Ina Da Tsananin Sha'awar Mace, Mene ne Mafita?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Mallam Tambayata a nan shi ne na kasance matashi yaro mai kimanin shekara 20 kuma ina da wata sha'awa sosai wacce idan ta tashi hankalina baya kwanciya, kuma ga yawan mafarki ina saduwa da mata kala kala kuma kusan kullum sai nayi sha'awar mace ???

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam To duk wanda yake son ya kubuta daga shaukin mata da kuma da kallon haram, to ya nemi taimakon Allah, sannan ya dawwama akan salloli guda biyar, domin ita sallah tana hana alfasha da mummunan aiki, sannan kuma kar ya manta da addu'a da Kankan da kai a lokutan amsar addu'a ga Allah maɗaukaki, ( kamar lokacin sahur da tsakanin kiran sallah da ikama da cikin sujjada) ya dinga yawaita cewa

    يَا مُقَلِّبَ الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ

    Ya mai jujjuya zukata ka tabbatar da ni akan addininka.

    Ya kuma yi kokari wajan nisantar wuraren fitina ta hanyar canza su da halal mai tsarki, ya dinga tuna faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam cewa: (Duk wanda ya bar abu saboda Allah, to Allah zai canza masa da abin da ya fi shi alkairi).

    Ibnu Mas'ud yana cewa: "Duk wanda wata mace ta burge shi, to ya tuna kazantarta (Fitsarinta da bahayarta) " saboda hakan zai sa ya shi ba ya sha'awarta.

    Sannan ka yi kokari wajan yin azumin litini da alhamis, saboda yana rage sha'awa, ka kuma nisanci yawan cin kayan-marmari, saboda suna tada sha'awa, kuma mutukar mutum yana cin su, to ko ya yi azumin ba zai rage

    masa sha'awa ba yadda ya kamata.

    Allah ne mafi sani

    DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.