Ticker

6/recent/ticker-posts

Bana Sha'awar Mace Sai Namiji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum, Mallam inada tambaya kuma zan ji dadi idan za a iya amsa mun. Mallam mutun ne balagagge namiji, tun lokacin da ya malliki hankalin shi yasan cewa yana cikin matsala, amma ya rasa inda zai danganta matsalan saboda ya daure masa kai. Bai taɓa kawo son mace a zuciyan shi ba ko sau ɗaya, baya taɓa sha'awar mace illa namiji kamar shi. wannan ba saboda yana kallon batsa bane ko kuma yana tare da marasa imanin mutane ba. A'a tun yana karami ake fada masa, cewa yakan daukan dankwali ya daura, yanayin sa ma kamar mace yake yi. muryan shi ma idan ba kasan shi sosai ba sai ka dauka mace ce magana, abun yana damun sa sosai, ya kai ga idan yayi barci yayi mafarki da maza yake yi wato saduwa har maniyyi ya fita. Toh mallam yanzu ya rasa yadda zai sa kanshi. wannan wace irin matsala ce? Kuma wani hanya za a bi wajen samun shifa'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To Ɗan'uwa tabbas ka haɗu da babbar musiba, sai dai akwai shawarwari da nasihu kamar haka

1. Ka rinka yawaita istigfari, saboda yana warware matsaloli, sannan sha'awar maza tana kaiwa zuwa ga luwaɗi, Allah ya hallakar da al'uma kacokan saboda suna aikata luwaɗi.

2. Ka dinga yawaita addu'a a lokutan da ake amsar roko, kamar cikin sujjada da karshen dare, saboda Allah zai iya karɓar kukanka, ya kare ka daga wannan fitinar.

3. Duk lokacin da tunanin namiji ya zo maka a zuciya ka yi kokari wajan kautar da tunanin zuwa wani abu daban mai amfani.

4. Shagaltuwa da ayyukan alkairi na taimakawa wajan kaucewa Alfasha.

5. Tuna azabar Allah da girmansa, suna taimakawa wajan barin saɓo.

6. Kada ka dinga kwanciya bacci, sai lokacin da ka tabbatar kana jin bacci, saboda tunane-tunane suna yawan zuwa a wannan lokacin.

7. Nisantar abokan banza yana gyara halaye.

8. Nisantar cakuduwa da maza zai taimaka maka wajan rashin sanya su a rai.

9. Yawaita karatun Alqur'ani na nisanta mutum daga Shaiɗanu, waɗanda suke juya dabi'ar mutum.

Tare da cewa akwai mutanen da Allah yake halitta suna da siffofin mata saidai ya wajaba ka yi iya bakin kokarinka wajan nisantar kamanceceniya da mata, saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata, a hadisi mai lamba ta:5546 a Sahihul Bukhari, sifar da ka yi iya bakin kokarinka ta ki canzuwa, to Allah ba ya dorawa rai sama da abin da za ta iya, kamar yadda aya ta karshe a suratu Bakara take nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments