Nazarin Turke a Wakokin Wasu Makadan Asharalle na Jihar Katsina

    Citation: Kurawa, M.A. (2024). Nazarin Turke a Waƙoƙin Wasu Makaɗan Asharalle na Jihar Katsina. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 330-340. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.038.

    Nazarin Turke a Wa ƙ o ƙ in Wasu Maka ɗ an Asharalle na Jihar Katsina

    Musa Abubakar Kurawa
    Department of Nigerian Languages,
    Yusuf Maitama Sule Uni v ersity, Kano. (YUMSUK)
    Musaudat5@gmail.com
    0803 703 8366

    Tsakure

    Wannan nazari ya ƙ unshi ta ƙ aitaccen bayani a kan wa ƙ ar Asharalle ne da kuma tsokaci a kan turakun wa ƙ o ƙ in wasu maka ɗ an Asharalle na Jihar Katsina. An yi amfani da ra’in Wa ƙ ar Baka Bahaushiya (WBB) ne wajen gina wannan nazari tare da fito da wasu turaku a wa ƙ o ƙ in wasu maka ɗ an asharalle na jihar Katsina ta amfani da ra’in, wa ɗ anda suka ha ɗ a da: Turken yabo da na ta’aziyya da na zambo da na ko ɗ a kai da na fa ɗ akarwa da na siyasa da kuma na soyayya. Haka kuma an gina muradin wannan nazari ne domin gano yadda maka ɗ an Asharalle suke amfani da fasaharsu wajen gina turakun wa ƙ o ƙ insu . Ginshi ƙ an hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike su ne; tattaro bayanai da matanonin wa ƙ o ƙ in maka ɗ an Asharalle, inda aka tattaro wasu wa ƙ o ƙ in maka ɗ an Asharalle, wa ɗ anda aka saurare su kuma aka juye su a rubuce. Haka kuma an tattaro bayanai ta hanyar hira da wasu maka ɗ an Asharalle. Haka kuma, nazarin ya ba da gudummawa wajen fito da hikimar da maka ɗ an Asharalle suke amfani da ita yayin gina turakun wa ƙ o ƙ insu.

    Fitilun Kalmomi: Turke, Maka ɗ an Asharalle, Wa ƙ ar Baka Bahaushiya (WBB)

    Gabatarwa

    Wannan nazari ya yi waiwaye ne kan gano fasahar maka ɗ an Asharalle, ta haka ne nazarin ya karkata ya bibiyi yanayin shirya ɗ iyan wa ƙ o ƙ insu da hikimominsu wajen gwanintar sarrafa harshe da kalmomi a yayin isar da sa ƙ o. Wanda aka mayar da hankali a turke kawai. W a ƙ ar baka ta Asharalle, ta samo asali ne a jihar Katsina daga wa ƙ e-wa ƙ en da Fulani suke yi a lokacin bikin baiko ko bikin aure ko bikin suna. Daga baya ta riki ɗ e ta komo ana yin ta da harshen Hausa a wajejen shekarar 1984 zuwa 1985. Maka ɗ an Asharalle suna da yawa a Arewacin Nijeriya, amma an fi jin ƙ ugin wa ɗ anda suka shahara a jihar Katsina, kamar su: Alhaji Audu Namata, da Alhaji Sirajo Mai’asharalle, da Wada Uban Maryama, da Amadu Sheme, da Audu Boda, da Abashe Galadanci, da Gambon Sirajo, da kuma Ali Guido. Ana iya wakilta tsari na aiwatarwa da ƙ ullawa da sadar da wa ƙ o ƙ in Asharalle a ƙ ungiya kamar haka:

      + Ƙ ungiya + Jagora +’Y/Amshi +Rauji +Rerawa +Sadarwa. Kurawa, (2019, sh.105)

    Turke shi ne wasu masana suke kira da jigo musamman a rubutacciyar wa ƙ a , wato dai ɗ anjuma ne da ɗ anjummai. A nazarin wa ƙ a idan an fa ɗ i ɗ aya daga cikinsu ana nufin sa ƙ on da ake son isarwa a wa ƙ a, wanda shi ne ya mamaye wa ƙ ar tun daga farko har zuwa ƙ arshe.

    Turke a luggance yana nufin “guntun ice da ake kafawa don ɗ aure dabba a jikinsa” (CNHN, 2006: 446).

    Turke a fannin Ilimi kamar yadda Gusau (2008, sh. 370) ya bayyana na nufin:

    Sa ƙ on da wa ƙ a take ɗ auke da shi. Idan an ce sa ƙ o kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa wa ƙ a tun daga farkonta har zuwa ƙ arshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba. Ashe ke nan, sa ƙ on da maka ɗ i yakan za ɓ a ya gina wa ƙ arsa, ya tauye kansa da kansa ya zuba ɗ iyanta bisa wasu za ɓ a ɓɓ un kalmomi da za su doshi wata babbar manufa ɗ aya, shi ake kira turke.

    Turakun Wa ƙ o ƙ in Asharall e

    Maka ɗ an Asharalle na jihar Katsina sun yi wa ƙ o ƙ i da yawa, wanda kowac c e tana da babban turken da ta ka ɗ aita da shi. A wannan bincike an kawo wasu manyan turaku na wa ƙ o ƙ in maka ɗ an Asharalle na jihar katsina da ake da su kamar haka: Turken yabo da na zuga da na ta’aziyya da na zambo da na ko ɗ a kai da na fa ɗ akarwa da na siyasa da kuma na soyayya.

    Turken Yabo

    Turken yabo shi ne turken da maka ɗ an baka suka fi yin wa ƙ a a kansa.

    Gusau (2008, sh. 376) ya bayyana ma’anar yabo da cewa:

    Mafi yawan wa ƙ o ƙ in manufofinsu sukan zamanto yabon wa ɗ anda ake yi wa su ne. Yabo shi ne ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amince wa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari. Ko kuma a iya cewa yabo wani lafazi ne da ake yi ga wani mutum domin a nuna halayensa da siffofinsa kyawawa da cewa abin so ne kuma abin ƙ auna ne.

    “Yabo a cikinsa maka ɗ i yakan yabi ubangidansa da ambaton darajar kakanninsa, da jarumtaka da kuma alheri” (Ibrahim, 1983, sh. 9).

    Bello (1976) da Yahya (1997) sun bayyana cewa akan yabi mutum ta ambaton addini ko asali da zuriya ko jarumta ko iya mulki ko kyauta ko kyan hali.

    Wannan bincike ya tsinto wasu wa ƙ o ƙ i da maka ɗ an asharalle na jihar Katsina suka yi amfani da turken yabo, kamar haka:

    Misali:

    Wa ƙ ar Hajiya Mariya Sunusi Ɗ antata , wadda Alhaji Sirajo Mai’asharalle ya yi:

    Jagora: Alhaji ya Mariya Sunusi,

    ‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi,

     

    Jagora: Najeriya ka game ta kwata,

    : Ba mata masu kallabi ba,

    : Had da mazan duk na ha ɗ e su su duka,

    : Ban ga ɗ iya mai kama da ke ba.

    ‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

     

    Jagora: Malaman ciki n Kano gaba ɗ ai,

    : Suna fa ɗ ar Mariya Sunusi,

    : Inda Kano Allah ya bamu ukku,

    : Kuma ukkun mai irin halinta,

    : Da talakawa ba su ƙ ara kuka.

    ‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

     

    Jagora: Dattawan cikin Kano gaba ɗ ai,

    : Suna fa ɗ ar Mariya Sunusi,

    : Yaushe rabon da ai irin halinta,

    : Tun zamanin nan na Annabawa.

    ‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

    (Sirajo Mai’asharalle: Wa ƙ ar Hajiya Mariya Sunusi Ɗ antata) .

    A wa ɗ annan ɗ iyan wa ƙ a da suka gabata, maka ɗ in ya yi ƙ o ƙ arin nuna kyawawan halayen Hajiya Mariya Sunusi Ɗ antata, a ɗ a na farko inda yake yabonta da cewa duk Nijeriya maza da mata babu mai irin halinta. Kamar yadda masana suka bayyana ambaton kyauta tubali ne na gina turken yabo.A ɗ a na biyu da na uku da aka kawo ya bayyana cewa tana da kyauta,wanda ya ce malaman Kano da dattawan Kano duk sun yabi halinta na kyauta da cewa da akwai masu kyauta irin ta guda uku da talakawa sun daina kukan talauci a Kano.

    A cikin wa ƙ ar dai ya yi amfani da ambaton zuriya wanda shi ma wani tubali ne da ake gina turken yabo da shi, kamar haka:

    Jagora: Uwar Wafa’ilu uwar su Abba,

    : Uwar su Sani uwar Aliyu,

    : Uwar su Fatima uwar Hadiza,

    : A Inna uwa mai hana mu kuka.

    ‘Y/Amshi: Alhajiya Mariya Sunusi.

    (Sirajo Mai’asharalle: Wa ƙ ar Mariya Sunusi Ɗ antata ).

    Haka ya mamaye wa ƙ ar da kalmomin yabo tun daga farkonta har ƙ arshenta.

    A wani misalin kuma, Amadu Sheme ya yi amfani da turken yabo a wa ƙ o ƙ insa. Misali: Wa ƙ ar “Sarkin Birnin Gwari” wadda ya yi wa Alhaji Zubairu Sarkin Birnin Gwari.

    G/Wa ƙ a: Sarkin Birnin Gwari,

    : Zubairu Sarki bawan Allah,

    Jagora: Sarki Zubairu shi ya biya mani Makka,

    `: Alhaji ya ƙ ara mani Makka ya ba ni gona,

    : Sarki ya ban gida kuma ya ban mota Sarki.

    ‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

    : Zubairu Sarki ba w an Allah.

    Jagora: Na yarda shugabanci yai ma kyawu,

    : Baba sarauta tai ma kyawu,

    : Ga ka da ilimi,

    : Ga son Allah,

    : Ga sadaka kuma ga alheri,

    : Da taimako ga dubun al’umma Sarki.

    ‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

    : Zubairu Sarki ba w an Allah.

     

    Jagora: Kai ba ni ke fa ɗ i ba,

    : Amadu me mai wa ƙ a,

    : Malamanmu na Birnin Gwari,

    : Suna ji sun canja mai suna,

    : Mai ƙ ur’ani jeri-jeri,

    : Ga su a mota,

    : Ga su a ɗ akin kwantawarsa Sarki.

    ‘Y/Amshi: Sarkin Birnin Gwari,

    : Zubairu Sarki bawan Allah.

    (Amadu Sheme: Wa ƙ ar Sarkin Birnin Gwari Zubairu)

    A wa ɗ annan ɗ iya da suka gabata ya yabi Sarki da kyawawan halaye irin na kyauta da ilimi da son Allah (addini) da sadaka da taimako da ri ƙ o da addini, wanda har ya hakaito cewa malaman Birnin Gwari sun canja masa suna zuwa Mai ƙ ur’ani jeri-jeri.

    Haka ya ci gaba da ambaton kyawawan halaye da zuriya da nasaba da addini da kyauta da addu’a da ambaton abokan arziki, wa ɗ annan tubala su suka mamaye wa ƙ ar tun daga farko har ƙ arshe. Don haka sun tabbatar da turken wa ƙ ar yabo ne.

    Turken Ta’aziyya

    Ta’aziyya na nufin “gaisuwa da ake yi wa mutanen da aka yi wa mutuwa don sanyaya musu zuciya” (CNHN, 2006, sh.416).

    Wannan kalma ta ta’aziya tana nuna juyayi ko alhini game da rasuwar wani masoyi, sannan da tuna wasu abubuwan alheri da ya yi a lokacin da yake raye, daga nan kuma sai a yi kukan rashinsa.Ta’aziyya takan ƙ unshi yi wa mutanen mamacin gaisuwa da taya su juyayi da ba su ha ƙ uri sa’annan da ro ƙ ar wa mamacin gafara da sauransu (Gusau, 2008, sh. 379).

    Duba da wa ɗ annan bayanai aka fahimci cewa ana gina turken ta’aziyya ta hanyar nuna tausayi da nadama tare da yin addu’a ko nuna ba ƙ in cikin rabuwa da mamaci ko yabon kyan halin mamaci.

    A wannan bincike an fito da wasu wa ƙ o ƙ i da maka ɗ an asharalle na Jihar Katsina suka yi masu ɗ auke da turken ta’aziyya. Kamar haka:

    Misali:

    Wa ƙ ar “Ta’aziyyar Marigayi Sarkin Katsina Kabir Usman” wadda Usamatu Iliyasu Wada Uban Maryama ya yi:

    G/Wa ƙ a: Ya Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.         

    Jagora: Ya Zuljalali Allah Ubangiji,

      : Ka amshi duk ro ƙ ona da nike.

    ‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Ya Zuljalali Sarki mai kyauta,

      : Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

    ‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Yau Najeriya fa ɗ inta kakaf,

      : Duk mun yi tagumi mun rasa rashi.

    ‘Y/Amshi: Ya Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Ya Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Kamar in yi kuka mai ki ɗ a,

      : Lokacin Sarki Katsina,

      : Garinmu duk kaf ba a hwa ɗ a,

      : Talakawa duk sun yaba shiri.

    ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Fulani mu da manoma,

      : Inyamurai da ‘ya’yan Hausawa,

      : Gaba ɗ ayanmu Alhaji ba a hwa ɗ a.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Yarabawa har da kare-kare da Fulani,

      : Yau duk ba mu hwa ɗ a.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Ya samu mun ri ƙ e addini,

      : Ya samu mui zumunci kullum,

      : Kullum yana kira mu koma shiri.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Ku mui ta addu’a talakawa,

      : Mata da maza mui ta addu’a.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

     

    Jagora: Allah ya yahe ma laihin da ku kai x 2.

     ‘Y/Amshi: Allah ka ji ƙ an Sarkin Katsina.

    A wa ɗ annan ɗ iya maka ɗ in ya yi amfani da salo na addu’a da juyayi da tuna halayensa na kirki da iya mulki da son addini, kamar yadda masana suka bayyana cewa a yayin ta’aziyya ana nuna juyayi ko alhini game da rasuwar wani masoyi da kuma tuna ayyukansa na ƙ warai.Wanda tun a gindin wa ƙ ar ya fara da addu’a haka ya ci gaba da juyayi da alhini na rashin Sarkin har zuwa ƙ arshen wa ƙ ar.

    Haka ma, Alhaji Amadu Sheme ya yi wa ƙ ar ta’aziyya wadda ya yi wa tsohon shugaban ƙ asa na farar hula Umaru Musa ’Yar’aduwa, kamar haka:

    G/Wa ƙ a: Shugaban ƙ asa Allah ji ƙ an,

    : Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

     

    Jagora: Ummaru angon Baturiya,

    : Mai ban sha’awa,

    : Ƙ ani ga Shehu Musa ‘Yar’aduwa,

    ‘Y/Amshi: ’Yar’aduwa,

    : Shugaban ƙ asa Allah ji ƙ an,

    : Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

     

    Jagora: Mu Umar,

    : Ka ri ƙ e mu tamkar ɗ a da iyaye.

    ‘Y/Amshi: Shugaban ƙ asa Allah ji ƙ an,

    : Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

     

    Jagora: Mu Umar ya ri ƙ e mu,

    : Tamkar ‘ya’ya da iyaye.

    ‘Y/Amshi: Shugaban ƙ asa Allah ji ƙ an,

    : Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

    (Sheme: Wa ƙ ar “Ta’aziyyar marigayi shugaban ƙ asa Ummaru Musa ‘Yar’aduwa”).

    A wa ɗ annan ɗ iyan wa ƙ ar da suka gabata maka ɗ in ya yi amfani da salon tuna abubuwan da ya yi na kyautata wa al’umma da yabo ha ɗ e da yabon kyawawan halayen shugaban ƙ asa wajen yin ta’aziyya, inda a wajen yabon yake danganta shi da matarsa da ɗ an’uwansa.

    A wajen yabon kyan hali kuwa ya bayyana yadda Ummaru Musa ‘Yar’aduwa ya ri ƙ e al’ummar Nijeriya kamar ri ƙ on ɗ a da iyaye.

    Ya sake kawo irin wannan salo na ambaton kyan hali a wani ɗ an wa ƙ ar kamar haka:

    Jagora: Kai jama’a ga shi babu rai nai ‘Yar’aduwa,

    : An rikirkita mu ƙ asar nan,

    : Mu ’yan arewa mun rasa inda akai,

    ‘Y/Amshi: Mu n rasa inda akai,

    : Shugaban ƙ asa Allah ji ƙ an,

    : Ummaru Musa ’Yar’aduwa.

    (Sheme : Wa ƙ ar Ta’aziyyar Marigayi Shugaban Ƙ asa Umaru Musa).

    A wannan ɗ an da ya gabata, yana yabon mamacin ne da cewa lokacin da yana da rai ana zaune lafiya, amma bayan ransa an rasa zaman lafiya a ƙ asa musamman a Arewa. Haka ya ci gaba da kawo kyawawan halaye na mamaci da kuma yabo, wanda wa ɗ annan su ne suka ƙ arfafi turken har ya kai ga isar da sa ƙ on.

    Turken Zambo

    Zambo na nufin “ ƙ aga wa mutum magana wadda za ta muzanta shi ta ɓ ata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba”, (CNHN, 2006, sh. 489).

    Zambo kalma ce wadda ake amfani da ita a matsayin kishiyar yabo. Akan siffanta mutum da wasu siffofi munana wa ɗ anda za su wula ƙ anta shi ko su jawo masa rashin martaba a idon mutane, tare da kau da kai wannan mutum yana da wa ɗ annan siffofi ko ba shi da su. Akan ƙ ara gishiri a zambo don a da ɗ a lalata hali ko ɗ abi’ar wanda ake yi wa shi (Gusau, 2008; sh. 380).

    Sa’id (2002, sh. 214-215) ya bayyana ma’anar zambo da cewa: “Zambo shi ne jifar wani mutum da mugwayen maganganu na cin mutunci da suka saboda wata gaba da ta shiga tsakani”.

    Ken nan akan gina turken zambo ta amfani da: Muzantawa ko ɓ ace ko zagi da kuma wula ƙ antarwa. A wannan bincike, an gano wa ƙ o ƙ in da maka ɗ an asharalle na jihar Katsina suka yi masu ɗ auke da turken zambo zalla, ga misalan wasu daga cikinsu.

    G/Wa ƙ a: Shanuwa mai ƙ ahwa da lalle,

    : Farin ciki ne muke da murna.

     

    Jagora: Garinmu ya da uwa za su karuwanci.

    ‘Y/Amshi: Kowacce ta ɗ auki ’yar jakarta.

    Jagora: Shegu.

    ‘Y/Amshi: Shamu wa mai ƙ ahwa da lalle,

    : Farin ciki ne mu ke da murna.

     

    Jagora: Shegu cikin Kano,

    : Mun game a Kurna,

    : Suna ta biyar maza,

    : Ana ta kissa,

    : An ga maza.

    ‘Y/Amshi: Sai a fara nikin,

    : Shanuwa mai ƙ ahwa da lalle,

    : Farin ciki ne muke da murna.

    (Amadu Sheme: Wa ƙ ar Shamuwa).

    A wa ɗ annan ɗ iya da suka gabata maka ɗ in ya yi amfani da zagi, inda ya zage ‘ya da uwa, ya ce musu shegu ya kuma kira su karuwai.

    A wani ɗ an kuma na Sheme ya yi amfani da muzantawa ha ɗ e da zagi kamar haka:

    Jagora: Shekara n na n ƙ arya,

    : Wadda tai ta sami ciwo,

    : Wata ƙ arya,

    : Shamuwa ta ranga ɗ a man,

    : Tai mana ƙ arya,

    : Wai za ta Makka sa ll a,

    : Ko da ta kai Kano,

    : Ta sauka mota,

    : Shegiyar kantin kwari tawo sayayya,

    : Tana nufin,

    : Da za ta zo garinmu,

    : Mu tai mana ƙ arya,

    : Ta ce suna Madina,

    : Sai tai tunani,

    : Ai ba ta da zamzam,

    : Idan ta zo,

    : Mu za mu tambaye ta,

    : Saboda mu,

    : ’Ya’yan ganin ƙ wa ƙ waf ne,

    : A anguwar Ali ta sauka mota,

    : Aminu Barau,

    : Shi ya ba ta zamzam,

    : Ta zo gida,

    : Ta raba ma dangi.

    ‘Y/Amshi: Shamuwa mai ƙ ahwa da lalle,

    : Farin ciki ne muke da murna.

    A wannan ɗ a da ya gabata Amadu sheme ya muzanta wacce yake wa wa ƙ ar, domin siffanta ta da ƙ arya wadda har ƙ aryar ta sa ta ciwo. Domin ƙ aryar ta zuwa Makka ta yi. Kuma wannan wa ƙ a ya yi ta ne ga wata mata da ta ce za ta ba shi ’yarta ya aura daga baya ta fasa ba shi kamar yadda ya fa ɗ a a wa ƙ ar, kamar haka:

    Jagora: To jam a ’a wannan wa ƙ ar,

    : Kun san ta shamuwa ce,

    : Duk ɗ an Sheme ya yarda ni na yi ta,

    : Kuma tilar ne ya sa ni wagga wa ƙ ar,

    : Saboda Shamuwa ni ta zambace ni,

    : Shegiya ina cikin garinmu,

    : Tai mani ƙ arya wai za ta ba ni ‘yarta ,

    : Aka sa rana,

    : Da har ina ta murna,

    : In na samo riga shegiyar ta ƙ wace,

    : Hula mai kyau sai na tsikaro ta hi ƙ e,

    : Takalmi mai kyau ni na sayo ta ƙ wace

    : Ban damu ba don ta ce za ta ba ni ’yarta,

    : Ran ɗ aurin aure,

    : Har nai kiran mawa ƙ a,

    : Tai gyaran murya,

    : An zo biki a Sheme,

    : An zo biki na ɗ an’uwa a cashe,

    : Muna zaton tun da safe za a ɗ aura,

    : Shegiyar,

    : Sai ta ce a ɗ an jira ta,

    : Sai an sallar Azahar,

    : Ɗ aya da rabi karyar ta shige a ɗ aki,

    : Ta ce da ni,

    : Wai ta fasa ba ni ’yarta,

    : Yo kina ta hauka ke,

    : Kin hana ni ’yarki.

    ‘Y/Amshi: A cikin gari an ka bani dozen,

    : Shamuwa mai ƙ ahwa da lalle,

    : Farin ciki ne m uke da murna.

    (Amadu Sheme: Wa ƙ ar Shamuwa) .

     

    Haka ma, Abashe Galadanci ya yi wa ƙ a mai ɗ auke da turken zambo, kamar haka:

    G/Wa ƙ a: ’Yar gadagalle gadagalle.

     

    Jagora: Ko uwarta ce gadagalle,

    : Ubanta Sarkin bori.

     

    ‘Y/Amshi: Sarkin bori,

    : ‘Yargadagalle gadagalle.

     

    Jagora: Sun ce ubanta sarkin bori,

    : Uwarta ce gadagalle.

    ‘Y/Amshi: ’Yar banza gadagalle.

     Jagora: Ji ƙ aninta ya lalace,

    ‘Y/Amshi: ’Yargadagalle gadagalle.

    A wa ɗ annan ɗ iya da suka gabata maka ɗ in ya yi amfani da zagi gami da wula ƙ antarwa ƙ uru- ƙ uru, inda ya zage wadda yake yi wa zambo. Ya kira mahaifinta da ɗ an bori mahaifiyarta kuma gadagalle (mai yawon banza).

    Haka kuma, ya sake yi a wani ɗ an ya ha ɗ e da ita da iyayanta ya zage su ha ɗ e da muzantawa da wula ƙ antarwa, kamar haka:

    Jagora: ’Yargadagalle kin zama gawo,

    : Matattarar tsuntsaye ’yargagalle.

    ‘Y/Amshi: Yargadagalle gadagalle.

     

    Jagora: Ƙ anin uwatta ya kwanta,

    : Ƙ anin ubanta ya kwanta.

    ‘Y/Amshi: ’Yargadalle gadagalle.

    Haka ya ci gaba da kawo irin wa ɗ annan munanan kalamai cikin wa ƙ ar tun daga farkonta har zuwa ƙ arshe. Hakan ya sa aka tabbatar da cewa turken wa ƙ ar zambo ne.

    Turken Ko ɗ a Kai

    Wannan kalma ta ko ɗ a kai Gusau (2008, sh. 388) ya bayyana ma’anarta kamar haka:

    Ko ɗ a kai ko wasa kai na nufin mutum ya fa ɗ i wata shahara ko ƙ asaita ko ɗ aukaka da yake ganin yana da ita. Wato ambato ne na abubu wan ƙ asaita ko burgewa da mutum yake da su ko yake aikatawa. Wani bi akan ha ɗ a da wuce gona da iri inda mutum zai bayyana fifikonsa kan sauran jama’a, ko ya nuna wata zala ƙ arsa kan wasu da sauran hanyoyin fifitawa. A irin wannan ha ɗ i mutum yakan zuga kansa da kansa ne.

    A wajen ko ɗ a kai “Maka ɗ i yakan wasa kansa da cewa babu wani maka ɗ in da ya fi shi” (Ibrahim, 1983, sh. 9).

    Ashe ke nan, akan ko ɗ a kai ta ɓ angarori kamar haka: Cika-baki ko alfahari ko fankama.

    Maka ɗ an asharalle na jihar Katsina sun yi amfani da turken ko ɗ a kai a cikin wa ƙ o ƙ insu. Misali:

    Alhaji Sirajo Mai’ashaalle a wa ƙ ar A sha ruwa ba don sabo ba.

      G/Wa ƙ a: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Kai ku buga min tambura,

    : Sirajo zai magana mai ƙ wari,

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sharuwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Ye yere-yere idan kura ta koka,

    : Karnuka bana sai ai baya.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Kai ƙ arya ta shekara ƙ arya,

    : Gaskiya na nan matsayinta,

    : Yaro bai yi kamar babba ba.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Yara komin ɗ an’akuya ya ƙ ƙ osa,

    : Kar ya sake ya bi hanyar kura.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Idan kun ce ya bari ya bi ta,

    : Ku bar shi ya bi ta ta lalata shi.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

    (Sirajo Mai’asharalle : Wa ƙ ar a sha Ruwa ba Don Sabo ba).

    A wa ɗ annan ɗ iya da aka kawo maka ɗ in ya fifita kansa a kan sauron maka ɗ a inda ya nuna shi kura ne sauran maka ɗ a karnuka ne, sannan ya ce shi ne maka ɗ in gaskiya sauran duk na ƙ arya ne komai shekarun da suka yi suna wa ƙ a. Haka kuma ya ci gaba da cewa maka ɗ i wanda ba shi ba ɗ an’akuya ne ya kira kansa kura kuma ya ce kar ya sake ya bi hanyarsa idan ya ce zai bi kuka hana shi ya ƙ i, to ku ƙ yale shi zai lalata shi.

    Har wa yau, ya ci gaba da cewa:

    Jagora: Dakata mani ina zuwa ba fashi,

    : Duk wanda ya taru wurin nan,

    : In dai ku ɗ i yake son ba ni,

    : Kay ya matsa mani in mishi wa ƙ a,

    : In ya matsa mani nai mashi wa ƙ ai,

    : In ya sake na taso shi ga wa ƙ ai,

    : Har sai ya tafi ba ban kwana.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,   

    : Ba don sabo ba.

    A wannan ɗ a ma ya wasa kansa da cewa mutane nema suke ya yi musu wa ƙ a, har ya nai musu kashedi kar fa su matsa shi ya yi musu wa ƙ a don in ya fara yi wa mutum wa ƙ a sai ya ƙ arar da ku ɗ insa ya tafi ba sallama saboda da ɗ in wa ƙ ar.

    A wasu ɗ iyan wa ƙ ar kuma cewa yake:

    Jagora: Shin ina mawa ƙ a ’yan zamani,

    : ’Yan yara-yara ƙ anana,

    : Je ka gaya musu albishirinsu,

    : Ya za su yi da ni ɗ an Hanza,

    : Ni Garkuwa na shata Mamman,

    : Duk wani mai wa ƙ a a ƙ asar nan,

    : Sai dai ya ce mani ya girme ni,

    : Ko ya gwada mani ƙ wambon iska,

    : Ni kau ni hi su yawan motoci.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Yanzu duk wani mai wa ƙ a ƙ asan nan,

    : Baba Shata baban Hajjo,

    : Yad dafa kanmu yay yi du’a’i,

    : Ya ɗ auki garkuwa yab ba ni,

    : To addu’asshi kau ta bi ni,

    : Yanzu ƙ wa ƙ walwata ta bushe,

    : Duk wani mai wa ƙ a a ƙ asar nan,

    : Nijeriya ƙ asarmu ta gado,

    : In dai da Hausa za ya yi wa ƙ a,

    : To sai dai a ha ɗ a mu ya ruga,

    : Na tattaro su na kamo su,

    : Duk na zuba s u cikin aljihu.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

     

    Jagora: Ina yara-yara ‘yan’asharalle?

    : A gaya musu yau ga dadi,

    : Yau dai sirajo ga ni firidom,

    : Alhaji ban ta ɓ a zawwa nan ba,

    : Sai ’ya’yana aka ɗ auka,

    : To yau ga shi da kaina Mamman,

    : Ni ne Maiasharallen zurfan,

    : Duk wani mai wa ƙ a a ƙ asar nan,

    : In dai da talle za ya yi wa ƙ a,

    : To ku tabbata yarona ne,

    : Ni ke asharlle su sace,

    : Har me Samandare ni nai ta,

    : Lobiyalaba ni nai ta,

    : Kuma Lambarko ni nai ta,

    : Ta yi rawa ɗ akin ni nai ta,

    : Hatta Ware gajai ni nai ta,

    : ’Yan yara-yara duk suka ɗ auka,

                ; Amma wanga ki ɗ in da na fara,

    : Duk ya akai ya fi ƙ arfin sata,

    : Dole su bar ni da ni da abina.

    ‘Y/Amshi: Ye ye yere-yere a sha ruwa,

    : Ba don sabo ba.

    (Sirajo Mai’asharlle: Wa ƙ a a Sha Ruwa ba Don Sabo ba)

     

    Idan aka yi la’akari da wa ɗ annan ɗ iya da suka gabata, maka ɗ in ya yi ƙ o ƙ arin kambama kansa da cewa yanzu duk wani mai wa ƙ a da Hausa a Nijeirya ya fi shi. Sannan ya dawo ya ce duk mai ki ɗ a da talle yaronsa ne shi ya ke wa ƙ a su sace, ya kuma lissafo wa ƙ o ƙ in da ya yi suka sace.

    Turken Fa ɗ akarwa

    Fa ɗ akarwa a harshe tana daidai da fa ɗ aka wadda take nufin “farka ko lura ko kula”. (CNHN, 2006; sh. 129). A ma’ana ta fannu kuwa kamar yadda Gusau (2015, sh. 40-41) ya ce fa ɗ akarwa na nufin:

    A ko da yaushe turke na fa ɗ akarwa yakan yi ƙ o ƙ ari ne ya samar wa da mutane wasu abubuwa sababbi da suke faruwa a rayuwar yau da gobe. Duk abin da ya doso ƙ asa wanda jama’a ba su da wani cikakken bayaninsa sau tari, da yawa wa ƙ o ƙ in baka sukan yi ƙ o ƙ arin fahimtar da jama’a shi. Wasu lokuta gwamnati da kanta takan umarci sarakuna su fa ɗ akar da talakawansu, game da irin wa ɗ annan abubuwa masu aukuwa. Ta haka ne wa ƙ o ƙ in baka suke taimakawa wajen yi wa jama’a sanarwa da wa’azi da garga ɗ i da jan kunne da kuma wayar da kai.

    Don haka fa ɗ akarwa na nufin garga ɗ i ko nasiha ko kuma ilmantarwa ko tarbiyantarwa tare da wayar da kai ko hannunka-mai-sanda gami da tunasarwa. Maka ɗ an asharalle na jihar Katsina sun fa ɗ akar a fannoni daban-daban a cikin wa ƙ o ƙ insu. Misali: Wa ƙ ar a sha ruwa don sabo wadda Audu Boda ya rera, inda yake tunasar da fa ɗ akar da mutane cewa komai yana hannun Allah, arziki da talauci da rayuwa da mutuwa da sauransu.

    G/Wa ƙ a: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yu n wa ba.

     

    Jagora: Ni Audu Boda da na lura,

    : A r zi ƙ i nufin Allah ne,

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

     

    Jagora: Da arzi ƙ i da karatu,

    : Kai duka nufin Allah ne.

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

     

    Jagora: Sarari dajin Allah,

    : Allah yake rayawa.

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

     

    Jagora: Allah shi ka kashewa,

    : Allah ke rayawa.

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

     

    Jagora: Ka ga gurgu bai da ƙ afafu,

    : Allah ke raya shi.

     

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

     

    Jagora: Makaho yana duhu,

    : Allah ke fidda shi.

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba magnain yunwa ba.

     

    Jagora: Ji dabba ba ta da baki,

    : Allah ke ci da ta,

    ‘Y/Amshi: A sha ruwa don sabo,

    : Ba maganin yunwa ba.

      (Abdu Boda : Wa ƙ ar a sha ruwa don sabo).

    Wa ɗ annan ɗ iyan wa ƙ a da suka gabata fa ɗ akarwa ce tsantsa, wadda Audu Boda yake yi wa al’umma kan cewa su mayar da komai gurin Allah. Domin cewa babu wanda zai sami komai sai da nufin Allah. Ya kawo misalai na ilimi da arziki duka nufin Allah ne. Sannan kuma ya ba da misali na cewa duk inda kake Allah ke raya ka, ya kuma kawo misalai na masu rauni duk Allah yana ba su abin da suke rayuwa. Haka ya ci gaba da irin wannan fa ɗ akarwa har ƙ arshen wa ƙ ar, don haka turkenta ya zama fa ɗ akarwa.

    Turken Siyasa

    A luggace siyasa na nufin “tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su (CNHN, 2006; sh. 397).

    Ma’anar kalmar siyasa ta fannu kuwa tana nufin: “Hanya ko dabara wadda ake amfani da ita a cim ma wani mataki na shugabancin al’umma. A tsarin siyasa akwai siyar addini da siyasar kishin kai da siyasar kishin ƙ asa da siyasar jam’iyya” (Gusau, 2002; sh. 34).

    Gusau ya ƙ ara da cewa:

    T urken siyasa ya ƙ unshi wa ƙ o ƙ i wa ɗ anda ake gina su a kan manyan sa ƙ onni na siyasa da suka ha ɗ a da bayyana manufofin jam’iyya ko yi wa jam’iyya kamfen ko wayar da kai kan za ɓ e ko yabon ’yan siyasa da sauransu . (Gusau, 2002; sh. 34).

    Ta la’akari da wa ɗ annan bayanai da suka gabata, za a iya kasa wa ƙ o ƙ in siyasa zuwa gida uku kamar haka:

    a.      Wa ƙ o ƙ in Siyasar kishin kai.

    b.      Wa ƙ o ƙ in Siyasar kishin ƙ asa.

    c.       Wa ƙ o ƙ in Siyasar jam’iyya.

    Daga cikin wa ƙ o ƙ i masu turken siyasa akwai wa ɗ anda aka yi su a kan kishin ƙ asa da kishin kai da kuma kishin addini. Alhaji Amadu Sheme ya yi wa ƙ a ta neman jiha a yankinsu wadda za mu iya ɗ ora ta a kan kishin ƙ asa. Misali:

    G/Wa ƙ a: ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

    : Allah ya ba mu jiha ta Kara ɗ uwa.

     

    Jagora: Yara in muka samu jiha a Kara ɗ uwa,

    : Hedikwata.

    ‘Y/Amshi: Na birnin Funtuwa.

    Jagora: Ai ko hedikwata.

    ‘Y/Amshi: Na birnin Funtuwa.

    Jagora: In ko hedikwata aka yi ta a Funtuwa,

    : Sai in biya.

    ‘Y/Amshi: In kar ɓ a in wuce.

    Jagora: Da na zo sai in biya.

    ‘Y/Amshi: In kar ɓ a in wuce,

    : ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

    : Allah ya ba mu jiha ta Kara ɗ uwa.

    A wannan ɗ an wa ƙ a da ya gabata Amadu Sheme ya nuna inda suke bu ƙ ata da ya zama babban birnin Jiha, idan har sun sami Jihar da suke nema wadda suka kira da Kara ɗ uwa. Sannan ya ci gaba da bayyana arzi ƙ in da ke yankinsu a matsayin dalilansu da suka sa suke ganin yankin nasu ya cancanci zama Jiha, kamar haka:

    Jagora: In ma’adanai ke sawa ai Jiha,

    : Ma’adanai da yawa a Kara ɗ uwa,

    : Farar ƙ asa,

    : Na birnin Ƙ an ƙ ara,

    : Idan kana so.

    ‘Y/Amshi: Zo a gwada maka.

     

    Jagora: Dutsen ku ɗ i,

    : Akwai kwaranda,

    : Birnin Sheme.

    ‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka.

     

    Jagora: Sannan muna da zinarenmu,

    : A Sabuwa.

    ‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka.

     

    Jagora: Malam muna da alherinmu a Sheme,

    : Muna da sinadarin da ake ha ɗ a kwano.

    ‘Y/Amshi: Idan kana so zo a gwada maka,

    : ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

    : Allah ya ba mu jiha a Kara ɗ uwa.

      (Amadu Sheme : Wa ƙ ar Neman Jihar Kara ɗ uwa).

    A wannan ɗ a kuma ya nuna irin arzikin da ke ƙ ananan hukomimin da suke ƙ ar ƙ ashin Jihar da suke nema. Wanda idan har ma’adanai ko arzikin ƙ asa ke sawa a yi Jiha to akwai su a yankin da suke neman Jihar. Haka kuma ya bayyana ƙ ananan hukomomin da za su zama cikin sabuwar Jihar kamar haka:

    Jagora: A kan wannan neman Jiha,

    : In muka samu Kara ɗ uwa,

    : Musawa Local Go v ernment ,

    : Suna cikin kwamitin.

    ‘Y/Amshi: Neman J iha .

    Jagora: Musawa Local Go v enrment ,

    : Sun hwa ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

    : Neman Jiha.

     Jagora: Matazu Local Go v ernment ,

    : Sun hwa ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

    : Neman Jiha.

    Jagora: Ƙ an ƙ ara Local Go v ernment,

    : Sun hwa ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamititin,

    : Neman Jiha.

    Jagora: Malunfashi Local Go v ernment,

    : Sun hwa ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

    : Neman Jiha.

    Jagora: Bakori Local Go v ernment ,

    : Sun k h a ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

    : Neman Jiha.

    Jagora: Ƙ afur Local Go v ernment,

    : Sun hwa ɗ i.

    ‘Y/Amshi: Suna cikin kwamitin,

    : Neman Jiha,

    : ’Yan’uwa kowa ya yi addu’a,

    : Allah ya ba mu Jiha a Kara ɗ uwa.

    (Amadu Sheme : Wa ƙ ar Neman Jihar Kara ɗ uwa).

    Turken Soyayya

    Kalmar soyayya a ma’ana ta harshe na nufin “nuna ƙ auna daga ɓ angarori biyu na masu ƙ aunar juna, musamman mace da namiji” (CNHN, 2006; sh. 398).

    Soyayya kuwa tana nufin so da yake aukuwa a tsak a nain masoya guda biyu inda za su dinga ƙ aunar juna, suna masu begen juna” (Gusau, 2008; sh. 393).

    Maka ɗ a da mawa ƙ a kan gina wa ƙ a a kan turken soyayya ta ɓ angarori kamar haka: Ko dai su yi wa ƙ a a kan soyayyar da suke yi da wata, ko kuma su yi wa ƙ a a kan soyayyar da ke tsakanin wasu ba su ba, ko kuma su yi wa ƙ a a kan soyayyar kanta.

    Dangane da turken soyayya a wajen maka ɗ an asharalle na jihar Katisna an same su ne a wajen maka ɗ i ɗ aya wato Audu Boda. Daga cikin wa ƙ o ƙ in da ya yi na soyayya akwai wadda ya yi wa soyayyar ita kanta kamar haka:

    G/Wa ƙ a: Soyayya da ɗ i ta fi zuma da ɗ i.

    Jagora: In na yi tunani,

    : Audu na san soyayya,

    : In nai nazarina,

    : Audu na san soyayya,

    : Don na ta ɓ a soyayya,

    : Ni na san soyayya,

    : Na san da ɗ inta,

    : Na san h a ɗ arinta,

    : Yara in so cuta ne,

    : Ha ƙ uri magani ne,

    : Wadda yac ci amana,

    : Amana kau za ta ci shi,

    : Mai ha ƙ uri mawadaci,

    : Wata ran zai dafa dutse.

    ‘Y/Amshi: Soyayya da ɗ i ta fi zuma da ɗ i.

    (Audu, Boda: Wa ƙ ar Soyayya)

    A wannan ɗ a da ya gabata Audu Boda ya yi bayani ne a kan soyayya na da da ɗ i kuma tana da ha ɗ ari, don haka yake ba wa matasa shawara da su yi takatsantsan idan so cuta ne to ha ƙ uri magani ne. Ma’ana, idan mutum ya kamu da soyayyar wani ya ga zai gamu da wata wahala to ya yi ha ƙ uri.

    A wani ɗ an kuma ya bayyana ha ɗ arin soyayya da cewa: Shi ne ranar rabuwa, kamar haka:

    Jagora: Kun ji akwai wata rana,

    : Wadda nake tsoranta,

    : To du akwai wata rana,

    : Wadda nake tsoranta,

    : To da ɗ a sai wata rana,

    : Wadda nake tsoranta,

    : In na yi tunani,

    : dole nake tsoranta,

    : Ni in nai nazarina,

    : Sai na ri ƙ a tsoranta,

    : Don rabuwa da masoya,

    : Dole yai mamu ciwo.

    ‘Y/Amshi: Soyayya da ɗ i ina soyayya.

    (Audu Boda: Wa ƙ ar Soyayya)

    Kammalawa

    Wannan nazari ya yi bayani a kan wa ƙ o ƙ in Asharalle wanda aka yi amfani da ra’in Gusau (2003) na nazarin wa ƙ ar baka Bahaushiya (WBB) aka kuma yi aiki da ɓ angaren nazarin turkena ra’in a wannan bincike. A nazari n an fahimci yadda maka ɗ an Asharalle suke amfani da salo daban - daban a gina turakun wa ƙ o ƙ insu. Wannan nazari da aka yi na turke a wa ƙ o ƙ in Asharalle ya nuna mana maka ɗ an suna da ƙ warewa a wa ƙ a saboda an zayyana yadda suke gina turakun wa ƙ o ƙ insu da kuma aiwatar da su. Bugu-da- ƙ ari nazari n zai ba da haske da gagarumar gudummawa a fagen ilimi ga masana da manazarta domin ci gaba da yin nazari a kan wa ƙ o ƙ in Asharalle . , An kuma adana fasahohi da hikimomin maka ɗ an domin yin bitar su a nan gaba. A ƙ arshe an fahimci yadda nazarin turke ke fito da dabarun maka ɗ i da hikimominsa da fasaharsa wajen gina turaku mabambanta. Don haka wannan nazari ya nuna yadda maka ɗ an Asharalle suke shirya zubin ɗ iyan wa ƙ o ƙ insu da sarrafa su, inda aka yi amfani da ɗ iyan wa ƙ o ƙ insu a matsayin hujja.

    Manazarta

    Ammani, M. (2019). Nazarin Awon Baka da Aiwatar wa a Wa ƙ o ƙ in Nafi’u Yakubu Baba. Kundin Digiri na Uku (PhD). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

    Bello, G. (1976). Yabo da Zuga da Zambo a Wa ƙ o ƙ in Sarauta Harsunan Nijeriya, V ol . V I:21-34.

    CNHN (2006). Ƙ amusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello Uni v ersity Press.

    Gusau, S. M. (2002). Sarkin Taushi Salihu Janki ɗ i , Kaduna: Baraka Press and Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazarin Wa ƙ ar Baka , Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2008). Wa ƙ o ƙ in Baka a Ƙ asar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2011). “Tarihi da Hanyar Nazarin Wa ƙ ar Baka Bahaushiya a Ta ƙ aice”. A Cikin Funtua, A. I. & Gusau, S. M. (Editoci), Wa ƙ o ƙ in Baka na Hausa . Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau , S. M. (2011). “Ta ƙ aitaccen Tarke a Kan Wa ƙ ar Jami’a ta Aminu Ladan Abubakar”. Ma ƙ ala a taron wa ƙ a a bakin mai ita na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2014). Wa ƙ ar Baka Bahaushiya , Kano: Bayero Uni v ersity. Inagural Lecture serial no. 14.

    Gusau, S. M. (2015). Mazhabobi da Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa, Kano: Century Research and Publication Limited.

    Gusau, S.M. (2015). Abdu Karen Gusau, Kano: Century Research and Publication Limited.

    Gusau, S.M. (2016). Ƙ amusun Kayan Ki ɗ an Hausa , Kano: Century Research and Publication Limited.

    Ibrahim, M. S. (1983). Kowa ya Sha Ki ɗ a , Lagos: Longman Nigeria Plc.

    Kurawa, M.A. (2019)Nazarin Turke da Awon Baka a Wa ƙ o ƙ in Asharalle a Jihar Katsina. Kundin digiri na Biyu . Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

    Sa'id, B. (2002). Rubutattun Wa ƙ o ƙ in Hausa a Ƙ arni na Ashirin a Jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara Nazari a Kan Bun ƙ asarsu da Hikimomin da ke cikinsu (Kundin Digiri na Uku). Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano.

    Yahya, A.B. (1997) Jigon Wa ƙ ar Baka. Kaduna: Fis Media Ser v ices.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.