudara, idan kuma ya yi alƙawari sai ya saɓa. (Sahih Al-Bukhaariy: 35, Sahih Muslim: 59).

    Amma idan akwai dalili, to ai ba ma a lokacin nema kafin ɗaurawa ba, har a bayan ɗaurawa da tarewa ma ma’aurata suna iya rabuwa da juna kamar yadda aka sani ta hanyar saki, a bisa ƙaidojin Sharia. Watau dai yana iya fasa neman aurenta, kamar yadda ita ma take iya fasa yarda da nemansa, in akwai wani dalili na Sharia.

    Bayan rabuwarsu malamai sun yi bayanin matsayin kyautar da ya shiga tsakaninsu kamar haka

    1. Idan abin da ya bayar ya kasance a matsayin wani sashe ne na sadakin auren, to idan auren bai yiwu ba sai a dawo masa da kyautarsa, ko da kuwa fashin yin auren daga wurinsa ne.

    2. Amma idan abin ya zama wani kyauta ne kawai a tsakaninsa da wadda yake nema da manufar ƙara jawo hankalinta da soyayyarta kawai zuwa gare shi, to yanzu da auren bai yiwu ba sai ta dawo masa da abin da ya saura na kyautarsa, muddin dai fashin yin auren daga wurinta ne. Domin dai ai bai kamata a haɗa masa zafi biyu ba: Ga mari kuma ga tsinka jaka?! An ce ba a sonsa, kuma an riƙe masa kyautarsa?!

    3. Idan kuwa fasa yin auren daga wurinsa ne, to bai kamata ya nemi ta dawo masa da kyautar ba, domin ai ba girmansa ba ne. Da wanne za ta ji: Da zafin fashin auren ko kuwa da zafin karɓe kyautarsa? Sannan kuma ga Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: Mai karɓe kyautarsa kamar kare ne ya yi amai kuma ya koma ya lashe shi! (Sahih Al-Bukhaariy: 2622).

    Sannan kuma fashin yin aure ai bai kamata ya zama dalilin aukar da rashin mutunci, ko samar da gaba ko ƙiyayya a tsakaninsu ba.

    A ƙarshe kuma ba za a ce wai ba zai sake dacewa da wata mace ta gari ba a cikin rayuwarsa ta gaba, matuƙar dai ba da wani mummunan nufi na cutarwa ne ya rabu da waccan da ya fara neman ba. wannan na Allaah ne. Allaah ya datar da mu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    08164363661

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.