Ticker

6/recent/ticker-posts

Alaqar Hadisin Fitowar Rana Daga Yamma Da Binciken Da Malaman Kimiyya Sukai Akan Tsakiyar Duniyarmu

TAMBAYA (73)

Don Allah mene ne alaqar dake tsakanin hadisin fitowar rana daga yamma da binciken da masana ilimin kimiyya sukai akan abinda ke faruwa a tsakiyar kasan duniyarmu

AMSA

Alhmdulillah

Hadisin yana cikin Sahih Muslim wanda aka karbo daga Abu Hurairah RA ya ce: Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya tuba ga Allah kafin rana ta fito daga mafadarta (yamma) to Allah zai karbi tubansa"

Hadisin yana bayyana cewar duk bawan da yayi taubatun nasuha ya koma ga Allah kafin rana ta fito daga yamma ta fadi a gabas to Allah SWT zai karbi tubansa saboda idan har ranar ta fito daga mafadarta to tabbas wannan ranar itace ranar karshe wato ranar tashin alqiyama

Hadisin, kamar yanda malamai suka ce yanada alaqa da binciken da kungiyar da take da alhakin tura masana zuwa sararin samaniya (space) mai suna National Aeronautic and Space Administration (NASA), gidan TV na CNN, Geographers (masana taswirar kasashe), Geologists (masana dutsuna), Oceanographers (masana teku) Geophysicist (masana dabi'un kasa) sukayi akan abinda ke faruwa acan karkashin kasa (earth's core) kimanin tafiyar kilometers 2,900 kacal

Abune sananne a cikin Qur'ani mai girma cewar sammai guda 7 ne hakama kassai guda 7 ne

(أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ ۚ إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَأْتِ بِخَلْقٍ جَدِيدٍ )

إبراهيم (19) Ibrahim

Shin, ba ka gani ba cwa lalle ne Allah Ya halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa. Idan Ya so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sabuwa.

Kuma komai a cikinsu tasbihi yake ga Allah Mdaukakin Sarki

(تُسَبِّحُ لَهُ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ وَالْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا )

الإسراء (44) Al-Israa

Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu suna yi Masa tasbĩhi. Kuma babu wani abu face yana tasbĩhi game da gode Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gafara.

Akwai kuma wasu sammai guda bakwai da suke a saman duniyarmu wadanda ake kira da; Exosphere, Mesosphere, Stratosphere, Troposphere, Thermosphere, Ionosphere da kuma Atmosphere dukkansu suna bada gudunmawa gameda rayuwar dan Adam da tsirrai da dabbobi. Kwanannan National Geographic suka fitar da bayanai na ilimi akan cewar akwai wasu layers a kasan duniyarmu guda 4 wato; crust, mantle, solid outer core sai kuma Inner core

Shi wancan Inner core (tsakiyar duniya) din shi ne wanda Prof. Michau Kaku ya ce: "Oh my God ! Core din duniyarmu ya tsaya cak kuma zai fara juyawa da baya da baya sabanin yanda ya saba"

Stephen Hawkins a cikin littafinsa mai suna: "The Brief History Of Time" (Taqaitaccen tarihin lokaci) yayi tsokaci akan abinda ya shafi juyawar earth's core wanda ake kira da retrograde motion wato juyawar duniya anticlockwise

Abinda ya basu mamaki shi ne, a yanzu haka duniyoyin da suke a anguwar rana (as-Shams) sun fara juyawa sabanin yanda suka saba ma'ana duniyar Neptune, Uranus, Saturn, Jupiter, Mars dukkansu rana tana bullowa ne daga Yammaci sannan ta fadi a Gabashi kuma yanzu haka duniyarmu ta Earth itace makociyar Mars ke nan (Duniyar da turawa suke son komawa da zama nan da shekarar 2026) nan da wani lokaci kadan muma zamu wayi gari mu ga bullowar rana daga mafadarta, tashin alqiyama ke nan !

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un !

Kwanakin baya jaridar "The Guardian" ta wallafa maganar wani Geophysicist daga British Geological Survey mai suna Ciaran Beggan, ya ce: "Duniya ta sauya tafiyarta daga matakin kilometers 10 (6 miles) zuwa kilometers 50 ko 60 a duk shekara. A yanzu haka tana gudu ne tana dosar yankin (direction) din kasar Siberia"

A yanzu haka ba kowa bane yasan da wannan bincike da akayi duk da cewar a zahiri mu kanmu mukance kalli fa yanda shekara take sauri, wata yake hanzarin karewa, sati yake gudu, mun manta da cewar duk wannan fa kananan alamomi ne na tashin alqiyama kuma mu musulmai a wajenmu ba abin mamaki bane ba domin kuwa sama da shekaru 1,400 baya Annabinmu SAW ya sanar da mu cewar shekara za ta koma kamar wata, yayinda wata zai koma kamar sati, satin kuma kamar kwana daya, sannan kuma rana za ta hudo ta mafadarta ma'ana daga Yamma za ta fadi a Gabas, daganan kuma shike nan rana ta daina aikinta na samar da haske ga halittun Allah SWT

Me na shiryawa zuwan wannan ranar?

Me ka shirya?

Me kika tanada?

Sai yaushe zamu koma ga Allah ne?

Amsar ta rage ga mai karatu

A yanzu ne tunanin canzawa zai amfani bawa, bawai sanda yaga Jahannama a zahiri ba kamar yanda Allah SWT ya fada;

(وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّىٰ لَهُ الذِّكْرَىٰ )

الفجر (23) Al-Fajr

Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunani. To, ina fa tunani yake a gare shi!

Fatana shi ne wancan hadisi da kuma wannan bincike da masana ilimi sukai ya kara nusar damu akan yawaita Istighfari kafin a rufe kofar tuba (lokacin da za a ga fitowar rana daga mafadarta)

A maimakon mu dinga yawan cece-kuce akan yanayin da muka tsinci kanmu na tsadar rayuwa, kamata yayi mu koma ga Allah SWT ta hanyar yin taubatun nasuha tunda wadanda suka gabacemu ma sai da Allah SWT ya jarabcesu kamar yanda ya fada a cikin Qur'ani mai girma;

(أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِكُم ۖ مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاءُ وَالضَّرَّاءُ وَزُلْزِلُوا حَتَّىٰ يَقُولَ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ مَتَىٰ نَصْرُ اللَّهِ ۗ أَلَا إِنَّ نَصْرَ اللَّهِ قَرِيبٌ )

البقرة (214) Al-Baqara

Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misalin waɗanda suka shige daga gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cũta sun shafe su, kuma aka tsoratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmani tare da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!

Kamata yayi mu hanzarta neman yafiyar wadanda muka sabawa kuma muyi gaggawar aikata ayyukan alkhairi da neman tuba kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada;

(وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )

آل عمران (133) Aal-Imran

Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda faɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta domin masu taƙawa.

Masu aikata alfashi a gaggauta tuba a tuno da matan Hurul Ayn wadanda Allah SWT zai aurar ga duk mai imani kamar yanda ya fada;

(وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَنُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۖ لَّهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَنُدْخِلُهُمْ ظِلًّا ظَلِيلًا )

النساء (57) An-Nisaa

Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, za Mu shigar da su gidajen Aljanna, (waɗanda) ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, matan aure masu tsarki, Kuma Muna shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.

(وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ )

الأعراف (179) Al-A'raaf

Kada mu fada tarkon shaidan mu yanke Rahamar Allah kamar yanda Elon Musk (Mai kamfanin Twitter da SpaceX, kuma mutum na 2 wanda yafi kowa kudi a duniya) wanda Shaikh Muhammad yayi masa tayin karbar addinin musulunci saboda yanda yake ganin ayoyin Allah a sararin samaniya a matsayinsa na masanin kimiyya, amman Elon Musk da ya tashi sai yayi masa reply da cewar ya gode da tayin da yayi masa amman ya zabi ya shiga wutar Jahannama da ya karbi musulunci wai saboda yaji cewar ma ai mutane sunfi yawa a wutar, hujjarsa itace ayarnan;

(وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ )

الأعراف (179) Al-A'raaf

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta saboda Jahannama, masu yawa daga aljannu da mutane, suna da zukata, ba su fahimta da su, kuma suna da idanu, ba su gani da su, kuma suna da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisashe suke. A'a, sũ ne mafi ɓacwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.

To anan gabar ne fa yakamata mu tuno da wannan sahihin hadisin da Annabi SAW ya ce: "Da ace duniyarnan tana da darajar fiffiken sauro a wajen Allah SWT da kafiri bai sha ruwa a cikinta ba"

Haka siddan zakaga mutane ba sa son musulunci, kamardai wani Christian wanda mukai karatu a department din Microbiology dake Jami'ar Bayero ta Kano wanda nayi masa tayin shiga musulunci yacemin ko da ace mutanen duniya gaba daya zasu shiga musulunci to shi ba zai musulunta ba. Sai na tuno da "Wanda Allah ya batar ba wanda ya isa ya shiryar dashi hakama wanda ya shiryar ba wanda ya isa ya batar dashi. Fatana shi ne Allah ya shiryar da wancan Trinitarian din

Kagadai Elon Musk shi ne na 2 a kudi a duk duniya kamar yanda Forbes suka wallafa to ammanfa kaga bashi da imani kai kuma ga ka kana karanta wannan saqon amman ko Naira miliyan daya bakada ita a cikin aljihunka ko account dinki to indai kina yin sallah akan lokaci kuma kina kiyaye dokokin Allah mastada' to hakan na nufin kin fi Elon Musk a wajen Allah Al-Azizu

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments