Table of Contents
Kwatancin
Karin Maganar Hausa Da Manganci
Ta
Fuskar Jigo
Na
ABDULKADIR, Ginsau PhD
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyar Harshe
Jami’ar Sule Lamido Kafin Hausa, Jigawa
0803 237 7941/0705 282 0708
abdulkadirgins2017@gmail.com
/
ginsau.a@slu.edu.ng
Tsakure
Manganci wani yare ne da wata kabila ke amfani da
shi wajen sadarwa, masu amfani da shi su ake cewa Mangawa. Ana samun su a
yankin kasar Ha
ɗ
eja da ke Jihar Jigawa.
Sun caku
ɗ
a da Hausawa matuka, wannan
ya sa kusan al’adunsu da yanayin zamanakewarsu suke cu
ɗ
anya da juna. Domin akan sami auratayya da harkokin
kasuwanci da ma sauran al’amuran gudanar da rayuwa da juna. Saboda haka a
ɓ
angaren harshe da
adabi, ba abin mamaki ba ne domin an sami kamanceceniya a azancin magana da
yadda ake amfani da aron kalmomi wa juna. Irin wannan ta sa ake samun ha
ɓ
akar adabi, a
ɓ
angaren
karin magana ta fuskar jigonsu a wa
ɗ
annan
harsuna mabambantan juna. Yin hakan kuma yana kara bunkasa harshe da adabi tare
da nuna alaka da juna, sannan kuma da fito
da muhimmancin zaman lafiya da al’ummun ke da shi. A wannan takarda an nazarci
Karin maganganun Hausawa da Mangawa ne ta fuskar jigon tarrbiyya, musamman abin
da ya shafi ha
ƙ
uri da juriya da neman na kai wato sana’a. An
kwatanta Karin maganganun an gano suna da kamanceceniya da juna ta fuskar jigoginsu.
Ke
ɓ
a
ɓɓ
un Kalmomi:
Hausawa,
Mangawa, Karin Magana, Jigo, Tarbiyya, Ha
ƙ
uri, Juriya, Sana’a
1.1
Gabatarwa
Kwatanci na nufin kawo abubuwa guda biyu ko
fiye domin nuna ala
ƙ
a ko bambancinsu. Jigo kuma na nufin sa
ƙ
on
da ake son isarwa ga mai
sauraro.
Kamar yadda Bunza (2009) ya ce, jigo wata da
ɗ
a
ɗɗ
iyar kalma ce, kuma bisa ga asali kalmar ta
Hausa ce. Kalmar jigo a Hausa kan iya
ɗ
aukar
ma’anar wani abin yin ban ruwa na kayan lambu. Haka kuma kalmar jigo kan iya
ɗ
aukar ma’anar shugaba, ko kuma jagora na wani
abu na musamman da aka fuskanta. Amma a adabin Hausa, kalmar jigo tana nufin sa
ƙ
on
da ke
ƙ
unshe cikin adabin.
A wannan takarda an nazarci karin maganar Hausa
da Manganci ne ta fuskar jigo, an kwatantasu ta fuskoki daban-daban, inda suke
da ala
ƙ
a ta fuskar jigon ha
ƙ
uri
da juriya da kuma sana’a.
C.N.H.N (2006:428) an bayyana kalmar tarbiya da
koyar da hali na gari. Shi kuwa Zarruk, da wasu (1982) sun bayyana ma’anar
tarbiyya da cewa “renon halaye ne da
ƙ
o
ƙ
arin shiryawa don yaro ya zama nagari kuma ya
iya kama kansa.” Akwai tarin karin maganganu a harshen Hausa da ke magana kan
tarbiyya. Mafi yawa na yin hannunka mai sanda kan aikata hali na gari, abin so,
musamman ga yara.
Kalmar ha
ƙ
uri kalma ce da ke da makusanciyar ala
ƙ
a
da kalmar juriya domin a yayin bayyana ma’anar ha
ƙ
uri
sai an yi amfani da kalmar juriya sannan ma’anar ta fito fili. Kamar yadda
Bargery (1934) ya yi amfani da kalmar juriya wajen fassara kalmar ha
ƙ
uri,
haka ma a cikin kamusun Hausa (2006) aka bayyana ma’anar ha
ƙ
uri
da cewa shi ne juriya ga wani abu na
ɓ
acin
rai ko masifa. Kodayake ma’anar ha
ƙ
uri ba ta takaita ga juriya ga masifa da
ɓ
acin rai ba, ta ha
ɗ
a da dagewa ga kowane yanayi ga gwagwarmayar
rayuwa, da fatan samun biyan bukata kome da
ɗ
ewa.
Ma’anar ha
ƙ
uri
na iya
ɗ
aukar ma’anar dogaro ga Allah
da mayar da al’amura gare shi, tare da kyakkyawar manufa. Karin magana kuma
wata muhimmiyar kafa ce ta nazarin
ɗ
aukacin
rayuwar al’umma. Haka al’amarin yake wajen nazarin jigon ha
ƙ
uri a karin magana. Daga
cikin sakonnin da karin magana ke isar wa game da ha
ƙ
uri akwai bayyana muhimmancin
ha
ƙ
uri ga
ɗ
an
’a
dam,
da kuma alfanu da ha
ƙ
uri
yake samarwa. Haka kuma akwai wa
ɗ
anda
matsayin ha
ƙ
uri
suke nunawa.
2.1 Karin Magana
A kamusun Bergery
,
(1934) an
bayyana
k
arin
magana
da cewa,
shi ne sauya tare da mur
ɗ
e ma’anar kalmomi a cikin
zance. A cikin Abraham
,
(1945) kuma,
cewa aka
yi, k
arin
magana na nufin adon magana. Yayin da C.N.H.N (2006) aka fassara Karin
Magana
da, magana ce ta musamman
wanda sai an yi tsokaci ake ganewa.
Kirk-Greene (1966) da yake
magana a kan karin magana, ya bayyana karin maganar da cewa
,
na
inganta al’adun al’umma da suka gada, da tarihin al’umma, da hikimomin al’umma.
Sai kuma
Skinner
(1980) ya bayyana cewa kusan ba nau’o’in adabin da ba a amfani da karin magana,
sai dai a al’ada an fi amfani da karin magana wajen tsarance. Umar (1980) kuma
ya ce, karin magana wata dun
ƙ
ulalliyar Jimla ce ’yar kil, mai sassa biyu da ta
ƙ
unshi zunzurutun ma’ana a
lokacin da aka yi bayani. Ya kuma kawo amfanin karin magana ga al’umma, ya ce
tana da amfani a cikin mu’amala da zancen yau da kullum na al’umma, akwai kuma
nuna
ƙ
warewar
harshe, da sanin harshe. A fahimtar Zaruk da Alhassan (1982:3)kuwa, cewa suka
yi, karin magana wani nazari ne na rayuwa a dun
ƙ
ule, cikin gajerun maganganu da misalai irin
na hikima. Sai suka
ƙ
ara da
cewa, Karin Magana bai fiye zuga ko ku
ɗ
a ba,
sai dai gwanintar kwatance.A
ɓ
angaren
Ɗ
angambo, (1984:38) kuma,
sai yace, karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko
‘yan kalmomi ka
ɗ
an, cikin hikima. Haka kuma, a wani wurin
Yahaya da
Ɗ
angambo,
(1986) sun bayyana karin magana a matsayin
ɗ
aya daga cikin nau’o’in zantukan hikima na Hausa, kuma
sun
ƙ
ara da
cewa, kowa na amfani da shi, yara da manya, maza da mata, a lokaci-lokaci.
La’akari da wa
ɗ
annan fassarorin ma’anar karin magana daga bakunan
magabata, mun fahimci karin magana a matsayin wani zance da ake dun
ƙ
ule magana ciki, domin
nusar da mai sauraro wajen aikata alheri ko hani ga barin mummunan al’amari.
Wannan ta sa al’ummar Hausawa
da Mangawa suke amfani da karin magana wajen bayar da tarbiyya a maganance.
3.1 Karin Magana Mai Jigon Tarbiyya
A
nan
an kawo karin magana masu jigon ha
ƙ
uri da juriya ne a harshen Hausa da Manganci,
an kwatanta su ta fuskar jigo, tare da bayanin
ma’anoninsu. Daga
ƙ
arshe kuma an ta
ɓ
o
wasu masu jigon sana’a. Saboda haka an bi tsarin kawo karin maganar Manganci a
farko sai kuma na Hausa ya biyo bayansa.
Manganci:
Kiska tin kirin tiya dungwaccai gamjiya namji.
(Icce tun yana
ɗ
anye ake tan
ƙ
wara
shi
)
Hausa:
Itace tun yana
ɗ
anye ake tan
ƙ
wasa
shi.
Wannan karin magana ana nusar da jama’a ne ta
hanyar yin hannunka mai sanda, ta yadda ya kamata a yiwa yara tarbiyya tun suna
ƙ
anana. Domin abin da yaro ya tashi da shi da wuya
in ya girma ya daina. Wannan ya yi daidai da fa
ɗ
in
Hausawa cewa, ‘tarbiyya daga gida takan fara’. Saboda haka ko a gidan akan fara
da tarbiyar yaro ne tun daga lokacin da ya fara fahimtar abubuwa, kamar yadda
zai yi idan ya ji matsuwa ta bahaya ko fitsari, da cin abinci ko kar
ɓ
a da hannun dama, da kuma hani a kan kwa
ɗ
ayi da rowa da makamantansu.
Manganci:
Na
kiri kura gibacciya guzarama naza koji bawo.
(D
a damuna guza ba
ta nisa)
Hausa:
Inda babban kare ya yi
fitsari a
nan
ƙ
arami yake yi.
Wannan karin maganar kuma yana koyar da al’umma
ne cewa, lalle su kiyaye wajen aikata abubuwan kirki da na banza. Saboda yaro
abin da ya gani babba yana yi, shi zai koya. Domin haka duk abin da babba ya
aikata yaro yakan kwaikwaya ne. Wannan yana nufin manya su zama masu ba da
kyawawan misalai ga yara domin su tashi da tarbiyya tagari.
Manganci:
Tazagana
gardama kare kam kuraye cifandibawo
(
Ƙ
aramin yaro mai gardama ba zai samu
kayan babba ba
)
Hausa:
Laifin babba rowa, laifin
yaro
ƙ
i
uya.
Wannan kuma yana hani ne da yin rowa ga manya
zuwa ga na
ƙ
asa da su, su kuma yara na
ƙ
asa
kada su yi ki
u
ya.
Saboda haka karin maganar yana
ƙ
o
ƙ
arin koyar da al’umma tarbiyya ne a kan wasu
muhimman al’amura na rayuwa, wato yin kyauta da gudun rowa.
Manganci:
Daraja
nma naftu karenimma koyina
(Darajar ka ta fi zaman kayan
)
Hausa:
Tsira da mutu
n
ci ya fi tsira da kaya.
Mutu
n
ci
yana
ɗ
aya daga cikin abubuwa
muhimmai da tarbiyya ta
ɗ
oru a kansa. Wannan ne ta sa
Hausawa da Mangawa suke da karin magana masu yawa da ke koyar da al’umma muhimmancin
mutumci. Saboda haka karin magana yana koyar da yadda ake tarbiyartar da
al’umma kan tsare mutunci
n
su.
Manganci:
Nan
jire kalgu kariye
(G
askiya rigar kaya
ce
)
Hausa:
Gaskiya rigar kaya
Kusan a kowane harshe ana da tarin karin
maganganu masu nuna muhimmancin gaskiya, da illar
ƙ
arya.
Duk wasu munanan abubuwa na rashin tarbiyya, abin da ke haddasa su ba ya wuce rashin
gaskiya. Duk wani mugun al’amari da aka aikata, idan aka duba za a tarar rashin
gaskiya ke haifar da shi. Domin haka, wannan karin magana ne dake koyar da ri
ƙ
on
gaskiya a rayuwar mutum. Hausawa da Mangawa suna amfani da wannan Karin magana
idan suna son nuna yadda gaskiya take da wahala a cikin rayuwar al’umma
ko kuma yayin da gaskiya ta yi halinta, ta
bayyana halin wani mutum a fili.
Manganci:
Kam
niya dangur nin jibadiya niye bari tiya badinmi
(In
mutum ya jifa ka da dutsi to kar ka rama
)
Hausa:
Ba a rama mugunta da
mugunta.
Wannan karin magana ne dake
ƙ
o
ƙ
arin
koyar da tarbiyya. Kamar yadda fassarar ke nunawa karin magana ne da ke hani a
kan rama mugunta da mugunta, domin inganta tarbiyyar al’umma, da kuma horo
wajen aikata abin kirki. Ana amfani da karin maganar a cikin al’ummar Mangawa
da Hausawa, domin mutane su kasance masu aikata alheri, saboda abin da ka shuka
shi za ka girba. Kuma su bar yin mugunta ga junansu, su kuma zama masu yafiya
wa juna.
Manganci:
Iyammam
gamiya Allah gamma (
In
ka bi iyayenka, ka bi
Allah)
Hausa:
Bin na gaba, bin Allah
Karin magana ne da ke nuna muhimmancin ladabi
da biyayya, a tarbiyyar al’umma. Ladabi da biyayya shi ne girmama na gaba, shi
ne abin da za a fara dubawa idan ana son nuna tarbiya ko rashinta a wajen yara.
Hausawa da Mangawa suna amfani da wannan karin magana domin ba yara tarbiyyar
su kasance masu ladabi da biyayya, musamman ga na gaba da su, wato wanda ya
girme su.
Manganci:
Malunmun
tima awo rawombe
(Malaminka shi ne abin
ƙ
aunarka
)
Hausa:
Malaminka abin
ƙ
aunarka.
Duk inda Malami yake akan
ɗ
auke shi tamkar uba ne, wani lokaci ma ya fi
uba kula da ba yara tarbiyya. Saboda haka Mangawa da Hausawa ke da karin Magana
da ke nuna muhimmancin malami ta yadda suke nuna girma da darajarsa ga al’umma.
Domin haka karin maganar yana
ƙ
o
ƙ
arin nuna darajar malami ne. Ana amfani da
wannan karin magana a al’ummar Mangawa da Hausawa wajen koyar da yara su
ƙ
aunaci
malamansu tare da girmamawa.
Manganci:
Awo
ginama kare kura cizangi (
Ƙ
aramin abu shi ke tada babban abu
)
Hausa:
Allura ta tono garma
Kusan komai na rayuwa da akwai tarbiyyar yadda
ake yin sa. Yawan magana da
ƙ
ananan maganganu wani nau’i ne na rashin
tarbiyya. Domin haka wannan karin magana ne da ke hani kan magana barkatai,
marar ma’ana, saboda tana iya jawo fitina a cikin al’umma. Ana amfani da wannan
karin magana wajen tarbiyantar da mutane cikin al’umma kan su san irin maganar
da za su yi, wato a tauna kafin a furzar, domin gudun
ƙ
aramar
magana kada ta haifar babba.
Manganci:
Unduwaye
Aman jubuya Aman tiya jibui
(K
owa ya ci amana, amana
za
ta ci shi)
Hausa:
Kowa ya ci amana, amana za
ta ci shi.
Tsare amana yana daga cikin kyakkyawar tarbiyya
a rayuwa. A wannan karin magana ana
ƙ
o
ƙ
arin cusa tarbiyya kan hani a bisa cin amanar
juna. Wato ke nan, karin magana ne mai koyar da illar cin amana a rayuwar
al’umma. Hausawa da Mangawa suna amfani da karin maganar ne wajen fa
ɗ
akar da mutane kan su zama masu rikon amana, su
guji cin amana. Saboda maci amana yana tare da kunya.
Manganci:
natu
kilabiya tabtu luwah kojina (
Z
aman lafiya ya fi zama
ɗ
an S
arki)
Hausa:
Kiwon lafiya, ya fi kiwon
dukiya.
Mai tsabta shi yake kula da kiwon lafiyarsa.
Ginshikin kiwon lafiya kuwa ita ce tsabta. Tsabta kuma tana daga cikin al’amura
kyakkyawana bayar da tarbiyya. Domin haka, wannan karin magana ne da ke nuna
muhimmancin lafiya da kiwonta a rayuwar
ɗ
an
Adam. Ana amfani da wannan karin magana a harshen Manganci da Hausa wajen fa
ɗ
akar da mutane da su yi kiwon lafiyarsu, saboda
ita ake komai na rayuwa. Kamar yadda ake cewa ‘lafiya uwar jiki babu mai fushi
da ke’.
3.2 Karin Magana Mai Jigon Hakuri da Juriya
Wa
ɗ
annan
kare-karen magana suna bayyana matsayin ha
ƙ
uri a rayuwar
ɗ
an
Adam, da cewa ha
ƙ
uri
baya
ɓ
aci. Haka kuma ha
ƙ
uri shi ne maganin wahala.
Duk wanda ya koshi da tarbiyya za a tarar da shi mai ha
ƙ
uri. Domin ha
ƙ
uri wani muhimmin abu ne
wajen gina tarbiyya a zukatan al’umma. Akwai abubuwa na sha’awa na jin da
ɗ
i, amma kuma na rashin tarbiyya ne. Amma sai a
hani mutum, a ce ya guji wa
ɗ
annan
abubuwa, wato ya hakurcewa zuciyarsa. Ana amfani da wa
ɗ
annan kare-karen magana a Manganci da Hausa
wajen tarbiyyar yara da su zama masu ha
ƙ
uri a rayuwa. Ire-iren wa
ɗ
annan kare-karen maganganun sun ha
ɗ
a da:
Manganci:
Kanadi
karun naftu duniyaye
(H
a
ƙ
uri maganin zaman
duniya)
Hausa:
Ha
ƙ
uri
maganin zaman duniya.
Wannan yana nuni da yin ha
ƙ
uri shi ne mabu
ɗ
in duk wata nasaara a rayuwar al’umma, wadda rashin
yin hakan yakan haifar da matsalolin rayuwa a shiga wahala. Saboda haka Hausawa
da Mangawa ke nusar da yara da sauran al’ummarsu wajen yin ha
ƙ
uri da jure duk wata wahala
da ake ciki domin yin ha
ƙ
uri
da ita a nemi mafita.
Manganci:
Gana
gana, gudo fazo cidi
(Da ka
ɗ
an-ka
ɗ
an tsuntsu yake kafa gida
)
Hausa:
Da ka
ɗ
an da ka
ɗ
an
tsuntsu yake gina shekarsa.
A wannan karin magana kuma ana koyar da halin
yin al’amura cikin nutsuwa, ba tare da yin gaggawa ba. Ba dare
ɗ
aya abu yake faruwa ba, sai a hankali kamar
yadda tsuntsu ke gina gidansa yana
ɗ
auko
tsinke
ɗ
aya da
ɗ
aya har ya gina. Saboda haka wannan karin
magana yana koyar da ha
ƙ
uri
da juriya ne wajen gudanar da al’amuran rayuwa.
Manganci:
Gashin
gowa badimi’a kangalen juwa bade.
(In ka jefar da
hawainiya ka jefar har karan
)
Hausa:
Komai nisar dare gari zai
waye.
Karin maganar na koyar da al’umma cewa duk
yadda abu ya kai ga da
ɗ
ewa akwai
ƙ
arshensa.
Domin haka ana koyar da juriya da ha
ƙ
uri ne. Wannan tarbiyya ce mai kyau wajen koyar
da mutum dogaro da ha
ƙ
uri.
Manganci:
Kargu
ni rannu kina ko kazakcina
(Na danne zuciyata, ko za ta iya)
Hausa:
Na danni zuciyata
Yana daga cikin tarbiyyar da ake ba
ɗ
an Adam wajen dannar zuciya yayin fushi da
ɓ
acin rai. Wannan ta sa Mangawa da Hausawa ba su
son mutum ya zamana mai zafin zuciya, mai saurin fushi da fusata. Saboda haka
ana bu
ƙ
atar mutum ya kasance mai dannar zuciyarsa a
kan wani abu na
ƙ
addara da ya same shi. Ko shugabanci ne akan ba
wa wanda yakan iya dannar zuciyarsa lokacin
ɓ
acin
rai. Wannan tarbiyya ce mai kyau.
Manganci:
Kam
kanadimazi tima kare wawatumawo
(Mahakurci mawadaci)
Hausa:
Maha
ƙ
urci
mawadaci.
Jigon wannan karin magana shi ne duk wanda ya
kasance mai ha
ƙ
uri,
to Allah ya yi masa babban arziki domin a wurin Mangawa da Hausawa da ha
ƙ
uri ake kai wa ga nasara har
a wadatu. Hausawa na da karin magana da ke cewa ‘ha
ƙ
uri jari ne a wurin mai shi’.
Duk inda aka ji maganar jari kuwa abu ne da ya shafi wadata.
Manganci:
Kam kanadiyazi tima kau kwadaje kalunju cai
(Mai
ha
ƙ
uri
shi
yake dafa dutsi
har
ya sha ruwansa)
Hausa:
Mai ha
ƙ
uri kan dafa dutse har ya sha
romonsa.
Wannan karin magana mai jigon ha
ƙ
uri, yana nuni ne da duk
wanda ya yi ha
ƙ
uri
ya jure da wani yanayi na wahala da ya samu kansa ciki, zai ga bayan wannan
wahala har ya kai ga biyan bu
ƙ
atarsa. Mangawa da Hausawa suna amfani da
wannan karin magana wajen koyar da al’ummarsu cewa, idan mutum ya yi ha
ƙ
uri abin da yake ganin kamar
ba zai yiwu ba, to sai ya ga ya yiwu har ya ci gajiyarsa. Wannan ya sa suka
kwatanta mai ha
ƙ
uri
da dafa dutse, ya nuna har ya yi laushi, ya fitar da romo, a sha. Wani abu da
ake ganin yana da kamar wuya.
Manganci:
Kanadi
tima kargun naftu duniyayewo (
H
akuri
shi ne
maganin zaman duniya)
Hausa:
Ha
ƙ
uri
maganin zaman duniya’
Karin maganar yana nuna rayuwar duniya
gwagwarmaya ce mai wuya, wata rana a sha zuma wata rana a sha ma
ɗ
aci. Wato za a iya samun kai cikin yanayin
farin ciki, wata rana kuma a shiga na bakin ciki. Al’ummar Mangawa da Hausawa
suna amfani da wannan karin magana wajen nusar da al’ummarsu cewa, zaman duniya
yana tare da matsaloli da sai an daure an yi ha
ƙ
uri sannan a sami zama lafiya.
Manganci:
Undu duwan naro kanindijiya huwunumiya tiya kojina cibandi
(Kowa
ya yi ha
ƙ
uri
da wuri in ya ci gaba zai samu wurin da ya fi shi)
Hausa:
Kowa ya ha
ƙ
ura
da wuri, zai samu wani a gaba.
Jigon wannan karin magana shi ne, wanda ya yi ha
ƙ
uri da halin da ya samu kansa
ciki, gaba zai samu wata kafar kai wa ga gurinsa. Wannan ma al’ummar Managawa
da Hausawa suna amfani da karin maganar wajen nusar da al’ummarsu cewa, duk
wanda ya yi ha
ƙ
uri
a kan wani abu, sai Allah ya fito masa da wata hanyar da zai samu abin da ya fi
wanda ya yi ha
ƙ
uri
a kan sa.
Manganci:
Kam bulun dorye danganajiya buniye gurejan (
Duk wanda ya dama kunun azahar, da daddare zai
jira)
Hausa:
Wanda ya ha
ƙ
ura
da kunun marece ya kai ga tuwon dare.
Karin maganar yana nufin duk abin da mutum ya
yi ha
ƙ
uri
a kansa zai samu madadinsa ko fiye da shi ba da da
ɗ
ewa ba. Saboda haka fassarar karin maganar tana
nuni ne da koyar da juriya kan abin da mutum ya sa ran samu, sai kuma bai samu
a lokacin da yake bukatar sa ba. A dalilin ha
ƙ
uri da juriya da ya yi, sai ya samu fiye da
abin da ya rasa.
3.3 Karin Magana Mai Jigon Sana’a
Sana’a wata babbar hanya ce da ake bi wajen
gudanar da rayuwa domin inganta ta. Saboda haka a cikin al’umma, duk wadda ba
shi da sana’a ake masa kallon biyu ahu, wato marar aikin yi, cima-zaune. Wannan
ta sa Hausawa da Mangawa ke yin Karin Magana domin nusar da al’ummarsu da su
tashi su yi sana’a komai kankantarta wato ko da karamin jari. Misalan irin wa
ɗ
annan Karin Magana su ne kamar haka:
Manganci:
Mazuma
ciro fandiyan karga
(Mai nema yana tare da samu)
Hausa:
Mai nema yana tare da samu.
Jigon wannan Karin magana shi ne, yayin da
mutum ya ha
ɗ
a nema da ha
ƙ
uri da juriya, zai iya kai wa
ga samun abin da yake bukata. Al’ummar Mangawa da Hausawa duk suna amfani da
wannan Karin magana wajen karfafa al’ummarsu, wajen su tashi su nemi na kansu
kuma su jure wahalar nema, koda kuwa yau sun rasa, to wata rana za su samu,
domin mai nema yana tare da samu.
Manganci:
Kawu
banaye sai kiji
(In kwanaki suka yi albarka sai da
ɗ
i)
Hausa:
Bayan wuya sai da
ɗ
i.
Wannan karin maganar Hausawa da Mangawa kuma
yana nuni ne da, idan mutum ya yi ha
ƙ
uri da wata wahala, akwai lokacin da zai zo, wannan
wuya da wahalar su zama tarihi. Domin da
ɗ
i
ba ya samuwa sai an sha wuya an nemo shi. Saboda haka, juriya a kan wuya kan sa
a sami sakamako mai kyau har a ji da
ɗ
i.
Manganci:
Kam kumine curuyyako kurnin kalassai curia (
Idan mutum yana ganin farinka ba zai ga ba
ƙ
inka
ba
)
Hausa:
Mai rabon ganin ba
ɗ
i ko ana dakawa a turmi sai ya gani.
Jigon wannan Karin magana kuma shi ne, mutum ya
nuna jajircewa a kan abu komai wuyarsa ba tare da tsoro ba. Irin wannan karin
magana yana
ƙ
ara
ƙ
arfafa zuciyar mutum wajen ganin ya nuna
jarumta da dagewa domin kai wa ga biyan bukata. Al’ummar Hausawa da Mangawa
suna amfani da wannan karin magana domin nusar da al’ummarsu a kan kada su zama
masu fitar da tsammanin samun duk wani abu da suka sanya gaba wajen nema.
Manganci:
Gana
ginaye biri kam cimbe bumi
(Da ka
ɗ
a-ka
ɗ
an ake tsotsar tuwo har a cinye)
Hausa:
Da sannu-sannu akan ci tuwon
mai rowa.
Kafin mutum ya kai ga biyan bu
ƙ
ata
dole ne ya bi sannu a hankali, ba tare da garaje ko kankamba ba. Hausawa da
Mangawa suna amfani da wannan karin magana yayin jan hankalin al’ummar su, a
kan ha
ƙ
uri
wajen neman wani abu musammana ga mai karamin jari na sana’a.
Manganci:
Gina
ginaye fulaza kuloro kargayen
(Da ka
ɗ
an-ka
ɗ
an Bafullace yake shige gonarsa)
Hausa:
A hankali filfilo kan shiga
daji.
Filfilo wani
ƙ
awaro
ne da wasu ke kira da Malam-bu
ɗ
e-littafi.
Yakan tashi daga kan wannan fure ya koma kan wancan fure. Sannan kuma akwai
wani abin wasan yara da sukan
ɗ
aura
masa zare ya yi ta tashi sama a hankali, wasu na kiran
sa da suna jirgin leda. A wannan karin magana
an yi amfani da wannan kalma domin nuna juriya, ta yadda za a samu cewa juriya
na da matakai daban-daban idan mutum ya jure wani mataki, zai iya
ƙ
ara
shiga wani mataki na gaba.
W
ato
ba dare
ɗ
aya ake yin arziki ba.
Manganci:
Kakanum
sa cidina
(Kakarka
ta y
i sa’a
)
Hausa:
Kakarsa ta yanke saka.
Wannan karin magana ne da ke nuna hoton rayuwar
al’ummar Mangawa da Hausawa ta fuskar irin sana’oin da suke yi. Haka kuma a
lokaci guda ana
ƙ
o
ƙ
arin fahimtar da al’umma cewa
Mangawa da Hausawa, mutane ne da ke da
ƙ
o
ƙ
arin yin sana’a. Domin kuwa daga cikin
sana’oinsu akwai sana’ar sa
ƙ
a. Ana amfani da wannan karin magana ne domin
nuna cewa mutum ya taki sa’a, ko ya huta, ko kuma Allah ya yi masa Alam-nashara
a rayuwarsa.
Manganci:
Hambara
hambarama naftu buwoma koyina (
Mai
buge-bu
ge ya
fi
mai
zaman banza)
Hausa:
Sana’a goma maganin takaici.
Wannan karin magana yana magana ne a kan raba
hannu a sana’a saboda wata rana. Wannan ma yana nuna cewa Mangawa da Hausawa
mutane ne masu yin sana’a da yawa. Wato idan wannan ta ki, sai a koma waccan.
Ana amfani da karin maganar domin fa
ɗ
akar
da mutane cewa, kada su dogara da sana’a
ɗ
aya.
Wato dai gida biyu maganin gobara in ji masu iya maganar Hausa.
Manganci:
Bare
firuzu garrasan dibinin badinimmi
(Kada a cire zare ba
a yada allura ba)
Hausa:
Kar ka koyi sa
ƙ
a
da mugun zare.
Kamar karin maganar da ta gabace ta, wannan
karin magana ne dake nuna muhimmancin mayar da hankali wajen koyon sana’a
saboda gudun ha’inci. Haka kuma karin maganar na kara nuna cewa al’ummar
Mangawa da Hausawa mutane ne da ke koyar da al’ummarsu sana’a, kuma daga cikin
sana’o’in da suke yi har da sa
ƙ
a, wadda take tsohuwar sana’a ce mai da
ɗ
a
ɗɗ
en
tarihi. Kuma suna amfani da wannan ne domin fa
ɗ
akar
da mutane cewa su kauce wa ha’inci a rayuwarsu.
Manganci:
Kannu
kahalal din timajiya firur zumme badiji
Hausa:
Ana zaton wuta a ma
ƙ
era.
Ana gane hoton rayuwar al’umma ta la’akari da
karin maganganunsu. Domin haka wannan karin magana ya fito da hoton rayuwar
Hausawa ta fuskar sana’oinsu na gargajiya. Karin magana ne da ke
ƙ
ara
jaddada cewa, ma
ƙ
era wuri ne da ake amfani da wuta fiye da
sauran wuraren da ake aiwatar da wasu sana’o’i na gargajiya. Al’ummar Mangawa
da Hausawa suna amfani da wannan karin magana ne lokacin da wani abu ya faru a
inda ba a tsammanin faruwarsa. Wato wuta da ake tsammaninta a ma
ƙ
era
sai kuma aka samu ta tashi a masaka. In da ake zaton abu sai a ji shi a inda ba
a ta
ɓ
a zatonsa.
Manganci:
Ciniyi
kattuye jirema rumbomaro
(Cinikin gaskiya maganin cinikin
ƙ
arya)
Hausa:
Cinikin
ƙ
arya,
gaskiya ke biyansa.
Wannan karin magana ne da yake nuna ha
ɗ
arin da ke tattare da cinikin duhu, saboda
ciniki ne na
ƙ
arya, amma gaskiya ce ke biyan irin wannan
cinikin. Karin maganar yana
ƙ
ara nuna cewa Mangawa da Hausawa mutane ne da
suke harkokin ciniki a rayuwarsu. Domin haka, suna amfani da karin maganar
wajen koya wa jama’a ladabi a harkar cikini, wato saboda mutane su kauce wa
cinikin duhu, wanda tamkar caca ne.
4.1 Kammalawa
Wannan takarda kamar yadda aka gani, an bayyana
cewa, Karin magana wani jigo ne da ake amfani da shi wajen ba wa al’umma
tarbiyya tun suna
ƙ
anana, musamman al’ummar Mangawa da Hausawa.
Yayin da aka tattaro wasu daga cikin irin samfurin karin maganar Manganci da
Hausa, wa
ɗ
anda suke da kamanceceniya da
juna ta fuskar jigo. Sannan kuma aka bayyana ma’anonin wasu daga cikin karin
maganar da aka nazarta ta hanyar fito da sa
ƙ
onnin
da ke
ƙ
unshe ciki. Saboda haka amfani da karin magana
a wajen al’ummu ba wani ba
ƙ
o ko sabon abu ba ne, musamman wajen horo ga
aikata alheri, ko hani ga barin aikata wani mummunan al’amari. Haka kuma sa
ƙ
on
da ke
ƙ
unshe cikin Karin magana, tamkar gya
ɗ
a ce sai an fasa akan san mai
ƙ
waya.
Domin haka yana da kyau a ci gaba da nazartar irin wa
ɗ
annan karin maganganu na al’ummu mabanbanta
juna, domin gano irin kamanci da ba
m
banci
da ke tsakaninsu ta fuskar harshe da jigogin azancin maganganunsu. Daga
ƙ
arshe
kuma, akwai kare-karen maganganu masu tarin yawa, wa
ɗ
anda suke da kamanceceniya da juna ta fuskar
jigo a harshen Manganci da kuma Hausa, wa
ɗ
anda
wannan takarda ta yi ka
ɗ
an wajen bayyana su. Wasu
daga ciki sun ha
ɗ
a da:
Manganci:
Kam
burzu rawama yimlaga dibi cibi
(Mai neman arha wata
rana zai sayi munmuna)
Hausa:
Arha maganin mai wayo.
Manganci:
Wuri
mazu kambuye ciniyi sameye (
Mai
neman ku
ɗ
i wata rana zai tashi sama
)
Hausa:
Neman ku
ɗ
i, makahon ciniki.
Manganci:
Ciniyi
darajan dimiye kilaninbe daraja
(Ciniki da
daraja-darajar mutum ne)
Hausa:
Cinikin mutum mutuncinsa
Manganci:
Awo gila yibumiya tima riba kilaye (
Siyan nagari mai
da
kudi
gida
)
Hausa:
Sayan nagari, mayar da ku
ɗ
i gida.
Manganci:
Mai
wuriba wowa inda wayanju (
Sarkin
da ba shi da ku
ɗ
i ba komai ba ne
)
Hausa:
Ina wayo, sarki ba ku
ɗ
i.
Manganci:
Allah
niya mai ba wo (
In
banda Allah
ba
wani Sarki
)
Hausa:
Babu Sarki sai Allah
Manganci:
Kam
mukon zu meyina tima soba maiyaye (
Y
aro da kudi abokin manya)
Hausa:
Mai ku
ɗ
i aminin Sarki.
Manganci:
Zori
taza gambi talayen kuyina
(Mahaukacin mai ku
ɗ
i ya fi talaka)
Hausa:
Ri
ƙ
on
mahaukaci sai sarki.
Manganci:
Kammunin burwoyi tima Mai kamuwanunbewo
(Matarka ta farko
ita ce shugabar matanka)
Hausa:
Uwargida sarautar mata.
Manganci:
Sim
Mai cironamazi kamzu gade rizibawa
(Wanda ya ki abokin
Sarki ya ki Sarki)
Hausa:
Idon da ya ga sarki, ba ya
tsoron galadima.
Manganci:
Ganga
maiyaye sai mai (
Ki
ɗ
an S
arki
sai Sarki
)
Hausa:
Sarki goma, zamani goma.
Manganci:
Mai
maiwu zaman maiwu
(Sarki goma zamani goma)
Hausa:
Idan ka
ji tambari, sai sarki.
Manganci:
Talaga
mairiro dazan lejiya tini mai rozuwa burwon
Hausa:
Rigaya zuwa fada ba shi ne
samun sarki ba.
Manganci:
Giri
ka ra’an tazanjuwa bikkerai
Hausa:
Barewa a daji da ‘ya’yanta
suke wasa.
Manganci:
Kawunun
hugujiya kare gubu runumi
(Duk wanda bai raina ka
ɗ
an ba, ba zai raina da yawa ba)
Hausa:
Inda ranka ka sha kallo.
Manganci:
Cilim
ma sammi kumara
(D
uk baki cinnaka ne)
Hausa: In da da ɗ i ma da kunya, abincin gidan surukai.
Manazarta
Amin, M. L. (2004). Re-Interpreting Hausa Pro
ɓ
erbs on Duniya”
Harshe 2, Department of Nigeria and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello Uni
ɓ
ersity.
Bargery,
G. P. (1993) A Hausa-English Dictioanary
and English Hausa Vocabulary (2nd ed.) Zaria: Ahmadu Bello Uni
ɓ
ersity Press Ltd.
Bugaje, H. M. (2016) Hakuri da Juriya a Mahangar Bahaushe: Tsokaci
Daga Karin Magana. Takarda da aka gabatar a taron kara wa juna sani, ranar
9-12ga watan Oktoba 2016. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (2006) Gadon Fe ɗ e Al’ada Lagos : Tiwel Nigerian Limited.
CNHN, (2006) Ƙ amusun Hausa: Kano; Jami’ar Bayero.
Ginsau, A. (2018) Nazarin Jirwayen Wasu Kayayyakin Sana’o’i A Karin M aganar Hausa: Kundin Digiri Na Biyu; Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
Haruna, M. (2017) Taskar Karin Magana. Kano: Benchmarks
Publishers.
Hassan, M. B (1981) “Karin Magana da Salon Maganar Hausawa”,
Nazari a kan Harshe, da Adabi, da Al’adu. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Hassan, S. (2009) “Nazarin Karin Magana da Suke Nuna
Rarrashi” Harshe 3. Department of Nigeria and African Languages, Ahmadu Bello
Uni
ɓ
ersity Zaria.
Junaidu, I. da Yar’aduwa, T.M (2007) Harshe da Adabin Hausa A
Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited.
Kirk – Greene, A.H. (1966). Hausa ba Dabo ba ne. Ibadan:
Uni
ɓ
ersity Press Ltd.
Koko, H. S. (1989). “Karin Magana a Hannun Mata a Garin Sakkwato.”
Kundin digiri na farko, Jami’ar Usman
Ɗ
anfodiyo,
Sakkwato.
NNPC (1958) Karin Magana. Zaria: Northern Nigerian
Publishing Company
Skinner, N. (1980), Anthropology of Hausa Language; Zaria. Northern
Nigeriya Company.
Umar, M.B. (1980) Dangantakar Adabi Da Al’adun Gargajiya.
Zaria: Hausa Publication Center Mangwaro Babajo.
Ɗ
angambo, A. (1982) Rabe-Raben
Ad
abin Hausa Da Muhimmancinsa
Ga Rayuwar Bahaushe:
Zaria:
Gaskiya Corporation Ltd.
Ɗ
angambo, A. (1984) Rabe-raben
Adabin Hausa da Mahimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishers
Ltd.
Ɗ
angambo, A. (2008) Rabe – Raben
Adabin Hausa. Zaria: Amana Publishers Ltd.
Ɗ
anhausa, A.M. (2012). Hausa mai
Dubun Hikima.Kano: Century Researchand Publishing Company Ltd.
Zarruk, R. M. (1990) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan makarantun Sakandire.Ibadan: Uni v ersity Press Ltd.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.