Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Na Yi Mafarki Yana Zama Gaskiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah Malam barka da sapiya, Malam menene fa'idar mafarkin da zakayi Kuma Sai kaga mafarkin ya faru azahiri, ma'ana nine nayi mafarkin gani awani wuri na musamman washegari Kuma Sai gani nazo dai-dai wannan gurin da nayi mafarkin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace. Mafarki wani yanki ne na Wahayi. Ko kuma kashi ɗaya daga cikin Ɗari Na Wahayi.

Sabida haka Irin wannan yana Faruwa ga Mutumin Kirki. Amma ba wani Abu bane in banda Kawai Allah ya Nuna Masa Abinda zai faru da shi Ne. Sabida Haka Ba Wani Abu Bane da suka Nuna Cewar Kana da wata Karama, wadda ta Wuce ta sauran Mutanen da kake Raye tare da Su. Bare Ma Mutum ya zo yana Ji-ji da kai cewar yafi kowa. Kuma Akasari zakaga Abinda Ake Nunawa Mutum a Mafarki, wanda yake Faruwa Zahiri kamar Yadda Ya Gani ba Mafarki banda na Rashin jin daɗi ko kuma mai Muni. Domin Hadisi Sahihi, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace MAFARKI MAI KYAU DAGA ALLAH NE. MAFARKI MARAS KYAU KUMA DAGA SHAIƊAN NE.

Da wannan ne Ma Yasa Wasu suke amfani da Mafarkin da Suke yi su Maida Duk wani Mafarki da suka gani Dai-dai ne. Kuma Tabbas Ba Makawa wannan Abin Sai ya faru. Wanda kuma hakan ba Lalle bane. Sabida shaiɗan yana Shigowa Mutum ta wannan Hanyar dan ya Jefa shi a Wani hali na daban. A haka sai kaga Mutum ya Fara bokanci da tsafi da duba da Sauransu. Ko kuma ya ɗauki duk wani Mafarki da yayi a Matsayin Gaskiya ne. Wanda kuma ba haka bane. Domin Mutum zai Iya Gani a Mafarki ga wani Abu yana Faruwa a gidan wani Mutum. Sai ya Baiwa Mutumin nan Labarin abinda yake Faruwa a gidansa. Kuma idan aka je sai a ga haka Abin yake. Kaga ke nan shaiɗan ya ɓullowa Mutum ta wannan hanyar dan ya Halakar da shi. Ya zama Mafarki Maras kyau. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya Ambata cewar Mafarki Maras kyau daga shaiɗan Ne.

Sabida haka Ke nan. Indai ba Alkairi Mutum ya Gani a Wannan Mafarkin Nasa ba to shaiɗan ne. Ba zai Baiwa kowa Labari ba. Sabida manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya hana bayar da Labari Akan Mafarki Maras kyau. Koda Kuma bayan Wannan Mafarkin ya ga Wannan Abin ya faru a Zahiri. Indai Maras kyau ne to ba daga Allah Bane. Domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam cewa yayi. IDAN MUTUM YAYI MAFARKI MARAS KYAU. KAR YA BAIWA KOWA LABARIN WANNAN MAFARKIN. Sabida Mutum zai Iya sanya Wannan Abin Maras Kyau a Zuciyarsa. Wanda hakan zai Iya Jefashi zuwa ga Wani Hali na daban.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments