TAMBAYA (74)❓
Idan ina period bana samun nutsuwa sai na kalli fina-finan
batsa. Mene ne mafita
AMSA❗
Lahaula wala quwwata illah billah
Mun tsinci kanmu a farkon qarni na 21 da ake kira da 21st
century wanda bala'i da masifar wayar hannu ya jefa yawancin samari kaso 99% da
kuma yan mata kaso 82% fadawa talbis iblis wato tarkon iblis ta hanyar aikata
zinar ido, kunne da hannu silar wanzuwar wayar salula kamar yanda bincike ya
tabbata da hakan
Yawancin mutane ba sa aiki ko kuma sun manta shawarar da
Annabi SAW ya bawa matasa cewar su yi aure idan suna da hali, idan kuma basu da
yanda zasu iya sai su dinga azumin nafila kamar irin azumin litinin da alhamis,
azumin 13,14, da 15 na kowanne wata, azumin Annabi Dawud AS wanda yake azumtar
yau gobe kuma yasha azumin har ya koma ga Allah SWT
Da ace zamu dinga koyi da hakan to da ko dai ba'a daina
fadawa tarkon kallon blue films ba to a qalla za a rage da kaso mai yawa wanda
a karshe abin zai zama tarihi ga wanda ya dabi'antu da aikata hakan
Malaman lafiya sun tabbatar da cewar kallon fina-finan batsa
yana kawo matsalar al'aura, qwaqwalwa ido da kuma yawan mantuwa
Akwai wani program da akayi da wata shahararriyar karuwa mai
suna Mia Khalifa (Yar asalin kasar Lebanon ce) wadda tace duk abubuwan da
mutane suke kallo a fina-finan batsa ba haka suke ba 100% kusan 50% na films
din duk editing ne don a janyo hankali masu kallo domin masu tsarawan su samu
kudi. Ita kuma mawaqiya Ketty Perry jan hankalin mutane ta yi akan cewar duk
wannan ado da qyale-qyalen da ake ganin tana sakawa ba gaskiya bane ba akwai
editing sosai a ciki kuma tace ita yanzu gaba daya ma bata jin dadin yanda take
rayuwa
A shekarun baya, Mia Khalifa itace ta sa jewellery company
suka fitar mata da wata sarqa wadda a jiki aka rubuta "Satan" wato
Shaidan kuma a haka wasu daga cikin matan musulmai suke siya da kudinsa suna
sakawa a wuyansu
A cikin wani rubutu wanda Muhammad Ubale Kiru ya fitar, yayi
bayani sosai akan illar dake tattare da kallon blue films. Ga rubutun kamar
haka;
Jima'i A Yau
~~🔞
A yan shekarun nan matsala jima'i na daga cikin matsalolin
da suke lalata rayuwar aure. Ire-iren matsalolin sun hada da rashin yin jima'i
shi kansa, rashin lafiyar gaba, sirihi, tasirin pornography wato blue film da
sauran su. Amma a yau, ina so nayi focussing ne akan matsalar da pornography ya
haifar a wannan zamanin. yarkeji
A Yau yana wahala ace akwai saurayi matashi ko yarinya
matashiya da basu taba kyella ido akan wannan fim na badala da ake kira da blue
film ko porn ba. Kusan duk a cikin mutum 10, to 8 zun taba kallo, ko dai so
daya, ko sau biyu, ko ma fiye da haka. Wasu ba sun kalla bane da niyyar ci gaba
da kallo, ko don suna so. Sun kalla ne watakila saboda sun ji wani yayi zancen,
ko kuma sun ci karo da shi wajen kallon fina-finan Amurkawa, ko kuma don kashe
kwar-kwatar ido (Allah ya tsare mu).
Kusan ya zama al'ada yanzu, idan matasa za suyi aure sai sun
kalla, ko dai saboda curiosity, ko kuma saboda neman ilimi, wanda kuskure ne
hakan. Domin kuwa Malamai magabata sun tabbatar mana da cewa lamarin jima'i
lamari ne daga Allah, kuma dan Adam baya bukata a koya masa, Allah ne yake bada
ilimin idan lokacin yayi. Shi yasa idan ka balaga abu na farko da kake fara
gani shi ne mafarki kana saduwa. Porn ba shi ne ya dace ya koyarwa kai ilimin
jima'i ba, saboda haka ne ma nake so a cikin wannan rubutu na bayyana mana wasu
abubuwa da yawa da muke ji, ko muke gani, ko ake fada game da jima'i da kuma
illar da porn ko blue film yake bari a kwakwalwar mutane.
Kallon wannan fim na badala ya canja mindset din matasa da
yawa, kai har ma da wasu manyan. Domin kuwa yanzu ana iya samun mace ta koka
akan cewa mijin ta baya iya gamsar da ita yadda take so. Ko kuma namiji yaji a
ran sa idan bai laga-laga da mace ba, to bai cika namiji ba. Ko kuma wasu suji,
ai kai ba jarimi bane sai idan zaka iya hour kaza, ka kayi jima'i a dare sau
kaza, shi ne ka cika jarima. Hakan nan idan kaje kasuwanni magani, da chemists,
za kayi ta cin karo da maza suna karbar magunguna Manpower don zaburar da
kawunan su. Su ma matan ba'a bar su a baya ba, domin kuwa ba sa zama ba tare da
sun sha ko sun ci wani abu makamancin wannan ba. Bana manta labarin wata baiwar
Allah da muka kashe auren ta saboda mijin ta yana shan magani manpower sosai, a
rana maganar bakwai ake zuwa goma. Wallahi wannan ne sanadiyya mutuwar auren.
Abin da mutane da yawa basu sani ba shi ne: Jaridar
Cosmopolitan ta wallafa wani interview da ta yi da jaruman blue film su 40. A
inda bayanansu suka nuna cewa shi film din blue film ko porn, film ne kamar
kowane irin film. Yana dauke da scripts, wato labari, action, fiction da
sauransu. 70-85% na abubuwan da ake bayyana wa a porn ba gaskiya bace zalla,
akwai zuki-ta-malle wato fiction. Za a iya nuna jarimi da jaruma sun shafe hour
daya zuwa biyu suna abu daya, amma a bayan fage, sun tsaya sun huta sama da sau
biyar. To amma a camera an yanke don kar ka gani. Saboda haka ake so ka yarda.
Suka kara da cewa, badan suna hadawa da magani ba, da ko
minti 10 baza su iya yi ba, kuma ba don taimakon camera ba, da shima hakan ba
zai samu ba. Wata daga cikin wanda akai wa interview din ta kara da cewa, ko
iface-iface da suke yi, saka su akeyi don karawa kallon armashi. Ta kara da
cewa, wasun su, a cikin tsananin zafi suke, saboda abin ya wuce hankalin da
kuma limit da jikin dan adam zai iya dauka. Don haka Director ne zai ta cewa
ayi ta ihu don a inganta scene din da ake. Don haka ba gaskiya bane. Wani
jarima shima ya tofa albarkacin bakin sa inda yace, shi mai aure ne, kuma tunda
yake saduwa da matar sa, bai taba wuce min 20 ba. Wanda idan da kuwa a film ne,
har mai hour uku yayi.
Idan ka koma bangaren litittafen Hausa da Novels, suma sun
taimaka kwarai wajen sanyawa matasa tutani makamancin wancen, da burika wajen
mu'amalar auratanya. Wannan shima koma bayane sosai, domin kuwa mata sukan
kalli mazajen su a matsayin malalata, ragwaye, marasa kuzari, saboda su a
tunanin su, namiji shi ne wanda yake lasting minti 30 zuwa hour daya. Sannan
bayan ya sauka, ya sake komawa, idan ya sauka ya sake, akalla sau uku ko hudu
kafin Asuba. Tabbas akwai maza jarumai wadda zasu iya haka. To amma tambaya
anan shi ne, meye matsayin hakan a lafiyance sannan da kuma addini?
Yazo a cikin Sahih Bukhari, Manzon Allah SAW yana cewa mu
guji yin abubuwa over, domin duk abinda ya wuce hankali yana zama cuta ne ga
dan adam. Jaridar PlayBoy ta Amurka ta wallafa wani bincike da ta yi akan
adadin mutanen da ya kai dubu hudu, a inda binciken nunawa cewa kaso 50% daga
cikin participants din only lasted 9 minutes 40 seconds a lokacin saduwa. Kaso
30% kuma minti 14 da second 10. Kaso 20% kuma minti 20 daidai. Sai masana suka
karkare cewa average mutanen duniya a yadda Allah ya tsara halitta, ba sa wuce
minti 4 zuwa minti 9 a lokacin saduwa (Saduwa anan yana nufin sanda aka hade
tirmi da tabarya). Sannan mafi yawancin mutanen duniya suna saduwa ne sau uku kacal
a kowane sati. Kadanne daga cikin mutane suke saduwa kullum ko kuma fiye da sau
daya a kowane wuni. Amma dai bayanai suna nuna cewa it is not normal dan adam
yayi jima'i fiye da sau uku a wuni daya. Bayanai sun nuna cewa masu yin jima'i
sama da 5 zuwa bakwai suna developing wata cuta mai sanya kwayayen da-namiji su
fara fitar da jini a maimaikon maniyyi. Sannan yi din da yawa ta hanyar amfani
da maganin sanya dadewa yana kawo mutuwar gaba ta dindindin bayan shekaru sun
ja.
Don haka ina so na ja hankalin ma'aurata da su sani cewa.
Abinda suke karantawa a littafi ko suke kallo a film, ba wani abu bane illa
shirin film ne kawai. Shirine don kayatarwa da nishadatarwa. Sannan binciken
masana ya nuna kamar yadda yazo a mujallar PentHouse cewa ma'auratan da suke
ta'ammali da porn ba sa iya gamsar da juna a lokacin saduwa. Jaridar ta kara da
cewa, wannan matsalar tana haddasa mutuwar aure da 9% a kasar Amurka duk
shekara. Sannan ta kara da cewa: bayanan sirri na porn industry sun nuna cewa
industry din tana fuskantar kalubale na shara'a da mutane da dama wanda suka
dauka cewa porn gaskiya ne, domin a cewar su, yayi destroying expectations na
su kuma ya lalata musu rayuwar aure.
Bari na dakata anan. Allah ya bamu ikon fadin gaskiya da
kuma aiki da ita, ya kuma ganar da mu gaskiya duk rintsi, sannan ya kare mana
idanuwan mu daga zinar ido.
✍️Muhammad Ubale Kiru
📅26/01/2024
🌐#MuhdKiru
MAFITA
Ta yaya mutum zai daina kallon blue films gaba daya?
Amsar mai sauqi ce, itace ta hanyar yawan ambaton Allah SWT,
ba ma iya gangar jiki ba har zuciya tana samun nutsuwa silar ambaton Allah
kamar yanda ya fada;
(الَّذِينَ
آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ
الْقُلُوبُ )
الرعد
(28) Ar-Ra'd
Waɗanda
suka yi ĩmani kuma zukatansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah
zukata suke natsuwa
Sai kuma bin shawarar Annabi SAW kamar yanda ya tabbata a
cikin sahihin hadisi wato yawaita azumin nafilfili kamar yanda na lissafo a
baya
Malaman ilimin sanin dabi'ar dan Adam (Psychologists) sun ce
ga wata hanya mai sauqi ga wanda yake son daina kallon blue films;
Na farko shi ne mutum ya gane cewar wannan fa babbar matsala
ce ga lafiya, saboda tun tuni yawan kallon yana cutar da tunanin mutum kuma za
ta iya yiwuwa mutum yayi kokarin dainawa amman abin ya ci tura, ka kaddara daga
wannan lokacin ba zaka kara kalla ba
A cikin second 1; zaka gane ka yanke shawara mai kyau. A
cikin mintuna 10 zaka ji kana alfahari da kanka silar dainawar. A mintuna 30
zaka ji kwanciyar hankali silar dainawar. Washegari zaka ji jikinka ya fara
sauyawa. A kwana na 2 zaka fara jin ciwon kai, zaka ji shaidan yana maka
waswasi akan ka ci gaba da kallon, nan take sha'awarka za ta ninku sau uku,
wadataccen bacci zai gagareka
A kwana na 3 zaka ji ka rasa sinadarin dopamine (sinadarin
da yake saka sha'awa). A kwana na 4 wannan karfin sha'awar yake rinjayar wasu
su koma kallon fina-finan batsan. A kwana na 5 qwaqwalwa za ta jinjinawa
al'aura ta yaba mata sakamakon yanda taga mutum ya dage akan rashin komawa
waccan mummunar dabi'ar. A kwana na 6 ciwon kai zai karu matuqa
A satin farko da mutum ya daina kallon blue films, zai fara
banbance alaqa tsakanin mummuna da kyakkyawa, a kwana na 10 kuma wayarka za ta
yi qoqarin mai da kai gidan jiya la'akari da kana cin karo da hotuna da tallace
tallace masu tada sha'awa. A sati na 2 kuma qalubalen zai zo maka da sauqi
sakamakon gyaruwar ruhinka. A kwana na 20 ne idanunka zasu dinga gani wasai
ma'ana tunaninka da ganinka zai yi kyau
A cikin wata 1 kuma zaka dinga tuno shafukan fina-finan
batsa kamar yanda masana suka fada, har saika fi karfin zuciyarka (musamman ta
hanyar yin azumi kamar yanda Annabi SAW ya shawarci matasa). A cikin wata 1 da
½ kuma cin abinci mai maiqo da kuma kayan marmari za su yi qoqarin tayarwa da
mutum waccan sha'awar. A cikin watanni 2 mutum zai wanzu cikin farin ciki kuma
zai dinga samun sha'awarsa ta wani abin amman badai kallace kallacen blue films
ba, zaka dinga kallon mace a matsayin mai daraja da kamala sabanin da can da
kake kallon dukkanin matan duniya a matsayin sex objects wato ababen biyan
buqata ko kuma ababen kawar da sha'awa
A cikin wata 2 da ½ kuma zaka ji kana samun energy, zaka ga
kana aiwatar da komai akan tsari. A cikin wata 3 zaka ji qwaqwalwarka ta dawo
daidai. Cikin wata 3 ½ zaka dinga samun ci gaba kodai silar karance karancen
littattafai ko kuma ta hanyar motsa jiki
Idan kayi qoqari ka share watanni 4 cur baka kalli blue
films ba to zaka ji kana buqatar yin aure domin gusar da sha'awarka a gurbin da
ta dace. A watanni 6 kuwa sha'awarka za ta ninninku fiye da can da, fitar
oxytocin zai qaru. A cikin shekara 1 zaka dinga tunanin shirmen da kayi acan
baya, danasani zai kewaye ka. To amman idan ka tuno da cewar Taubatun Nasuha
kayi sai kaji wani sakayau damuwar ta gushe. A shekara 1 da ½ zaka ji kayi
balance, su kansu yan uwanka zasu gane ka canza. Idan kayi shekaru 2 cur baka
ziyarci shafin blue films ba to zakaji rayuwarka ta sauya kuma zaka ji kana
alfahari da kanka sakamakon wannan niyyar da ka yi na cewar ba za ka qara
kallon fina-finan ba
Wannan a taqaice shi ne abinda masana suka fitar nima kuma
na dan yi qari a cikin bayanan don sauqaqe fahimta
A karshe ina son in bawa maza da mata shawara akan duk wani
abu da zai kusantamu da aikata zina to mu nesance shi don cika umarnin Allah;
(وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
)
الإسراء
(32) Al-Israa
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha
ce kuma ta mũnana ga zama hanya
Sannan kuma ina son nayi amfani da wannan damar don isar da
saqon wata yar uwa da take son a saka ta a cikin addu'a domin kaucewa hadarin
dake cikin wayar salula. Kuma muna roqon Allah ya sa wayarmu ta zamo silar
shigarmu Aljannah, ba wuta ba. Allah ya rabamu da rudin shaidan domin kuwa
malamai sunce iblis bai taba samun dama da kuma kayan aikin halakar da bani
Adam ba kamar irin yanda ya samu a wannan zamanin na Technology
Allah yasa mu wanye lafiya
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.