Ticker

6/recent/ticker-posts

Kimiyyar Magungunan Ciwon Daji a Mahangar Hausawa

Citation: Abdulrahaman, M.A. & Gulbi, A.S. (2024). Kimiyyar Magungunan Ciwon Daji a Mahangar Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 341-348. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.039.

Kimiyyar Magungunan Ciwon Daji a Mahangar Hausawa

Musa Alhaji Abdulrahaman PhD
Sashen Nazarin Yarukan Afrika Da Kimiyyar Harshe
Jimi’ar Jahar Yobe, Damaturu
abdulrahamanmusa1661@gmail.com
08036719021/ 08027277904

Da

Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi
Depertment of Nigerian Languages
Usmanu Ɗ anfodiyo University, Sokoto
08089949294

Tsakure

Magani musamman na Gargajiya a wajeen Bahaushe na da matu ƙ ar matsayi da muhimmanci ga rayuwar al’ummar ƙ asar Hausa, an san Bahaushe mutum ne mai matu ƙ ar ri ƙ o da al’adunsa wanda ya gada tun iyaye da kakanni, barantana kan abin da ya shafi harkar magani. Ma ƙ asudin wannan nazari shi ne fito da Magungunan ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don kawo sau ƙ i da waraka a rayuwar su ta yau da kullum, sani ko fahimtar magani ya na taimakawa wajen shawo kan ciwo ko cuta da wuri kafin ta azzara a jikin majinyaci, nazarin zai yi bayani kan wasu Magungunan ciwon daji. Manufar wannan bincike kuwa shi ne ƙ o ƙ arin fito ko tantance Magungunan Ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don warkarwa, wa ɗ annan magunguna ga su nan a fili ko sarari don a ƙ ara sanin su, ba don komi ba sai don ƙ ara inganta rayuwa da lafiyar Hausawa ko majinyata, musamman masu fama da ire-iren Ciwon ko cututtukan daji da suke addabar al’umma. An yi amfani ta hanyar hira, wato tattaunawa da masana magunguna da masu bayar da magani da sauran mutane a wasu ɓ angarorin ƙ asar Hausa da kewayanta don fito da wa ɗ annan Magungunan ciwon daji. 

1.0 Gabatarwa

Sanin alamar ciwo na da matu ƙ ar muhimmanci ko amfani don gano matsala da ɗ aukan mataki tun daga farko, wannan ma ƙ ala ce da take magana kan alamomin wasu cututtukan daji da raga-kafin kamuwa da su. Sanin asalin cuta na nufin, farkon abu ko usuli ko asali ko dalili, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 314). A Bahaushiyar al’ada in ana so a fahimci asali ko mafarin cuta, sai an nutsa cikin abubuwa kamar: iskoki, adabi, camfi, tsafi, gado, hatsari da yanani, lalube cikin wa ɗ annan abubuwa da ka zayyana a sama za su taimaka matu ƙ a wajen binciko mafarin cuta a Bahaushiyar al’ada, da farko ya kamata mu san mene ne; Iskoki da adabi da camfi da tsafi da gado da hatsari da yanani? Raga-kafi ya fi magani, a yi riga-kafi kafin abkuwar cuta da gane alamun cuta na taimaka wa al’umma a fagen kiwon lafiyarsu.

Iskoki a wajen Bahaushe wasu halittu ne masu kama da mutane ta fuskar halittarsu, da surarsu, da ayyukansu, da al’adunsu, da ɗ abi’unsu, da harshensu, da siyasar rayuwarsu, da dai makamantansu. “Bahaushe ya yi imani da samuwar su a kowane tudu da rahi na bangon duniya, wurare da ake samun ‘yan Adam, da wuraren da ba a samun su. A wajen ‘yan bori da matsafa ana iya amfani da Isaka wajen neman wani amfani, da tunku ɗ e wata cuta ga rayuwa, ko aukar da wata cuta ga wani, ko wasu, ko wani wuri”, (Bunza, 2006: 1). 

Camfi, yarda da cewa abu zai auku ta hanyar jahilci, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 71) Ma’anar camfi da al’ada makusanta ne ƙ warai irin na jini da tsoka. Camfi wata da ɗ a ɗɗ iyar ala’da ce da Hausawa suka tarar kaka da kakani. Masana da manazarta Hausa sukan yi wa camfi kallo biyu, wasu na ganin camfi al’ada ce kawai kamar irin/kowace al’ada; a ganin wasu kuwa, abin ya wuce haka, ya kai matsayin addini daga cikin addinan gargajiyar Bahaushe, (Bunza, 2006: 58) camfin gargajiya da ba ya da sofane kowace irin al’ada a cikinsa face al’adar Bahaushe da ya gada kaka da kakani. Ire-iren wa ɗ annan camfe-camfe za a tarar suna bayyana tantagaryar abubuwan da ke aukuwa a ƙ asar Hausa tun gabanin saduwarta da kowane irin saukakken addini, (Bunza, 2006: 64). 

Tsafi na nufin bin wasu hanyoyi musamman yi wa Iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata bu ƙ ata, ko samun wani amfani, ko tunku ɗ e wata cuta, (Bunza, 2006: 35). Tsafi, a magani aka fi samun sa, amma kuma akwai tsafin da ake yi don a cutar da wani, ko don yin kashi a gona. Daga cikin irin wannan tsafin cutarwa akwai ‘sammu’ da ‘Uwar Gona’, (Gobir, 2013: 829). Tsafi hanyar ba da gaskiya da wani abu daban ba Allah ba, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 449).

2.0 Matsayin Maganin Gargajiya ga Bahaushe

Magungunan gargajiya na da matu ƙ ar matsayi da muhimmanci ga al’ummar Hausawa a jiya balantana yau, an san Bahaushe mutum ne mai matu ƙ ar ri ƙ o da al’adunsa balantana kan abin da ya shafi harkar cuta da magani.

Maganin gargajiya na Hausawa yana da babban matsayi a al’dar Hausawa domin kuwa shi ne maganin da Hausawa suka gada iyaye da kakanni. Kafin shigowar Turawa ƙ asar Hausa da ma bayan shigowarsu ana amfani da ‘ya’yan itatuwa da sassa ƙ e-sassa ƙ e da sauyoyi da ganyayen itatuwa da tsirrai da hakukuwa iri daban-daban domin magance cututtukan da kan matsa wa mazauna wannan ƙ asa ko a ce Hausawa, Abdulrahaman, (2023). Haka kuma ana amfani da wasu abubuwa wa ɗ anda suka ha ɗ a da sassan jikin dabbobi da ƙ wari da tsuntsaye a wasu lokuta har da sassan jikin mutane domin ha ɗ a magungunan da suka danganci tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce, Sallau B. (2010).

Ya ci gaba da cewa, “saboda yarda da Hausawa suka yi da ire-iren wa ɗ annan itatuwa da tsirrai wajen warkar da cututtuka ya sa, ko da Turawa suka kawo maganin zamani ba su daina yin amfani da magungunan gargajiya ba. Hasali ma, akwai wa ɗ anda ba sa amfani da maganin asibiti, don kuwa zuciyarsu ba su ba ta aminta da ire-iren wa ɗ annan magunguna ba” Sallau, (2010). 

Ta fuskar addinin Musulunci, maganin gargajiya yana da matu ƙ ar amfani, don kuwa Annabi Muhammadu (SAW) tsira da amincin Allah su ƙ ara tabbata a gare shi, ya yi horo ga Musulmi da su ri ƙ a amfani da ‘ya’yan itatuwa ko ganyayensu ko sa ƙ e-sa ƙ ensu da tsirrai da hakukuwa domin akwai magani a cikinsu. A wani hadisinsa yana cewa:

“Ina horon ku da wannan itaciya ta Hindu domin a cikinta akwai warkarwa bakwai”

An bayyana itaciyar Hindu tana kama da Giginya. “Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ƙ ara bayyana cewa, haramun ne ga Musulmi, ya yi amfani da najasa ko ya yi wani surkulle wajen yin maganin kowace irin cuta”, (Sallau, 2010: 13).

3.0 Kimiyyar Magungunan Ciwon Daji

Abin da Bahaushe yake kira da ciwon daji ko sabara ko maharbi ko mata ɓ i, wata halitta ce daga cikin Aljanu wanda a cikin Aljanun ma Maharba ne, ma’ana Baushe wannan Baushen a ko da yaushe ba ya rabuwa da iyalinsa, wato matarsa haka suke tare dukkansu maharba ne, shi maharbi ne ita ma maharbiya ce don haka kuma tare suke farautarsu, ba ya iya tafiya ba tare da ita ba hakan ya sa, matar ko mijin dukkansu ba wanda in ta kama ba ya harbin Ɗ an Adam, wato mutum, har dabbobi suna harbi, mutane suna fassara wannan Aljani da cewa wani ɗ an Aljani ne gajere da kullum yana sanye da kayan sa ƙ i da hularsa irin ta maharba. [1] Sabara sunan aljana matar Gajere wato Jeji ko Daji, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 379). Ɗ aya daga cikinsu in har aka musu wani abu da ba sa so musamman da daddare ko ta ɓ a wani abu mai ƙ ara ko ya dame su, mijin ko matar kan harbi mutum a kowane irin ɓ angaren jikin ɗ an Adam, harbin yana kasancewa wani lokaci kamar an soki mutum, mutum zai ji a jikinsa, (Hira da Abu Ubaida Sani). Bahausawa kawai ba akwai ƙ abilu da dama da suke danganta ciwon daji da Iskoki ko Aljanu, kuma su yi magungunansu na gargajiya su dace [2] Daji, Sabara, Mata ɓ i wannan duk na daga cikin sunayen da Bahaushe ke ƙ iran ciwon daji da shi. A nan bayanai ne da za a gabatar kan magungunan ciwon daji da kuma kimiyyar amfani da su don magance ciwon daji, Allah da kansa yake cewa ba wata cuta face shi ya sau ƙ ar da ita kuma bai sau ƙ ar da ita ba face sai da ya sau ƙ ar da maganin ta. Ibn Ƙ ayyim, (1999: 24). Magungunan da kimiyyar su sun ha ɗ a da:

3.1 Hantar Ra ƙ umi

Ra ƙ umi wata irin dabbar gida mai dogon wuya da dogwayen ƙ afafu da kuma tozo, Ƙ amusun Hausa, (2006: 365). Hanta wata irin tsoka nama maimlaushi mai launin ba ƙ i da surkin ja wadda ake samu a cikin-cikin tsuntsu ko dabba ko mutum, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 195). Yadda ake amfani da hantar ra ƙ umi a matsayin maganin ciwon daji, a samu hantar ra ƙ umi za a iya gasa ta ko soya ta ko dafa ta ake ci sau biyu (2) a rana har tsawan sati (2) za a samu lafiya da yaddar Allah. (Nura, 2017: 12).

3.2 Fitsarin Ra ƙ umi

Yadda ake amfani da fitsarin ra ƙ umi a matsayin maganin ciwon daji, fitsarin ra ƙ umi cikin babban cokali ɗ aya (1) a ha ɗ a da manyan cokali shida (6) na nonan ra ƙ umi, ya zama cokula bakwai (7) za a sha cokali bakwai (7), tsawan sati hu ɗ u (4), cokali bakwai-bakwai ke nan. A rana ta biyar (5), za a sha cokali bakwai (7) sau biya (2), wato safe cokali bakwai (7) da yamma cokali bakwai (7). A rana ta shida (6) za a sha cokali bakwai (7) da safe, cokali (7) da rana, cokali bakwai (7) da daddare cokali bakwai, wato sau uku kenan a rana. Haka kuma a rana ta bakwai (7) cokali bakawi (7) da safe, cokali bakwai (7) da rana, cokali bakwai (7) da yamma cokali bakwai (7) cokali bakwai (7) da daddare. Kwana bakwai sati ɗ aya ke/ nan. Ana so a maimaita wannan tsarin har tsawan sati ukun (3) da ya rage. (Nura, 2017: 15-17).

3.3 Lemon Tsami 

Wata irin itaciya mai ƙ aya wadda wani nau’inta yana da ‘ya’ya masu tsami wani kuma za ƙ i, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 305). Amma mai tsamin. A Samu Lemon Tsami ƙ waya uku (3) da ruwa kamar lita (Litre) ɗ aya (1) a yanka Lemon Tsamin har ɓ awonsa a zuba a ruwan a dafa hi ya dafu sosai sai ake sha sau uku (3) kullum na tsawon sati biyu (2) da yardar Allah za a dace, ya danganci da ɗ ewar ciwon da kuma sau ƙ in da ake gani [3]

3.4 Ganyen Magarya

‘Magarya’ Wata bishiya mai ƙ aya da ƙ ananan ‘ya’ya jajaye masu kama da na kurna, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 316). Ganye tohon da ke fitowa a jikin reshen bishiya, yakan zama mai fa ɗ i ko siriri, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 157). A samu ganyen magarya a shanya shi a inuwa ya bushe a daka shi ya daku sosai, sai a dafa shi ya tafasa sai ake sha kamar shayi in da sarari ko hali a samo zuma mai kyau mara algus sai ake ha ɗ awa ana sha sau uku (3) kullum, in kuma ya yi gyambo sai a samo ma’ulkal, wani ruwa ne mai hasken gaske da ake amfani shi kan abubuwa da dama, ake wanke wuri da shi kullum sai ake zuba dakakken garin Ganyen Magarya a gurin har zawon sati biyu (2) ko fiye da hakan, ya danganci da ɗ ewar ciwon da kuma sau ƙ in da ake gani [4]

3.5 Ciwon Daji da ake Amfani da Kanwa a Matsayin Maha ɗ in Magani 

Kanwa wani ma’adini tattaura da ake ha ƙ owa a ƙ asa mai ɗ aci- ɗ acin ɗ an ɗ ano da ake magani da shi wajen Ciwon ciki, akwai fara da kuma ja. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 232). 

3.6 Kurna 

Kurna wata bishiya mai ƙ ananan ganye da ƙ aya, takan yi ‘ya’ya ƙ anana da ake ci. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 256). A samu sassa ƙ en kurna in ya bushe sai a ha ɗ a shi da kanwa ake wanke ciwon kuma ake barba ɗ awa a kan Ciwon. 

3.7 Gunji/Gumza

Rurin kuka. Wata irin ƙ atuwar bishiya da ake samun tan ƙ o a jikinta. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 175).A samu saiwar gunji a ha ɗ a da jar kanwa sai a dafa kulum a sha a yi wanka, zai yi magani. 

3.8 Hankufa 

Wani tsiro mai kama da tafasa da ake magani da saiwarsa. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 2194). A samu saiwar ciyawar hankufa a ha ɗ a da jar kanwa a dafa a ri ƙ a sha ana yin wanka da shi.

3.9 Barbaje 

A samu saiwar barbaje a ha ɗ a da jar kanwa a dafa a ri ƙ a sha sau uku a rana safe, rana da dare, za a samu sau ƙ i da yaddar Allah. 

3.10 Ararra ɓ

Ararra ɓ i wata irin bishiya mai ganyaye kamar yatsu. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 18). In aka samu sassa ƙ en ararra ɓ i a ha ɗ a da jar kanwa a ji ƙ a ake sha. 

3.11 Danya 

Wata irin bishiya da ganyenta ya yi kama da na dalbejiya, tana kuma da ‘ya’ya masu tsami-tsami. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 97). A samu sassa ƙ en danya a ha ɗ a da jar kanwa a dafa ake sha a yi wanka, kuma ake zuba maganin a kan ciwon zai warke, (Hira da Malam Abdullahi Haruna Imam, 12th/3/2021). 

3.12 Marke 

Marke wani itace ne mai ƙ wari da ake sassa ƙ a turmi da shi. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 334). A samu sassa ƙ en marke a ha ɗ a da kanwa a dafa ake sha ana yin wanka da ruwan, a dingi yin haka har sai an ga sau ƙ i ya fara samuwa.

3.13 Taura 

Wata irin bishiya mai ‘ya’ya kamar na gawasa. Ƙ amusun Hausa, (2006: 433).A samu sassa ƙ en taura a ha ɗ a da kanwa da runhu a dafa a yi wanka a sha. 

3.14 Gabaruwa 

Wata irin bishya wadda ake jima da rini da ‘ya’yanta. Wata irin ƙ atuwar bishiya da ake samun tan ƙ o a jikinta. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 147). A samu sassa ƙ en gabaruwa a ha ɗ a da kanwa sai a ri ƙ a sha ana shafawa safe da yamma. 

3.15 Gamji 

Wata irin ƙ atuwar bishiya da ake samun tan ƙ o a jikinta. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 153). A samu sassa ƙ en gamji a ha ɗ a da kanwa a daka a wanke Ciwon a zuba garin a kan Ciwon kullum da safe, yana maganin Ciwon daji [5]

3.16 Ganyen Gwanda 

Ganye gwanda tohon da ke fitowa a jikin reshen bishiya, yakan zama mai fa ɗ i ko siriri, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 157). Gwanda wata irin bishiya doguwa mai ganya kamar na zurman, tana yin ‘ya’yan da suka yi kusan girman Kabewa, masu za ƙ i da ake sha, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 182). A samu ganyen gwanda in mai fa ɗ i ne a samu lita ruwa shida (6) in ba mai fa ɗ i ba ne a samu litar ruwa hu ɗ u (4) a dafa da wuta sama-sama kar a raraka masa wuta in an dafa sai a bar shi ya kwana, za a sha sau uku (3) kullum safe, rana, da dare kofi ɗ aya (1) kowane lokaci, tsawan wata uku (3) da izinin Allah kowane irin Ciwon daji ne za a samu waraka, (Malam Gwani Bauchi).

3.17 Albasa Da Zuma

Albasa wani irin tsiro mai yaji dangin mabun ƙ asa ƙ asa da ake miya da shi, ko lawashinsa, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 11). Zuma Wani ƙ waro dangin ƙ uda sai dai ya fi ƙ uda girma, launin jikinsa fatsi-fatsi; yana fitar da wani ruwa mai za ƙ in gaske da ake sha, kuma yana da ƙ ari da yake harbi da shi, za ƙ i da wannan ƙ uda ke samarwa, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 496). Amma za ƙ in da wannan ƙ uda yake samarwa ake nufi a nan. A samu ruwan albasa wato a matse albasa a tatso ruwanta cokali uku (3) da ruwan zuma cokali biyu (2) a ha ɗ a a cikin kofin ruwa ɗ aya (1) madaidaici a sha sau biyu (2) a rana tsawan kwana sha ɗ aya (11) yana magance ciwon dajin ido, da yardar Allah. [6]

3.18 Leman Tsami da Albasa Da Zuma

Wata irin itaciya mai ƙ aya wandda wani nau’inta yana da ‘ya’ya masu tsami wani kuma za ƙ i, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 305). Amma za ƙ in da wannan ƙ uda yake samarwa ake nufi a nan. Ruwan lemon tsami cokali uku (3) da ruwan albasa cokali uku (3) da zuma cokali ɗ aya (1) a sha da safe a sha da yamma, tsawan kwana sha hu ɗ u (14) wato sati biyu (2) yana magance ciwon daji na cikin huhu da yardar Allah. [7]

3.19 Tafarnuwa

Tafarnuwa wata aba ƙ arama dangin mabun ƙ asa- ƙ asa mai kama da albasa mai wari, wadda ake sawa a abinci ko a ha ɗ iya don maganin sanyi, musamman mura, Larabawa suna amfani da ita a wajen toye-toye kamar yadda ake yi da albasa, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 41). Shan garin tafarnuwa a shayi ba madara sau ɗ aya (1) a rana na tsawan kwana sha hu ɗ u (14) wato sati biyu (2), yana magance ciwon daji na cikin ha ƙ ori. [8]

3.20 Kabeji da Tumatur 

Tumatur wani tsiro mai ganye kamar karkashi da ‘ya’ya masu yin ja wa ɗ anda ake ha ɗ awa da tattasai a malka ɗ a a yi miyar dage-dage, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 44). A matse ruwan kabeji da ruwan tumatur a cikin kofi ɗ aya (1) asha sau ɗ aya (1) a rana na tsawan kwana sha hu ɗ u (14) wato sati biyu (2) yana magance Ciwon daji na cikin jini, da yardar Allah [9]

3.21 Yazawa

Yazawa bishiya mai ‘ya’ya da ake sha kmua ake amfani da madarar da ake samu a ƙ wallonta tilon zane a fuska ko ajiki, wanda idan ya bushe sai wajen yay i ba ƙ i kamar an tsaga, ko Kashu, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 482). A samu kwallon yazawa mai kama da gya ɗ a ana ci ko a samu yazawa a matse ruwanta a ke sha sau biyu a rana yana magance Ciwon daji da yaddar Allah. (Hira da Dr. Abdulwahab Goni Bauchi)

3.22 Ganyen Goba

Ganye goba tohon da ke fitowa a jikin reshen bishiya, ya kan zama mai fa ɗ i ko siriri, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 157). A samu gyanyen goba guda shida a wanke a tafasa shi da ruwa lita (1) ɗ aya a kasa shi gida hu ɗ u (4) a sha sau uku (3) a rana, kuma idan ciwon daji ya yi ruwa ko ƙ urji sai ake ba ɗ a busheshshen dakakken gyanyen goba a gurin. (Hirar da aka yi Dr. Abdulwahab Goni Bauchi a gidan Radiyo Gwatal da ke Adamawa, 10/31/2019).

3.23 Ƙ odago da Man Shanu

Ƙ odago na nufin, kwallon giginya ko goruba, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 282). Amma a nan muna Magana ne kan kwallon goruba. A samo kwallon goruba a ƙ ona shi ya ƙ onu kamar gawayi sai a daka shi ya daku sosai sai a ha ɗ a shi da man shanu a caku ɗ a sai ake shafawa inda Ciwon Daji yake za a dace da yaddar Allah [10]

3.24 Matsattsagi 

Matsattsagi, wani itace ne mai ganye ƙ anana kore shar da ake samu yawanci a bakin kogi kuma ana ha ɗ a magani da shi. A samo ganyen matsattsagi ɗ anye sai a kir ɓ a shi ya kir ɓ u sai a ji ƙ a a ruwa in ya ji ƙ u sai ake shan ruwan kuma diddigar sai ake shawa inda Ciwon dajin yake, da yaddar Allah za a samu waraka [11]

3.25 Aduwa

A ɗ ebo ganyen aduwa a shanya shi a inuwa ya bushe, sai a daka shi ya daku, kuma a ɓ are ɓ awon kwallon aduwa in aka ɓ are ɓ awon shi ma a daka shi ya daku, sai shi kansa kwallon adauwar shi kuma sai a ƙ ona shi kenan an samu abubuwa guda (3) wato dakakken ganyen aduwa, dakakken ɓ awon aduwa da kuma ƙ onannan ƙ wallon aduwa, sai a ha ɗ a garin ganyen aduwa da garin ɓ awon aduwa yawansu ya zama daidai da juna sai a gaurayasu wuri ɗ aya su gaurayu sosai, shi kuma ƙ onannan kwallon aduwa sai a samo man zaitun a ha ɗ asu a gaurayesu wato a caku ɗ a su. Garin ganyen aduwa da garin ɓ awon aduwa sai ana zubawa cikin cokali babba a nono ana sha safe da yamma sau biyu a rana, a sha shi zawon sati biyu, ake amfani da kofi irin na masu shayi. Shi kuma ƙ onannan kwallon Aduwa aka kwa ɓ a da man zaitun in wurin da ciwon daji ya yi ƙ urji ko ciwo sai ake shafawa a wurin, shi ma za ake shafawa sau biyu a rana wato safe da yamma [12]

3.26 Garahuni

Garahuni, wani irin tsiro mai ya ɗ o ya hau danga; ana yin fate-fate da shi kuma yana maganin Ciwon ciki, Ƙ amusun Hausa, (2006: 157). A samu garahuni a shanya shi a inuwa ya bushe a daka shi ya yi laushi sosai, sai a sami nono a ɗ ebi garin garahuni ƙ aramin cokali guda ɗ aya (1) a zuba a nono a gaura ake sha sau biyu (2) a wuni, wato safe da yamma [13]

3.27 Dashi

Dashi wani irin tsiro mai ƙ aya- ƙ aya wanda ake yin mashiyin tozali da shi, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 99). A samu sassa ƙ en dashi da ganyansa a shanya su bushe sai a ha ɗ a su guri ɗ aya a daka su yi gari sosai sai ana sha cokali ɗ aya (1) sau uku (3) a rana ko wuni, in ciwon dajin nono ne sai ana barba ɗ a garin maganin a gurin [14]

3.28 Barbaji da Ɗ orawa

Ɗ orawa wata irin bishiya mai ganye kamar tsamiya wadda ake yin daddawa da ‘ya’yanta, a kuma yi gaskami da garin da aka yi daga ‘ya’yan. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 126). A samu barbaji da saiwarsa da sassa ƙ en ɗ aurawa sai a daka a sha da nono ko da kunu tsawon kwaina bakwai (7) wato sati ɗ aya safe da yamma, za a samu sau ƙ i da yaddar Allah [15]

3.29 Wurshi da Gishiri

Wurshi wani irin itace ne ko bishiya, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 474). Gishiri wani farin ma’adni wanda ake sakawa a abinci, kamar nama ko miya don ya ba da ɗ an ɗ ano mai da ɗ i. ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 168). Irin wannan itace ana amfani da shi wajen ha ɗ a magunguna da dama. A samu garin ganyen icen wurshi a ɗ ebo a bar shi ya bushe a inuwa sai a daka shi ya daku sai a ɗ ebi garin a hada da gishiri ake kurkure baki a shi yana maganin ciwon daji da ya shafi Ha ƙ ori da yaddar Allah [16]

3.30 Ganyen Sabara

A samo ganyen sabara a daka shi ya yi laushi sosai, a sha da nono ko kunu ko koko rabin cokali sau biyu a wuni ko rana, tsawon sati biyu (2) amma kar a sha sai an ci abinci [17]

3.31 Ganyen Goba 

A samo ganyen goba guda hu ɗ u ko biyar (4/5) ɗ anye sai a ɗ an jajjaga shi a tirmi ya jajjagu sosai, sai a tafasa shi ya tafasu a sha sau uku kullum na tsawon mako biyu ko kuma har sai an warke [18]

3.32 Ganyen Zaitun 

In an samu ganyen Zaitun za a daka shi a sha da shayi ba madara ko da ruwan zafi, na tsawon sati uku (3) sau biyu a rana (2) [19]

3.33 Ganyen Zogale 

Zogale, wata bishiya da ake shukawa ko dasawa a gida ko a gona, wadda ake tsirkar ganyenta ana dafawa ko a kwa ɗ anta a ci ko a yi dambu ko fate-fate ko a yi miya da shi, Ƙ amusun Hausa, (2006: 494). A daka ganyen zogale ake shafawa a gurin da ciwon Daji yake kuma a tabbatar ganyen bai ha ɗ u da wani ganye ba na daban, ake yin haka har sai an ga sau ƙ i ya samu [20]

3.34 Garin Hul ɓ a

Hul ɓ a, wa ɗ ansu irin ƙ wayoyi masu launin rawaya wari ɗ aya ko tsabarsu da aka fi samu a wurin ‘yan koli ko masu sai da kayan yaji, ko ‘yan masu ganye; ana magunguna da yawa da shi kuma ana ha ɗ a ta a cikin kayan shayi. A samu garin hul ɓ a a sha da madara ko da nono sau biyu a rana har sai an warke, sai kuma ake wanke inda ciwon Daji yake da ruwan Albasa, in kuma an so za a iya ha ɗ a garin Hul ɓ a da garin Habba [21]

3.35 Lalle da Man Shanu

Lalle, wani tsiromai tsaurin saiwoyi, da ƙ ananan ganye, wanda mata ke dakawa suna yin ƙ unshi da shi a ƙ afa da hannu don ado, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 300). A samu garin lalle mai kyau a kwa ɓ a shi da man shanu ake shafawa a jiki yana maganin ciwon daji da sauran ƙ uraje da suke damun jikin mutane da yaddar Allah [22]

3.36 Sassa ƙ en Itacen Runhu 

Runhu, wani irin tsiro dangin su sabara wanda mata kan yi wankan jego a shi, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 376-377). A nemo sassa ƙ en runhu ka dafa shi ya tafasu sosai, sai a samo zuma mai kyau a ha ɗ a da taashenshen sassa ƙ en runhu, ake shan ruwan sau uku (3) a rana. Za a ga abin mamaki game da magance ciwon daji [23]

3.37 Ma ɗ aci da Gumbi/ Ƙ aida-jini da Jar Kanwa

Ma ɗ aci, wata doguwar bishiya wadda itacenta ke da naci ainun ana yin magani da ganyenta da sassa ƙ enta, kuma ana yin katako da itacenta, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 313). Gumbi wani irin tsiro mai ƙ aya mai sassar ƙ ewa wuri guda, ( Ƙ amusun Hausa, 2006: 174). A samu sassa ƙ en ma ɗ aci da saiwar ba ƙ in gumbi/ ƙ aida-jini da jar kanwa ka ɗ an a tafasa a dama kunu a sha sau uku (3) a rana idan ciwon daji ya kumbura ake yiwa haka da yadda Allah za a samu waraka, za a a sha har tsawon sati biyu (2). Duk kumburin da ciwon daji ya haifar in sha Allah zai baje [24]

3.38 Gwanda 

Gwanda wata irin bishiya doguwa mai ganya kamar na zurman, tana yin ‘ya’yan da suka yi kusan girman Kabewa, masu za ƙ i da ake sha, ( Ƙ amusun Hausa, (2006: 182). A samu kwallon gwanda da ganyenta a shanya su bushe a dake su guri ɗ aya su da ku sosai ake sha a kunu ko a bura sau biyu (2) a wuni ko rana in sha ciown daji kowane iri ne zai warke da yaddar Alla, za a sha na tsawon wata guda wato sati hu ɗ u [25]

3.39 Aduwa

A samu ɓ awon aduwa da ganyen aduwa a shanya su bushe a daka su guri ɗ aya ake sha da nono sau biyu a rana, har sati hu ɗ u wato wata ɗ aya, cikin ikon Allah za a samu sau ƙ i, haka kuma dakakken ɓ awon aduwa da ganyenta za a kwa ɓ a da man zaitun ake shafawa a ciwon daji [26]

4.0 Kammalawa

Kimiyyar magungunan ciwon daji a mahangar al’adar Hausawa, kimiyyar ku a nan ita ce a ha ɗ a ice ko ganye da wani ice ko ganye don samar da Magani da kuma a sha sau kaza a wuni har tsawon wani lokaci, hakan duk na nuna kimiyyar gargajiyar Bahaushe. Magungunar gargajiya na da matu ƙ ar matsayi da muhimmanci ga rayuwar al’ummar Hausawa, Hausawa mutane ne masu matu ƙ ar ri ƙ o da al’adunsa wanda suka gada tun iyaye da kakanni, barantana kan abin da ya shafi harkar magungunansu. Wannan nazari ne da aka yi ƙ o ƙ arin fito da Magungunan ciwon daji a tunanin Hausawa, sani ko fahimtar magani ya na taimakawa wajen shawo kan ciwo ko cuta da wuri kafin ta azzara a jikin majinyaci, binciken ya yi bayani kan wasu Magungunan ciwon daji da Bahaushe yake amfani da su a fagen warkarwa. Wa ɗ annan magunguna ga su nan a fili ko sarari don a ƙ ara sanin su, ba don komai ba sai don ƙ ara inganta rayuwa da lafiyar Hausawa ko majinyata, musamman masu fama da ire-iren Ciwon ko cututtukan da suke da ala ƙ a da daji da suke addabar al’umma. An yi amfani ta hanyar hira, wato tattaunawa da masana magunguna da masu bayar da magani da sauran mutane a wasu ɓ angarorin ƙ asar Hausa don ha ƙ a ta cimma ruwa. 

Manazarta

Abdulrahaman, M, A (2023) Nazarin Kimiyyar Ciwon Daji Da Hanta Da Hawan Jini A Mahangar Al’adar Hausawa. Kundin Digiri Na Uku Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe, Ga ɗ a Jami’ar Jahar Bauchi 

Bunza, A.M. (2006). Gadon Fe ɗ e Al’ada . Lagos: Tiwal Nigeria LTD.

CNHN, (2006). Ƙ amusun Hausa . Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Gobir, A. Y. (2013). Cuta A Tunanin Hausawa: Waiwaye A Kan Cutar Iskoki. Kano: Studies In Hausa Languege, Literature and Culture, 1ST National Conference, Held at Mambayya House, Bayero University, Between 14th-16th January, 2013. 

Imam Ibn Ƙ ayyim, A. (1999) . Healing with the Medicine of the Prophet. Saudi Arabia: Darussalam Publishers And Distributors, Riyadh.

Nura, S. A. (2017). Ra ƙ umi Halittar Allah No. 530 Sani Mainaigge Sabon Titi, Gidan Ƙ an ƙ ara Gwale L.G.A Kano-Nigeria.

Sallau, B. A. (2010). Magani a Sha a yi Wanka a Buwaya. Kaduna: M.A. Njajiu Professional Malali Kaduna.



[1] Hira da Dr. Kabiru Usamatu Gwammaja Kana, 14/1/2022

[2] Hira da Dr. Ibrahim Muhammad Jawa Sabon Fegi Damaturu, 12/2/2022

[3] Hira da Dr. Nura Salihu Adam Babban Layi Kano 15/1/2022

[4] Hira da Malam Khalidu Abubakar Jibril, 12/4/2022

[5] Hira da Malam Abdullahi Haruna Imam, 12/2/2021

[6] Hira da Dr. Nura Salihu Adam, 14/01/2022

[7] Hira da Dr. Nura Salihu Adam, 14/01/2022

[8] Hira da Dr. Nura Salihu Adam, 14/01/2022

[9] Hira da Dr. Nura Salihu Adam, 14/01/2022

[10] Hira da Malam Hassan Musa, 23/9/2021

[11] Hira da Dawa Mai Magani, 7/12/2021

[12] Hira da Malam Musa Muhammad Gyara Kayanka Arigungu, (27/9/2021)

[13] Hira da Siba Abubakar Mai Magani a Garin Gashua, (6/11/2021)

[14] Hira da Siba Abubakar Mai Magani a Garin Gashua, (6/11/2021)

[15] Hira da Malam Yahaya Kore Damagum, (12/12/2019)

[16] Hira Malam Isiyaku Nuhu Wudil mai maganin Gargajiya, 25/11/2021

[17] Hira da Ibrahim Maijalalaini Ƙ ofar Ruwa Kano, 14/01/2022

[18] Hira da Ibrahim Maijalalaini Ƙ ofar Ruwa Kano, 14/01/2022

[19] Hira da Ibrahim Maijalalaini Ƙ ofar Ruwa Kano, 14/01/2022

[20] Hira da Ibrahim Maijalalaini Ƙ ofar Ruwa Kano, 14/01/2022

[21] Hira da Dr. Abdulrazak Abubakar Ɗ anfodio Islamic Health Centre Ɗ aurayi Kano, 15/1/2022

[22] Hira da Malam Isa Shu’aibu Sokoto, 28/1/2022

[23] Hiira da Dr. Zaharaddeen Katsina. 25/10/2020

[24] Hira da Abbas Mai Kano Jega 17/01/2023

[25] Hira da Abbas Mai Kano Jega 17/01/2023

[26] Hira da Abbas Mai Kano Jega 17/01/2023

Post a Comment

0 Comments