𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam Watane tana Tambaya in sun haɗu da saurayinta sai sunyi
kissing suna hugging amma basa saduwa kuma tana so tadena wannan aikin amma
takasa yaza tayi Malam nagode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus salam, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah.
Zina (yin fasikanci)
ba wai yana nufin saduwa kawai ba, a'a, akwai zinar hannu, wato taɓa abinda yake haramun, da
zinar idanu, wacce take ta kallon haram, duk da cewa zina wacce aka yi ta da
al'aura, ita ce zina wadda ake azabtar da wanda suka yi ta da azabar haddi.
An karbo daga Abu
Hurairata Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya ce: “Allah ya shar’anta wa kowane ɗan
Adam rabonsa na zina, wanda ba makawa zai aikata. Zinar idanu ita ce kallo,
zinar harshe itace magana, mutum yana iya buri da sha’awa, al’aura kuma ita ke
tabbatar da haka ko kuma ta musanta”. (Bukhari ya ruwaito shi, 5889; da Muslim,
2657).
Ba ya halatta ga musulmi ya yi kwadayin abubuwan da zasu kai
shi ga zina, kamar sumba, kadaitaka, taɓawa
ko kallo, domin duk waɗannan
haramun ne kuma suna kai ga mafi girman sharrin zina.
Allaah ( تعالى ) yana cewa
وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha
ce kuma ta mũnana ga zama hanya. (wato duk abin da ya ketare iyakokinsa: zunubi
mai girma, kuma muguwar hanya ce wadda take kai mutum wuta face sai idan Allah
Ya gafarta ma mutum). Suratul Isra’i 32].
Duban abin da yake
haramun ne yana daga cikin kiban Shaiɗan,
wanda ke kai mutum ga halaka, ko da bai yi da gangan ba tun farko. Allaah ( تعالى ) yana cewa
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ
يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ
اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
“Ka
ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare
farjojinsu (daga haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne Allah, ga
abin da suke aikatawa Masani ne.[suratul Al-Nur aya 30]
وَقُل
لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ
Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga ganinsu (daga
kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga haram)”. [suratul Al-Nur aya 31]
Ka yi tunani a kan
yadda Allah ya haɗa
lamarin runtse ido da mas’alar kiyaye farji (kare farjinta) a cikin waɗannan ayoyi, da yadda aka
fara ambaton runtse ido, kafin kare al’aura, domin ido yana rinjayar zuciya
wajen aikata zunubi.
Shaikh Abdul'Azeez bn
Baaz (rahimahullah) yana cewa: A cikin waɗannan
ayoyi guda biyu, Allah ya umurci muminai maza da mata da su runtse idanuwansu,
su kiyaye farjinsu, saboda tsananin girman zina da abin da yake haifar da
fasadi mai girma a tsakanin musulmi. Barin kallonsa ga abinda yake haram yana
daga cikin abubuwan da ke haifar da cuta a cikin zuciya da faruwar ayyukan
fasikanci, yayin da runtse ido yana daga cikin hanyoyin kiyaye kai daga hakan. Don
haka Allah ( تعالى ) yake cewa
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ
يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ
اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
“Ka ce wa muminai
maza su runtse daga ganinsu (daga kallon haram), kuma su tsare farjojinsu (daga
haram). Wancan ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da
suke aikatawa." [Suratul Nur Aya 30].
Runtse ido da kiyaye farjin shi ne mafi tsarki ga mumini
duniya da Lahira, amma mutum ya bar kallonsa cikin walwala da rashin kiyaye
farjinsa suna daga cikin manya-manyan sababi na halaka da azaba a duniya da
kuma Lahira. Muna rokon Allah ya kara mana kare mu.
Allah ya gaya mana
cewa shi Masani ne ga abin da mutane suke aikatawa, kuma babu wani abu da yake ɓoye a gare shi. Wannan
gargadi ne ga muminai a lokacin da suke aikata abin da Allah ya haramta da
nisantar abin da Allah Ya shar'anta musu, kuma tunatarwa ce a gare shi cewa
Allah yana ganinsa, kuma ya san dukkan abin da yake aikatawa, na alheri ko
waninsa. Kamar yadda Allah ( تعالى
) yake cewa
يَعْلَمُ
خَائِنَةَ الْأَعْيُنِ وَمَا تُخْفِي الصُّدُورُ
"ALLAH yana
sanin ha'incin idanu, da abin da qirji ke ɓoyewa".
[Surat Ghafir Aya 19]
Ƙarshen
magana Daga bakin al-Tabarruj wa Khataruhu.
Wajibi ne musulmi ya
ji tsoron Ubangijinsa a ɓoye
da bayyane, kuma ya nisantar da abin da Allah Ya haramta na kadaita shi da wani
ma'abocin jinsi, kamar kallo, ko musafaha, ko sumbata da sauran ayyuka na haram
wadanda ke kai ga aikata fasikanci (zina).
Kada a yaudari juna
da tunanin cewa ai ba zina ake ba, kawai dai sumbata ne da runguma, kuma shi
wanda aka yaudara ya tsaya a kan wannan cewa ba komai bane, ko soyayya ce ko
aure zamuyi, ya sani irin wannan laifin ke kai ga aikata babbar zina, kuma a
karshe a zo ayi abinda za a zo ana da - na - sani.
Kuma ayi duk iya kokari wajen nesanta kai daga wannan
mummunar dabi'ar da kazantar, domin kazanta ce mace ta sa bakinta akan bakin
saurayin da bata aura ba, bama ta gama sanin rayuwarsa ba, kuma zunubi ne mai
girman gaske da ke kai mutum ga azabar Allah maɗaukaki.
Kuma babbar hanyar nesanta kai daga wannan mummunar dabi’un shi
ne rabuwa da wanda ake yi dashi, da guje masa, da rashin haɗuwa dashi, da kuma tuba
na gaskiya da istigfari, kuma mutum ya ɗaure
yayi aure sai ya huta daga irin waɗannan
kananan zunuban da sukan kai mutum zuwa shiga wuta, Allah ya tsare mu.
Wanda ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan ayyukan to ya tuba
ga Allah, domin duk wanda ya tuba Allah zai karɓi
tubarsa, wanda ya tuba kamar wanda bai yi zunubi ba ne.
Ɗaya
daga cikin mafi girman kaffarar irin waɗannan
zunubai shi ne yawaita salloli biyar akan lokaci. Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce: “Salloli biyar, da daga wata Juma’a zuwa wata, da kuma
watan ramadan zuwa wani, suna kankare zunubban da suka shiga tsakani, matukar
dai an nisanci manyan zunubai”. Muslim ne ya rawaito shi, 1/209
Kuma Allah ne Mafi
sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.