Ticker

6/recent/ticker-posts

Sallah Walha

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ina so a yimin ƙarin bayani a gameda sallar walaha

    (ُصَـــلَاة الـضُّــحَــيٰ)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ita dai sallar walaha wata nafila ce da ake yinta bayan rana ta fito ta ɗan ɗaga sama kaɗan, kuma nafila ce da Mαnzon Allαн(Sallallahu alaihi Wasallam) ya kwaɗaitar a riƙa yinta saboda ɗimbin ladan da ke cikinta, domin akwai Hadisai masu ɗimbin yawa na Mαnzon Allαн(Sallallahu alaihi Wasallam) da yake kwaɗaitarwa game da yinta, saboda ɗimbin falala da ke cikintara, kuma lokacinta yana farawa ne bayan hudowar rana yayinda ta ɗan ɗaga sama kaɗan har zuwa lokacin da rana za ta yi zawali.

Alal haƙiƙa babu wani saɓani tsakanin Malamai game da cewa mafi ƙarancin abinda akeyi a sallar walaha shi ne raka'a (2).

Sai dai Malamai sunyi saɓani ne a game da cewa nawa ne mafi yawa na adadin raka'o'in sallar walaha? Malaman da ke Mazhabin MALIKIYYA da kuma mafi yawa na Malaman da ke Mazhabin SHAFI'IYYA da HANABILA, sun tafi ne akan cewa mafi yawan adadin raka'o'in sallar walaha su ne raka'o'i(8), kuma sun kafa hujja ne da Hadisin Ummu Haniy da tace

"أن النبي(ﷺ) دخل بيتها يوم فتح مكة، فصلي ثماني ركعات، ما رأيته صلي صلاة قط أخف منها، غير أنه كان يتم الركوع والسجود"

(رواه البخاري)

MA'ANA

Mαnzon Allαн() ya shiga ɗakinta (Ummu Haniy) a ranar da a ka yi fathu Makka, yayi Sallah raka'a (8), (tace) tunda nake ban taɓa ganinsa yayi sallah mai sauƙi (sauri) kamar rannan ba, tare da cewa yana cika ruku'inta da sujjadar ta

Amma Malaman Mazhabin HANAFIYYA tare da wani ɓangare na Malaman da ke Mazhabin SHAFI'IYYA, su sun tafi ne akan cewa mafi yawan adadin raka'o'in sallar walaha su ne raka'o'i(12), sun kafa hujjarsu ne da wani Hadisi na Anas Ɗan Malik da yace Mαnzon Allαн(Sallallahu alaihi Wasallam) Yace

"من صلي الضحي ثنتي عشرة ركعة بني الله له قصرا من ذهب في الجنة،"

(رواه الترمذي)

MA'ANA

Duk Wanda yayi sallar walaha raka'a (12) to Allαн() zai gina masa katangar zinare a gidan Aljannah

To amma sai dai wannan Hadisi da suka kafa hujja da shi, akwai ƙwanƙwasa a kansa, wato dai Hadisi ne Mai rauni kamar yadda Malamai suka faɗa, sai dai wasu Malaman suna ganin babu laifi ayi amfani da Hadisi mai rauni amma a ɓangaren da ya shafi aikin mustahabbi kaɗai.

To amma sai dai magana mafi inganci kamar yadda Malamai suka rinjayar itace, adadin raka'o'in sallar walaha su ne raka'o'i (8)

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

   Mυѕтαρнα Uѕмαи

    08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments