Mijinta Ya Rasu Tana Cikin Idda

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Matar da take cikin iddar saki ukun da mijinta ya yi mata, sai kuma ya rasu alhali ba ta gama iddar ba, to yaya za ta yi? Shin za ta cigaba da iddar sakin ne, ko kuwa za ta koma ga iddar mutuwa ne?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Dangane da matar da take cikin iddar saki sai kuma mijin da ya sake ta ya rasu, malamai sun karkasa magana a kanta gida-gida ne kamar haka

    1. Idan iddar ta sakin da ya ke akwai kome a cikinsa ne kamar na-farko ko na-biyu, to sai ta bar iddar sakin ta koma ta faro iddar mutuwa tun daga ranar rasuwar mijin, domin akwai sauran alaƙar aure a tsakaninta da mamacin. Kuma za a ba ta gado. Duk wannan saboda maganar Ubangijinmu Tabaaraka Wa Taaala cewa

    وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَلِكَ إِنْ أَرَادُوا إِصْلَاحًا

    Kuma mazajen aurensu su suka fi cancantar su mayar da su a cikin hakan, idan dai sun yi nufin kyautatawa. (Surah Al-Baqarah: 228)

    A nan sai Allaah ya kira wanda ya yi saki na kome da sunan: Miji ga wacce ya saka, ishara ga cewa akwai sauran alaƙa a tsakaninsu.

    2. Idan kuma sakin wanda babu kome a cikinsa ne kamar saki na-ƙarshen uku, ko kuma idan sakin daga wurin matar ne kamar na khuli, to a nan abin da ya fi daga cikin maganganun malamai shi ne, ba za ta komo ga iddar sakin ba, domin babu wata alaƙa da ta saura a tsakaninta da mamacin. Don haka a nan babu gadon da za ta samu.

    3. Amma idan aka gano cewa a cikin rashin lafiya na ajali ne ya yi mata sakin na-ƙarshe domin ya hana mata samun gadonsa, to a nan za ta dawo ta yi masa takaba kuma a ba ta gado. Haka kuma tana da gadonsa ko da a bayan ta gama iddar sakin ne ya rasu. Wannan kuwa domin ƙaidar malaman Fiqhu mai cewa

    مَنِ اسْتَعْجَلَ شَيْئًا قَبْلَ أَوَانِهِ عُوقِبَ بِحِرْمَانِهِ

    Duk wanda ya gaggauta zuwan wani abu kafin zuwan lokacinsa, to sai a yi masa horo da hana masa wannan abin.

    Ana iya duba As-Sharhul Mumti’u: 5/669-671 na Al-Allaamah Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah).

    Allaah ya ƙara mana fahimta.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄��𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.