Matar Aure Mara Sha’awa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

     As-Salaam Alaikum. Magidanci ne yake da matar aure mara sha’awa, yana shan wahala sosai wurin neman biyan buƙatarsa a wurinta. Takan tsara masa wasu abubuwan da sai ya cika su kafin ya samu biyan buƙatar, wasu lokutan ma sai ta gama lamarrunta kafin ta saurare shi. Abin har yakan kai shi ga bin wasu hanyoyi kamar kallon haram domin gamsar da buƙatarsa. Wai wace shawara za a ba shi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Da farko dai wajibi ne ma’aurata su san cewa biyan buƙatar juna ta hanyar saduwa yana daga cikin manyan dalilai ko maƙasudan yin aure.

    Kauracewa Shinfidar Miji ba Tare da Wani Karɓaɓɓen Uzuri a Shar'ance ba Yana Daga Cikin Manyan Zunuban da Saboda Girmansu Har Ubangiji Ya La'anci Matar da take Aikata Haka. Hadisi Ingantacce Ya Tabbata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yana Cewa

    عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم-: ”إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشه فأبت فبات غضبان عليها؛ لعنتها الملائكة حتى تصبح

    {مسلم: ١٤٣٦}

    An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: “Idan Miji Ya Kira Matarsa Zuwa ga Shinfidarsa Taqi Zuwa, Za ta Kwana Ana Fushi da Ita; Mala'iku Zasu Dinga tsine Mata Har Gari ya Waye”.

    {Muslim: 1436}

    Haƙƙi ne mai girma a kan mace ta zama a cikin shirin biya wa mijinta wannan buƙatar a duk lokacin da ya yi buƙata, matuƙar dai ba tana cikin yanayi ko halin da sharia ta hana saduwa a cikinsa ba ne, kamar a lokacin rashin lafiya ko haila ko nifasi. Har a waɗannan lokutan ma malamai sun yarda cewa matar tana taimaka wa mijin wurin jin daɗi da duk inda ya so a jikinta, ta hanyar shafa ko runguma ko sumba da makamantansu, in ban da saduwar ta wurin da aka hana. Watau, bai halatta ya yi amfani da al’aurarsa a cikin gabanta a lokacin haila ko nifasi ba, haka ma ta cikin duburarta, ko ta cikin bakinta ba a kowane lokaci.

    Amma a lokacin da miji ya ga irin wannan matsalar a cikin matarsa, abu na farko da ya kamata ya fara dubawa shi ne: Ta yaya aka samu hakan? Matsalar daga wurin ta ne, ko kuwa daga wurin sa ne?

     

    Abin nufi a nan shi ne: Me yiwuwa matar tana da wata matsala ta damuwa ko rashin lafiya ne shiyasa take gudun saduwar. Ko kuma ba ta da sha’awar saduwar da namiji ne, saboda ta riga ta shiga ƙungiyar masu maɗigo da suke neman yawaita a wannan zamanin! (Allaah ya kiyaye).

    Haka kuma matsalar tana iya kasancewa saboda dalilin yadda shi ya fara mu’amalantarta a karon farko ne, ko kuma yadda yake mu’amalantarta har a yanzu. Watau, me yiwuwa a karon farko da ƙarfi ya yi mata, ba tare da kulawa da ƙoƙarin janyo hankalinta ko motsar da shaawarta ga buƙatar ba. Ko kuma me yiwuwa ba ya damuwa da ita ta samu nata biyan buƙatar ko ba ta samu ba. Shi dai kawai idan ya gama buƙatarsa shike nan, babu ruwansa!

    Shi dai mu’amalar saduwa a tsakanin ma’aurata, kamar yadda masana suka yi bayani, ba abu ne da za a ɗauke shi irin yadda wasu sabbin angwaye da amare suke ɗaukarsa ba: A riƙa neman shi a kullum da safe, da rana, da yamma, da daddare kamar ibadar Sallah da Salati! Abin da babu wanda zai ƙwace maka, kuma babu ranar da zai ƙare har zuwa mutuwa, menene na haɗama ko gaggawa a kansa?

    Shi ana zuwa masa ne a lokacinn da buƙatarsa ta taso kawai, kamar dai abinci. Amma sai ka ji wasu a kan haka wai har magani suke sha, domin ya nuna mata shi namiji ne! Ko wai ta nuna masa ita ba ƙaramar mace abar wasa ba ce! Irin wannan shi ke janyo matsala a tsakanin maaurata idan ba a samu daidaito a tsakaninsu ba.

    Maganin wannan dai ma’aurata su zauna, ko dai su kaɗai ko tare da wani amintaccen masani, domin bayar da shawarwari masu amfani a kan wannan matsalar. Muhimmi dai su riƙa laakari da yanayi da halin buƙata ko rashinta daga juna a kowane lokaci, kafin neman biyan buƙatar. Ita dai mace, kamar yadda na faɗa a baya, a kullum ta zama a cikin shirin biya wa mijinta buƙatarsa.

    Al-Imaam Muslim (1403) da Al-Imaam Abu-Daawud (2151) da Al-Imaam At-Tirmiziy (1158) sun riwaito hadisi sahihi daga Sahabi Jaabir (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

    Watarana Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ga wata mace a waje, don haka sai ya tafi gida wurin matarsa Zainab (Radiyal Laahu Anhaa), ya same ta tana aikin jeme wata fata. Sai ya biya buƙatarsa a wurinta, sannan ya fito wurin Sahabbansa, ya ce

    « إِنَّ الْمَرْأَةَ تُقْبِلُ فِى صُورَةِ شَيْطَانٍ ، وَتُدْبِرُ فِى صُورَةِ شَيْطَانٍ ، فَإِذَا أَبْصَرَ أَحَدُكُمُ امْرَأَةً فَلْيَأْتِ أَهْلَهُ ، فَإِنَّ ذَلِكَ يَرُدُّ مَا فِى نَفْسِهِ »

    Ita mace tana fuskantowa a cikin siffar shaiɗani ne, kuma tana juyawa a cikin siffar shaiɗani ne. To, idan ɗayanku ya ga wata mace, sai ya koma gida ya sadu da matarsa. Wannan shi zai mayar da abin da ke a cikin ransa.

    Wannan ya nuna

    1. Mace a gidan mijinta tana zama a cikin shirin biya masa buƙatarsa ta saduwa ce a duk lokacin da ya yi buƙatar hakan daga wurinta.

    2. Zama cikin wannan shirin ba ya hana mace ta cigaba da wasu ayyukanta na yau da kullum a cikin gidan, kamar yadda ya same ta tana gyara fata.

    3. Ba daidai ba ne mace ta zauna haka nan kawai, ba ta aikin komai sai latsa wayoyi da kallon tashoshin nuna fitsara iri-iri.

    4. Wannan shi ke haifar da matsaloli a cikin gidajen auren zamunan yau, domin ma’aurata suna yin watsi da haƙƙoƙin da suka zama wajibai zuwa ga abubuwan da ba su da muhimmanci a rayuwarsu!

    5. Bai halatta mace ta tsara wa mijinta wasu abubuwan da wai sai ya gama yi mata su, sannan ne za ta amince ta biya masa buƙatarsa ba.

    6. Idan kuma ta tsaya a kan yin hakan, to bayan zunubin hana shi haƙƙinsa, akwai kuma taimakawa wurin buɗe ƙofar yin zina a wurin mara tsoron Allaah, musamman ma a wannan zamanin.

    7. Sannan yaya matsayin irin wannan matar zai kasance a lokacin da mijin ya samu damar auro wata matar kirkin da ba ta yi masa irin wannan?

    Allaah ya faɗakar da mu.

    Kallon tsiraici domin wai samun biyan buƙata da kwantar da shaawa shi ma matsala ce. Domin bayan ya saɓa wa koyarwar Addini, akwai kuma koyon munanan ɗabi’u da halaye a cikinsa. Wani namijin kan iya ƙoƙarin kwatanta duk abin da ya gani a cikin waɗannan hotunan, wanda kuma ba gaskiya ba ne, domin tsara su ake yi a fim kawai. Wannan shi ke kai wani ga cutar da jikinsa, ko kuma ma ga hallaka kansa. Kamar yadda wata macen ma kan kasa gamsuwa da mijinta, saboda bai iya yi mata irin yadda ta ga ana yi a cikin irin waɗannan fima-fiman ba!

    Abin da ya ke magani dai shi ne, duk mu ji tsoron Allaah kawai a cikin zamantakewarmu a gidajen aurenmu. Kar mu sake mu bi hanyoyin son-kai, ko cutar da abokin zamanmu ba da haƙƙi ba. Kar mu ɗauki al’amarin saduwar aure ya zama kamar abincin da babu makawa a rayuwa sai an ci shi, mu riƙa yin haƙuri da juna, mu nisanci shaye-shayen magungunan ƙarin ƙarfi, ko masu janyo ƙarin shaawar saduwa ba da wata larura ko umurnin masana ba.

    Amma idan duk waɗannan hanyoyin da makamantansu sun gaza kawo maslaha a tsakanin ma’aurata, to suna iya ɗaukar matakin rabuwa da juna, ko dai ta saki ko kuma ta khul’i a ƙarƙashin koyarwar Sunnah.

    Da fatar Allaah ya zaunar da gidajenmu lafiya, mu iya haƙurin tarbiyyar yayanmu tarbiyyar musulunci sahihiya.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.