Table of Contents
- Tsakure
-
1.0
Gabatarwa
- 2.0 Manufar Bincike
- 3.0 Dabarun Bincike
-
4.0
Waiwayen al’adun zamantakewa tsakanin Hausawa da kaza
- 5.0 Nau’o’in Kajin Hausa
- 5.1 Amfanin Kaza
- 6.0 I llolin Kaza
-
7.0
Tasirin Zamantakewar Hausawa da Kaza a Adabin Baka
- 7.1 Tasirin Kaza a Cikin Karin Magana
- 7.2 Tasirin Kaza a Cikin Tatsuniya
- 7.3 Tasirin Kaza a Cikin Kacici-kacici
- 7.4 Tasirin Kaza a Cikin Kirari
- 7.5 Tasirin Kaza a Cikin Habaici
-
7
.6 Tasirin Kaza a
Salon Magana
-
7
.7 Tasirin Kaza a
Labara Hausa
-
8
.0 Na
ɗ
ewa
- Manazarta
Citation: Aminu, N. & Rambo, R.A. (2024). Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 349-357. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.040.
Gurbin Kaza a Zamantakewar Hausawa: Duba Cikin Adabin Baka
Daga
Dr. Nasiru Aminu
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Phone - 07067706006
nsrklg@gmail.com
Da
Dr. Rabi’u Aliyu Rambo
Department of Nigerian
Languages,
Usmanu Danfodiyo Univesity, Sokoto.
Phone: 08125507991
dirindaji12aa@gmail.com
Tsakure
Wannan ma
k
ala ta yi nazari a kan rayuwar Hausawa
a zamantakewarsu da kazar Hausa. Tunanin wannan ma
ƙ
ala ya samo asali ne daga duban irin
yadda Bahaushe ya sha
ƙ
u da kiwon kaza zamunna da yawa, da yadda sunanta ya samu
matsayi a wasu sassan adabin baka. Ma
ƙ
alarta kuma hango
cewa ko bayan sassan jama’a, akwai wasu abubuwa kamar dabbobi da tsuntsaye da
tsirrai da ke da muhimmanci a cikin muhallin Bahaushe wan
ɗ
anda zumuncinsu da al’umma na da tasiri da matsayin da ya
kamata a yi nazari. Manufar wannan ita ce yin amfani da wasu sassan adabin
Hausa a fito da wani sashe na falsafar rayuwa da al’adu da zumunci a tsakanin
Bahaushe da kazar Hausa. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su domin cimma
manufar wannan bincike akwai tattaunawa da jama’a da duba ayyukan masana da
tattaro maganganun azanci da wasu bayanai na adabi masu ala
ƙ
a da aiki kai tsaye a cikin al’ummar
Hausawa.
An kuma
yi amfani da Ra’in
Nazarin Al’adu daga adabin baka (Cultural Studies Theory) wanda ya ba da dama
tsauro bayanan al’ada daga adabin baka ta hanyar yin la’akari da yanayin
rayuwar al’umma da tattalin arziki da tsarin zamantakewa da yadda suka yi
tasiri a rayuwar al’umma. Wannan ya ba bincike tsakuro bayanai game da adabin
baka da
ƙ
unshiyarsa da kuma
wasu al’adu da
ɗ
abi’u da suka shafi rayuwar Hausawa dangane da
dangantakarta da kaza. Sakamakon bincike ya tabbatar da cewa akwai zumuncin
zamantakewa tsakanin al’ummar Hausawa da wasu tsuntsaye kamar kaza wanda
tasirin ya haifi wasu nau’o’in adabin bakan Hausa masu bayanin wasu al’adu da
ɗ
abi’un Hausawa.
1.0
Gabatarwa
Al’adun
al’ummar Hausawa suna tsira ne a muhallin da ake aiwatar da su, su ya
ɗ
u, su bun
ƙ
asa wasu wurare. Shi kuma adabi wani fage ne da ake
nazari domin fito da yadda al’adu suke, da kuma matsayinsu a cikin al’umma,
Ɗ
angambo, (1984). Don
haka. kowace irin al’umma a duniyar nan tana da nata ke
ɓ
a
ɓɓ
un
ɗ
abi’u da al’adu da ke
iya tantance kowace iri ce, mai amfani da tsarin rayuwa tun kaka da kakanni ko
na zamani, wa
ɗ
anda hotonsu ke iya fita daga adabinta. Wannan tunani ne
ya tayar da magana a
kan duba rayuwar Hausawa
ta gargajiya daga adabin bakan Hausa. Sai dai a nan, akwai wasu abubuwa da aka
yi la’akari da su a
ƙ
o
ƙ
arin fito da hoton
rayuwar da ake tunani. Daga ciki akwai tsarin rayuwa da
ƙ
addarorinta da
tunanin Bahaushe a tsarin zamantakewa da rayuwa. A cikin takardar an yi bitar
yadda zumuncin mutum yake gudana a tsakaninsa da kazar da yake kiwo da yadda
wannan zumuncin ya haifar da wani sashe na adabin bakan Hausa da ya zama taskar
al’adu da halaye da
ɗ
abi’un al’umma.
Wannan ma
ƙ
ala tana da tunanin
cewa kaza na da matu
ƙ
ar muhimmanci ga
rayuwar Hausawa wadda ta zama sanadin bun
ƙ
asar adabin bakan Hausa. Shi kuma adabi da
ɗ
a
dd
en abu ne da ake
aiwatarwa da ka, a kuma adana shi da ka. Yana kiyaye al’adu da
ɗ
abi’un al’umma, ya fito da halin rayuwar al’umma zamunna
masu tsawo zuwa zamanin yau. An kasa wannan ma
ƙ
ala zuwa sassa guda
uku. An yi tsokaci game da adabin baka da matsayin kaza ga Bahaushe da kuma
fito da wasu sassan rayuwa daga adabin kazar Bahaushe.
Ita kuma yanayin zamantakewar Hausawa na nuni da irin
dangantaka da mu’amala da ke wanzuwa cikin al’umma tsakaninta da jama’a ko wasu
abubuwa da ke zaune ko tare da ita a rayuwar yau da kullum. Irin wannan yanayi
na zama tare ne ake iya hangowa domin gano wata dangantaka da ke gudana
tsakanin jama’a da al’dunsu. Wannan yana da ala
ƙ
a da cewar Adoro, (2013:127), “Halaye da al
’
adu su ne al’umma, duk al’ummar da ta rasa su, to ita kaman
an gama da ita, domin su ne madubin kowace al’umma. A cikin wannan nazari an
kalli yadda zamantakewa da kaza ta haifar da wasu al’adu tsakaninsu da magidanta
da sauran jama’a da ke kiwon kaji a matsayin sana’a ko don biyan wasu bukatu
kamar yadda suka fito a cikin adabin baka na Hausawa.
A nan yana da kyau a fahimci cewa bayan ita kanta kazar
wadda jigo ce a wannan bincike, shi ma adabin da aka gina da sunanta da al’adun
da ya
ƙ
unsa na da babban matsayi wannan aiki, da kuma matsayinsa
ga al’ummar Hausawa.
2.0 Manufar Bincike
Manufar wannan takarda ita ce yin amfani da wasu
sassan adabin bakan Hausa a fito da wani sashe na al’adu da falsafar rayuwa da irin
zumuncin da ke akwai tsakanin Bahaushe da kazar Hausa wadda yake mu’amala da
ita a matsayin abukiyar zama ta hanyar kiwo.
3.0 Dabarun Bincike
Dabarun
bincike na nufin hanyoyi da hikimomin da mai bincike ya yi amfani da su wurin
aiwatar da bincike tun daga farko har zuwa
ƙ
arshensa.
ƙ
amusun Hausa,
(2006:82) ya bayyana dabara a matsayin kyakyyawan shiri ko wayo ko hikima ko
tsari, na aiwatar da wani abu. A ta
ƙ
aice, dabarun bincike na nufin bin diddidgin wani abu
bisa tsari cikin haza
ƙ
a domin gano wani
sabon abu ko tabbataswa da yin gyara. Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da
su a wannan bincike sun ha
ɗ
a da;
Duba ayyukan da masana suka gabatar game da ma’ana,
matsayi da muhimmancin adabi da rabe-rabensa, kamar karin magana da habaici da
salon magana da tatsuniya da labarai da makamantansu.
An kuma shiga a cikin al’ummar Hausawa aka yi hira da
wasu mutane aka tattaro wasu nau’o’in adabin baka da suka shafi kaza, wa
ɗ
anda su ne zuciyar wannan aiki.
Sai
ɗ
ora aikin a kan Ra’in Nazarin Al’adu daga adabin baka
(Cultural Studies Theory) wanda ya ba da dama tsakuro bayanan al’ada da wasu
dab’iu da halayya jama’a daga adabin baka ta hanyar yin la’akari da yanayin
rayuwarsu ta yau da kullum wadda ta shafi tattalin arziki da tsarin zamantakewa
da tarbiyya da jagoranci don fito da yadda suka yi tasiri a rayuwar al’umma.
4.0
Waiwayen al’adun zamantakewa tsakanin Hausawa da kaza
Masana da dama sun yi bincike a cikin mujallun ilimi da
kimiyya, kan kiwon kajin Turawa da kajin gargajiya na Hausa. Daga cikin akwai
Nwosu, (1979) wanda ya yi bincike game da wasu
ɗ
abi’u da suka shafi
kajin gida (na gargajiya) da Ayieko, (2014), shi kuma ya yi bincike ne yadda
kiwon kaji ke amfanin al’umar Masueni ta
ƙ
asar Kenya. Sai Maikasuwa da Jabo, (2011), sun yi nazari
kan matsalolin kiwon kajin Turawa a
ƙ
asar Sokoto. Akwai Nwagu, (2002), ya gudanar da bincike
kan matakan kiwon kaji na gargajiya da na Turawa.
Daga cikin manyan dalilai da ke sa Bahaushe ajiye kaza
sun ha
ɗ
a da bukatar kiwo da kasuwanci
da abinci (
ƙ
wai da nama) da sha’awa
da magani. Bahaushe ya da
ɗ
e da al’adar kiwon
dabbobi da tsuntsaye har zuwa lokacin da Allah ya hore masa su, tamkar abokan
zama a muhallinsa. Dalilin haka ne, a yau ake samun ‘yan kasuwa wa
ɗ
anda hajarsu ba ta wuce kaji ba. A
ƙ
asar Hausa abu ne mai
wuya a sami gidan da ba a kiwon kaza, saboda tana da sau
ƙ
in kulawa, kusan ma a
ce ita take kiwon kanta, Aminu, (2015)
5.0 Nau’o’in Kajin Hausa
Daga cikin nau’o’in kaji akwai farare da ba
ƙ
a
ƙ
e da jajaye da wake-wake. Bayan haka, akwai masu kama da
zabuwa da hankaka (mai yankan batta) da kaza durgu (mai guntayen ga
ɓ
o
ɓ
i), haka kuma akwai
ƙ
uzugu (maras gashi a
jikinta) da kuma ja da surkin ba
ƙ
i a jikinta) da
ƙ
yanshen zakara,
Aminu, (2015). Har ila yau, a wata tattaunawa da Samaila Umar na Gidan Igwai
Sakkwato, ya ce daga cikin nau’o’in kaji akwai kaza mai tuntuwa da kaza fingi
da higirgita.
5.1 Amfanin Kaza
Bayan nau’o’in kaji bincike ya gano cewa kaza na
k
yan
ƙ
yasar
ƙ
wai a sami ‘ya’ya
‘yan-tsaki kafin su zama ‘yan burtaye zuwa matasan kaji har a samu kaji budare
da da
ƙ
wale. Daga wannan
matakin rayuwa sai zama kwalinto (zakaru) zuwa shekarun tsufa.
Bayan haka yana da kyau a fahimci wata ala
ƙ
a da ke tsakanin kajin Hausa da al’umma, kamar yadda
bincike ya nuna, Aminu, (2015) da Abdullahi, (2008), sun nuna cewa, idan uba ya
zana wa
ɗ
ansa sunan
mahaifinsa, idan aka
ɓ
ata wa yaron rai, ana
yanka masa kaza a matsayin rarrashi ga yaron. Bayan haka akwai wasu muhimman
batutuwa da suka shafi ala
ƙ
ar kaza da Baahaushe
kamar haka;
i
.
Tsafi da neman biyan bukata
a.
Haka
ana yanka jan zakara a wurin tsafin Uwar-gona, da wurin Bori da wurin
ƙ
auri, inda ake fige
wa mai haihuwa kaza guda a matsayin tallafin kula da lafiyarta.
b.
A
mafi yawancin matsafun Hausa, Tsafi da Bori ba su kammala sai da kaza.
c.
Sadaka
don neman biyan bukata a wajen wasu- malamai, ana yanka kaji.
ii
.
Al’ada
a.
Haka ma a fa
ɗ
uwar haure ga yaro. Idan ya jefa a kan
ɗ
aki zai samu zakara da safe.
Wannan ma wani camfi
ne da aka fi amfani da shi a can dauri.
b.
A al’adar ginar rijiya a wasu wurare
akan ba mai aikin ginar kaza da farawa da kuma idan
ya
ƙ
are.
c.
Akan
biya shara irin ta taubasantaka da kaza.
iii
.
Abinci
a.
Abinci/
ƙ
wai- Bahaushe na
amfani da kaza a matsayin abinci na morewa ga attajirai, ko a wurin liyafa, da
tarbon ba
ƙ
i, kaza na kashe
kunya inji Bahaushe.
iv
.
Bukukuwa
a.
Bukukuwa:
A nan ma duk wani buki na Bahaushe da ba a yi bushasha da nama ba kaji ba, to
lallai ana iya cewa bai
ƙ
ayatar ba, ko tsarin
abincin ya yi rauni.
v Aikata Ayyukan
Alheri, kamar;
a.
Tarbon
mahajjata bayan sun dawo gida daga aikin hajji. Al’ada ce ta Hausawa.
b.
Ziyarar
dangi a
ƙ
auye. Dangi kan ba maziyarta
kyautar kaza.
c.
Sallamar
ɗ
an reno. Idan kaka
mace ta yi reno ko yaye takan ba da kaza sallama ga jikanta.
vi Magani
Magani don neman
waraka da inganta lafiya. Wasu wurare da ake magani da kaza ko warkarwa da
inganta lafiya sun ha
ɗ
a da:
a.
Kaciya:
Reno da jinyar sabuwar kaciya ga yara
b.
Kariya:
Jinyar mai sabuwar kariyar
ƙ
ashi saboda wani
hatsari ko wata
ƙ
addara
c.
Budurcin
‘ya mace/ gyara ‘ya mace a satin aure.
d.
Mura:
Shirya farfesun kaza mai isasshen kayan yaji
e.
Maganin
maza da mazan zakara/gidibe
f.
Zuciyar kaza
g.
Bali
ƙ
oto.
Daga bayanan da aka
jeranta a sama, za a fahimci akwai zumunci da babbar ala
ƙ
a ta rayuwa a tsakanin Bahaushe da kaza lokaci mai nisa
zuwa yau. Wannan na iya zama dalili da ake iya ganin hoton wannan zamantakewa a
cikin wasu sssan adabin bakan Hausa.
6.0 I llolin Kaza
Bayan da wannan
takarda ta yi bitar wasu fa’idojin ko amfanin kaza a cikin al’ummar Hausawa, ta
kuma yi kokarin fito da wasu muhallai da Bahaushe ke ganin illar kazar a
zamantakewarta da Bahaushe, daga cikin akwai yawan yin kashi da banna da tono
da rashin tsafta da makamatansu. Ga bayanin wasu daga ciki;
a.
Kashi: Kashi a Hausar Sakkwato na nufin tutu. Kaza tsuntsuwa ce da ke
yawan yin tutu a duk inda ya zo mata ba tare da la’akari da cewa ta
ɓ
ata wuri ko ta
ƙ
azamtar da wani bagire ba. Tana iya yin kashi a saman shimfi
ɗ
a ko a baranda ko a
cikin
ɗ
aki ko wani bagire da bai dace ba. Wannan ne ya sa mafi yawan Hausawa ba
su bukatar zama da ita a wuri daya. Daga cikin
ɗ
abi’unta na yin
kashi, tana da bukatar jama’a su gayara wuri mai kyau ko su yi shimfida domin
zama amma da kaza ta hau kansa sai ta zuba kashi kafin ta wuce. Idan kaza na
kwa
c
in
ƙ
wai, a duk lokacin da ta fito sai ta zuba kashi mai warin gaske. Shi
kuma kashin kaza yana daga cikin na’u’in najasa da Bahaushe ya tsananta.
b.
Ɓ
anna: Kazan na da yawan yin
ɓ
anna. Wato ishe an yi shanyar wani abu mai daraja kamar garin abinci ko
an tara shara, sai ta shiga ciki ta yi tono, ta watsar da shi. A wasu lokuttan
takan waste shi ta yadda za a iya yin hasararsa har idan mai amfani ne. Haka
idan ta samu an ajiye tumatir ko kayan miya ko ruwa ko wani abu tana iya sa
bakia ciki ta
ɓ
annatar da su. Don haka wasu rukunin jama’a ke ganinta a matsayin ma
ɓ
annaciya.
c.
Rashin tsafta. Ana ganin kaza kamar mai yawan tsafta ta hanyar gyaran
jikinta a koyaushe, amma Bahaushe na ganinta a matsayin dabba mai rashin tsafta
ta hanayar cin kowane abinci da ya ja hankalinta. Daga ciki kuwa har da najasa
tana i
ya
sa baki ga najasa cikin gida ko bayan gida. Kaza na da sha’awar zama
kusa ruwan ta
ɓ
o. Wani lokaci takan yin wanka da habdi ko kasa ko wani rairayi maras
tsafta. Irin wannan dabi’a c eta sa ake ganinta maras tsafta.
d.
Cin najasa. Kaza na cin kashin yara ko na manya a bayan gida. Cin kasha
kuwa ba
ɗ
abi’a ce mai kyau ba. Don haka Bahaushe ya tsane ta a irin wannan yanayi
e.
Shan
ƙ
wai; Yayinda Bahaushe yake ajiye kaza don amfani da ita a wasu mahallai
na abinci ko samun ‘ya’yan kaji domin nama ko kasuwanci, akwai kajin da ke sa
mai su yin hasara. Ana samun irin wannan hasara ta shan
ƙ
wai. Takan sha
ƙ
wan da ta nasa kafin tai kwanciya, ko kuma a lokacin da take kan
kwanciya da
ƙ
yan
ƙ
asa. Bahaushe ba
ya son hasarar ko da
ƙ
wai
ɗ
aya ne na kazarsa. Ya fi so ta
ƙ
yan
ƙ
yashe su baki
ɗ
aya.
f.
Tono; Hauswa na ka ce kaza mai yawan tone-tone. Kaza takan yi wannan ne
domin ta samu kwari da tsutsa da ke cikin kasa a matsayin abinci gare
ta ko ya’yanta.
Sakamakon haka takan
ɓ
ata shar
a
r da aka yi ko
kuma
ta t
ay
a
r
da
ƙ
ura a cikin gida
.
g.
Kafar-kai: Kazan na da kafewa, a yi kora har a gaji ba
ta tafiya. A wasu
lokutta sai an hada da kare sannan a kora tat a gudu ko ta bar wuri. Ita ma
kazar da ta saba da shiga cikin daki ko hawan tabarma, bat a bari sai an kai
ruwa rana da iyalin gida.
h.
Fa
ɗ
a/ sa
ƙƙ
wata: idan kaza ta fito daga
ƙ
yan
ƙ
yasa, a koyaushe za a tarar tana da fa
ɗ
a da yara ko wasu
kaji. Wannan kan kai ga sa
ƙƙ
wata ko c
i
zo domin ta kare
‘ya’yanta
daga yara ko wasu kaji.
Irin wa
ɗ
annan abubuwa da aka
lissafa a sama na daga cikin wasu illoli dab AHAUSHE ya fahimta na halaye da
dabi’un kazar Hausa. Wannan baa bin mamaki ne ba, domin Hausawa na cewa mutun
dan tara ne bai cika na goma ba. Manufa dukda cewa mafi yawanci daga rayuwarta
abin amfani ce ga Bahaushe, amma, a kan samu wasu muhallai da take da gaira ko
sabani.
7.0
Tasirin Zamantakewar Hausawa da Kaza a Adabin Baka
Adabi ya kasance wata taska da ake iya adana dukkan
al’adun al’umma daga aure da haihua har zuwa mutuwa. Dalilin wannan bayani shi
ne, domin duk wani abu da ake nema game da al’umma, za a iya samun sa a cikin
adabi al’ummar. Adabi yakan fito da darajar al’umma a idon duniya. Akwai ir-iren
adabi guda biyu a
ƙ
asar Hausa. Adabin
gargajiya da adabin zamani. A wani
ƙ
aulin akan kira su adabin baka da rubutaccen adabi.
Masana sun ba da bayani game da adabin baka wa
ɗ
anda ra’ayoyinsu ke da ala
ƙ
a makusanciya . Alal misali, Bunza, (1995) ya ce “Adabin
baka na Hausa shi ne wanda ake ya
ɗ
a shi, ake aikata
shi, ake tsara shi da adana shi duk da ka”. Shi kuma Ibrahim, (1985) ya bayyana
adabin baka a matsayin abin da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni. Su ma
Muhammad, (2003) da Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M. (2007) suna da madangancin
wannan ra’ayi.
Ganin irin yadda
Bahaushe ya kusanci kiwo da zama da kaji da yake amfani da su, don abinci da
biyan wasu bukatoci na rayuwa da gina tattalin arzikinsa, ya sa rayuwarsa ta
yau da kullum a baki-
ɗ
aya take da ala
ƙ
a da irin abubuwan da yake da dangantaka ko zumunci da
su, zamani mai tsawo zuwa yau, Aminu, (2015).. Wannan ne ya haifar da wata
makusanciyar dangantaka a tsakanin Bahaushe da kaza a dukan
ɓ
angarorin rauwa. Ana iya tabbatar da haka ta hanyar kafa
hujja da da
ɗ
a
dd
un hikimomin magana da tatsuniya ko labaran Hausawa.
Wannan kan faru a lokacin maganar yau da kullum a tsakanin jama’a ta furta
maganganu ko yin tsokaci na habaici ko gugar zana da karin magana, ko labarai
na gargajiya, bisa kwatance da rayuwar kaza a gidan Bahaushe. Bisa ga al’adar
Bahaushe duk abin da ya samu matsayi a adabin bakan Hausa, abu ne da ya ratsa
tunani da rayuwarsa ta yau da kullum. Za a iya fahimtar haka idan aka yi
la’akari da yadda aka yi amfani da suna ko halin rayuwar kaji domin gina wa
ɗ
annan karin maganganu na azanci da ake isar da sa
ƙ
onni, kamar haka:
7.1 Tasirin Kaza a Cikin Karin Magana
Karin magana, wata dabara ce ta dun
ƙ
ule, magana a cikin
‘yan kalmomi ta amfani da hikima a ta
ƙ
aice, yayin da wasu ke yi mata kallon dun
ƙ
ulalliyar magana
wadda ke
ɗ
auke da sharhi a kan
rayuwa cikin hikima da fasaha. Tana nuna
ƙ
warewar harshe da
ƙ
ara wa magana armashi, bayan zamanta madubi na al’adun
al’umma.
Da yawa a cikin Karin maganar Hausa Hausawa maza da mata
kan yi amfani da karin magana mai ala
ƙ
a da kaza domin isar da wani sa
ƙ
o fito da hoton wani
abu ko wata dangantaka zuwa ga wanda yake son isarwa. Alal misali, “A bar kaza
cikin gashinta”. Wannan karin magana ne da ke
ƙ
o
ƙ
arin nuna hali ko
bukatar sirrantawa ko rufin asiri a tsakanin mai magana da masu sauraro. Akan
gabatar da irin wannan domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wani
al’amari mai rikitarwa. Hakan ba ya rasa nasaba da halin Bahaushe na bukatar
rufa wa juna asiri a addinance.
Bayan haka idan Bahaushe na cikin wani tashin hankali ko
da alamunsa ya fahimta, ba shakka yakan
ɗ
auki matakai na janyo hankalin makusantansa ko dangi ko
ma
ƙ
wabcinsa domin samun taimako ko ba da shawara. Haka yake
yake, a irin
ƙ
arar da kaza kan yi
idan ta za a yanka ta, kusan duk wanda ke kusa yakan ji
ƙ
ararta. Saboda haka
idan akwai wani hali na tashin hankali ga wani akan gabatar da Karin Magana mai
cewa “Awai! Kaza ta ji wu
ƙ
a a wuya”.
A halayen
Ɗ
an’adam akwai nuna
iyawa da
ƙ
wazo da
ƙ
asaita da za
ƙ
ewa a wurin aiwatar
da wani abu. To haka shi ma Bahaushe yakan samu kansa a cikin irin wannan hali
da yanayi na rayuwa, nan take za a yi masa garga
ɗ
i a cikin Karin Magana da ke nuna masa ya wuce wuri. A
irin wannan ne ake samun Karin maganar da ke cewa “Abin mamaki kaza ta jawo
muzuru kwanan gida” ko kuma
‘Karambanin kaza auren muzuru’. Wato a duk inda aka frta
irin wannan karin magana, an aikata abin da bai dace ba, kuma ana zaton
mummunan sakamako tare da shi. A cikin al’ummar Hausawa akan samu irin wannan
ko a tsakanin matasa da masu sana’ar maza.
Wani al’amari ko yanayi da ake iya amfani da Karin Magana
mai ala
ƙ
a da kaza, musamman
wurin kwananta (akurki) shi ne a inda mutun ya shiga halin
ƙ
a
ƙ
a-nikan-yi, hali na
wahala na rashin mafita. A nan tilas ya yi wa kansa mafita domin ceton
rayuwarsa don haka a wurin ba da labari yakan yi amfani da Karin maganar da ke
cewa “Akurki ma abin kwana ne idan rana ta
ɓ
aci” wato Karin Magana ce mai kama da “wanda yace duhu,
to bai ji zawo ba”. Idan aka duba ba sunan kaza a ciki, amma a sanadinta ne aka
samu akurki. Don haka Karin Magana ne mai ala
ƙ
a da kaza, sanadiyar
zama-tare.
Bayan haka akwai
jerin Karin maganganu dake fitar da wani yanayi ko hali ko
ɗ
abi’a irin ta rayuwar Hausawa da a kaikaice ake tsarma
Karin Magana mai ala
ƙ
a da kaza domin samun
mafita ko garga
ɗ
i ko horarwa da dai
makamantanu ga misalansu:
Karin Magana |
Jigonta |
Ala
ƙ
a da darasi |
Albarkacin
kaza
ƙ
adangare kan sha
ruwan kasko |
Samun
Alfarma |
Darajar
wani, wani kan samu |
Buki
na farar kaza, balbela ba gayyata akai ba |
Bukin
Dangi |
Gayyata
da zumunci |
Ana
muzuru ana shaho, zakaran da Allah ya nufa da cara sai ya yi |
Arziki
da samu |
ƙ
addarorin rayuwa |
Fatara
mai sa a sayar da kazar kwanci |
Talauci |
Neman
mafita
Wuya
mai sa a sayar da damen iri |
In
ka ga da
ƙ
walwar kaza kasuwa,
in babu gurdumu/
ɗ
an hoda
,
akwai shan
ƙ
wai |
Ciwo
da rashin
ɗ
a’a |
Cuta
da cutarwa |
Wurin tone -tone
kaza ta tono wu
ƙ
ar yanka ta |
Garga
ɗ
i |
Tsaro |
Kada
kaza ta yi murna don ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta |
Garga
ɗ
i/ jin
ƙ
ai |
In
ka ga gemun
ɗ
an uwanka ya kama
da wuta..
Inda
saniyar gaba ta sha ruwa na ta baya kan sha |
7.2 Tasirin Kaza a Cikin Tatsuniya
Tatsuniya wata al’ada wani tsararren labari ne da ke
ɗ
auke da hikima da nuna
ƙ
warewa da shiryawa da
nuni zuwa ga halaye na gari da tarbiyatarwa da nisha
ɗ
antarwa.
Ɗ
an Kaza Mai Layar
Ƙ
amzo
Ɗ
an Kaza ne mai layar
ƙ
amzo, ya kama hanya
zai je kar
ɓ
ar bashin babansa.
Kan hanya ya ha
ɗ
u da Kyanwa. Ta ce “
ɗ
an kaza mai layar
ƙ
anzo ina za ka” ya ce “zan je kar
ɓ
ar bashi ne”. Ta ce “ina zuwa”. Ya
ɗ
auke ta ya ka
ɗ
a cikin burgame. Yana
cikin tafiya. Ya ha
ɗ
u da kura, ta ce tana
zuwa, ya ka
ɗ
a ta cikin burgame.
Ya ha
ɗ
u da zaki ya ce yana
binsa. Ya
ɗ
auka ya ka
ɗ
a shi cikin burgame, ya ha
ɗ
u da talalla
ɓ
iya da ruwa. Da ya
isa mutanen suka ce wanga wane irin
ɗ
an kaza ne marar
kunya. A ha
ɗ
a shi da
ɓ
era, sai nan take ya fitar da kyanwa, ta cinye
ɓ
era. Aka sa shi cikin akuyoyi don su take shi, sai kura
ta fito ta cinye su. Mutane suka
ɗ
auko ta
ɓ
arya za su buge shi, sai talalla
ɓ
iya ta kwashe su. Aka
ɗ
ebo wuta, ruwa suka wanke wuta.
ƙ
urungus.
7.3 Tasirin Kaza a Cikin Kacici-kacici
Kacici – kacici a matsayin adabin baka tambaya ce ko
tambayoyi na wasa
ƙ
wa
ƙ
walwa kuma zaunannu
masu zaunannun amsoshi da mafi yawan lokuta yara kan yi a tsakaninsu.
Misali: -Yadda kaza takan yi
ƙ
wan nan, haka
ƙ
wan nan yaka yin kaza
- Da kwai da kaza,
wa ya riga duniya
7.4 Tasirin Kaza a Cikin Kirari
Shi ma kirari yana
ɗ
aya daga cikin adabin
bakan Bahaushe wanda ya gada kaka da kakanni. Ana yin kirari a lokuta
daban-dabam. Wasu na ganin sarakuna da muhimman mutane ka
ɗ
ai ake yi wa kirari domin fitar da kamanni da halayensu.
Ko ta yaya, kirari ya yi kama da yabo. ‘Yan ma’abba da maro
ƙ
a da masunta da ‘yan
wasan kokawa ko dambe da ‘yan tauri da mafarauta duk suna yin kirari yayin da
suke gudanar da wasanninsu ko sana’o’insu.
Kirarin da Sunan Kaza
Kirari |
Asali |
Alaka da darasi |
Zakara mai neman
suna ba da
ƙ
waya ka ci tsakuwa
|
Magidanci da
ciyarwa |
Daukar nauyi da
nuna isa |
Kaza uwar tone-tone
|
Zama tare |
Yawan tayar da
zaune-tsaye |
Zakaran gwajin dafi
|
Tsaro a zamantakewa |
Nuna zaruntaka |
Ɗ
an Kaza Mai Layar
Ƙ
amzo
|
Sihiri |
Siddabaru |
Kaza a ci a goge
baki |
Cimaka |
Tsafta da nuna
hadama ko butulci |
Ɗ
an kaza samu ka
ƙ
i dangi |
Nakkaso cikin
habaici |
Raunan matsayi |
7.5 Tasirin Kaza a Cikin Habaici
Wani
ɓ
angare na adabin
bakan Hausa shi ne Habaici. Habaici zance ne da ake yi da
ɓ
oyayyar ma’ana wanda ke
ƙ
auke da wata manufa
ta daban wadda ba kowa ya san tab a, sai wanda aka yi wa. Akan gina habaici a
kan wani abu da ake tsammanin ya ta
ɓ
a faruwa.
Idan aka kalli ta
ƙ
aitatun bayanai da ke sama, ana iya fahimtar cewa dukansu
sassa ne na adabin bakan Hausa, kuma bayanan da aka gabatar suna da ala
ƙ
a ta kusa da wannan
takarda.
a.
Ko ba a gwada ba linzami ya fi
ƙ
arfin bakin kaza.-
FIFIKO
b.
Mu aka wa sammu a
ƙ
asa, da zakara ya tono wu
ƙ
a a
ƙ
asa.- WAIBUWA
c.
Ba samun abin duniya ba wurin ci nai.- HADAMA
d.
Da
walakin tuwon ‘yan ga aiki da guraye.- WUCE GONA DA IRI/TUHUMA
e.
Wata
sabuwa kaza ta ji shi
ƙ
ar dare.-
KWANKWANTO/ZAMANANCI
f.
Kaza a ci a goge baki.- HA
Ɗ
AMA/TSAFTA/BUTULCI - KA WA MUTUM RANA YA YI MA DARE
g.
In
fitsari banza ne kaza ta yi.- ABIN DA BA YA YIYUWA/GAGARA
h.
Ɗ
an kaza in ka samu gudani dangi.- HADAMA
i.
Cin dan
ƙ
o har da su kaza.- ABU YA YI BANZA
7
.6 Tasirin Kaza a
Salon Magana
Yadda
ƙ
wan nan yakan yi kaza, haka kaza takan yi
ƙ
wan nan.
7
.7 Tasirin Kaza a
Labara Hausa
Labarin Muzuru da Zakara da Kare
Wata rana da Mazuru
da zakara ana wasa, sai kwa
ɗ
ayi ya kama mazuru. Nan da nan, ya canja ra’ayinsa ya kame zakara da
niyyar ya cinye shi. Ya kama hanya zuwa bayan gari domin ya cika gurinsa, sai
suka ha
ɗ
u da kare ya fito yawon neman abinci.
Sai ya shiga tsakanin zakara da mazuru, ya ce me ke
faruwa? Nan take muzuru ya ce “Ai wasa ce muke yi”. Zakara ya ce ‘Haka ake wasa
da kaina a cikin bakinka? Nan take mazuru ya saki zakara ya gudu, shi ma ya
ranta a cikin na kare don kada kare ya gama da shi. Ashe ko gaba da gabanta.
8
.0 Na
ɗ
ewa
Daga bayanan da suka gabata ana iya fahimtar cewa akwai
tasirin adabin baka a zamantakewar kazar Hausa da al’ummar Hausawa. Bincike ya
yi amfani da wasu sassan adabin baka da aka gina da kazar Hausa, aka fito da
wani sashe na falsafar rayuwa da zamantakewa a cikin al’umma. Daga ciki, akwai
tsarin rayuwa da halaye da
ɗ
abi’u da fa
ɗ
akarwa da makamantansu. Don haka yana da muhimmanci
manazarta su fa
ɗ
a
ɗ
a kafofin bincike ta hanyar duban dangantakar Hausawa da wasu
abubuwa ko halittu da suke zaune tare, maimakon mayar da hankali kan al’adun
aure da haihuwa da mutuwa da suka shafi jama’a. wannan zai inganta fito hoton
al’umma a wasu muhallan rayuwa.
Manazarta
Abdullahi, I. S. S.
(2008) Bamaguje da
Ɗ
an Akuya:
Ƙ
auna ko
Ƙ
iyayya? Departmental Seminar, Department of Nigerian
Languages Sokoto: Usmanu Danfodiyo Universty.
Adamu, M. (1976),
“The Spread of Hausa Culture in West Africa 1700 – 1900” Savannah
A Journal of the
Environmental and Social Sciences. Zaria: No 5. Vol. 1, Ahmadu Bello
University.
Adoro,
A. L. (2013) Halin Zamantakewar Hausawa Tsakanin Jiya da
Yau, in Experts of International Seminar on Ta
ɓ
ar
ɓ
arewar Al’adun
Hausawa (The Deterioration of Hausa Culture) Organised by Katsina State History
and Culture Bureau and Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina. Zaria: Ahmadu
Bello University, Press.
Ajayi, F.O. 2010. Nigerian Indigenous Chicken: A Valuable
Genetic Resource for Meat and Egg Production.
Asian
Journal of Poultry Science, 4: 164-172.
Alhassan, H. (1982). Zaman Hausawa Zaria, A.B.U. Press.
Aminu, N. (2015) Kaza ga Bahaushe, Jiya da Yau, Algaita Journal of Current Research in Hausa
Studies. Special Edition. Department of Nigerian Languages, Bayero
University, Kano. Vol. 1 no. 1, Pages 631 – 638. ISSN: 2141-9434, Zaria: Ahmadu
Bello University, Press.
Ayieko, D.M.O. and Bett, E.K. and Kabuage, L.W. (2014)
Profitability of Indigenous Chicken: The Case of Producers in Makueni County,
Kenya. Journal of Economics and
Sustainable Development, Vol 5, No. 11, 2014. ISSN 222-2855.
Blench, R. (1997) Neglected
Species, Livelihoods and Biodiversity in Difficult Areas: How Should the Public
Sector Respond? In Natural Resources
Perspectives, Number 23, Sept. 1997.
Chicken – Wikipedia, the
Free Encyclopedia- en.wikipedia.org/wiki/chicken – Retrieved 08/11.2023,
8:58 p.m
Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano (2006)
Ƙ
amusun
Hausa. Zaria, Ahmadu
Bello University Press.
Copland, J.W. and
Alders, R. G. (2005) The comparative advantages of village or smallholder poultry
in rural development, in the
Proceedings
of an international conference held in Dar es Salaam, Tanzania, 5–7 October
2005. ACIAR
Ɗ
ahiru, I. (2012) Nuni
Cikin Rayuwa Daga Labaran Dabbobi, Kundin Digiri na Biyu,. Department of
Nigerian Languages, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Ibrahim, A. A, Aliyu, J., Wada, N.I and Hassan, A. M
(2012) Effect of Sex and Genetype on Blood Serum Electrolylete and Biochemical
Parameters of Nigerian Indigenous Chickens, Iranian
Journal of Applied Science, 2012, Vol, 2 No. 4, PP. 361-365, Dec. 2012.
Ishaq, Y. (2013) Sirrin
Mijinka a Tafin Hannunka Bugawar Da
ɗ
in Kowa Publishers, Kano, Nijeriya
Junaidu, I. da
‘Yar’aduwa, T. M. (2007) Harshe da Adabin
Hausa a Kamalle don Manyan Makarantun Sakandare. Zaria: Spectrum Books
Limited.
Maikasuwa, M. A. and Jabo, M.
S. M. (2011) Profitability of Backyard Poultry Farming in Sokoto Metropolis,
Sokoto State, North-West, Nigeria, in
Nigerian Journal of Basic and Applied Science, 2011, 19 (1): 111- 115
Makarantar Hausa
(2007) ‘Bahaushen Zakara ya Fi Mutum Iya Zama da Iyali, 1
& 2, Yuni da Yuli, Fitowa ta Biyu da ta Uku, shafi 42
Muhammad, Y. M.
(2003) Adabin Hausa Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
Nwagu, B.I. (2002). Production and Management of
Indigenous Poultry Species. A Training Manual in National Training Workshop on
Poultry Production in Nigerian National Animal Production Research Institute,
Shika, Zaria. 10 – 26pp.
Nwosu, C. C. (1979) Characterization of the Local Chicken
in Nigeria and its Potential for Egg and Meat Production. Proceedings of the
First International Seminar on Poultry Production, December 11-13, A.B.U Zaria,
Pp 187-210.
Sharif, H. S. (BS)
Ƙ
asaitacciyar Macce
mai Mallakar Mijinta,
Al-Amin Bookshop,
Mandawari Printing Press, Kano.
Rataye:
Kaza a Karin Maganar Hausa
A bar kaza a cikin gashinta
A wai! Kaza ta ji wu
ƙ
a a wuya
Abin mamaki kaza ta jawo muzuru kwanan gida
Akurki ma abin kwana ne idan rana ta
ɗ
aci
Albarkacin kaza
ƙ
adangare kan sha ruwan kasko
Ana muzuru ana shaho, zakaran da Allah ya nufa da cara
sai ya yi
Buki na farar kaza, balbela ba gayyata akai ba
Da walakin tuwon
danga aiki da guraye
Fatara mai sa a sayar da kazar kwanci
Hushin kaza ya huce a kan dami
In ka ga da
ƙ
walwar kaza kasuwa,
in babu gurdumu/
ɗ
an hoda akwai shan
ƙ
wai.
Kada kaza ta tono wu
ƙ
ar yanka ta
Kada kaza ta yi murna
don ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta
Karambanin kaza auren
muzuru.
Kaza mai ‘ya’ya ke
gudun shirwa.
ƙ
wai a baka ya fi kaza a akurki.
ƙ
wai ma ya yi wayo
balle
ɗ
an kaza
Maganar banza zakara ya taka wu
ƙ
a
Mai kaza a aljihu bai han
ƙ
urin has
Rashin sani kaza ta kwana a kan dami
Raina da
ƙ
una kaza ta kwana kan
dami
Sabo da kaza ba ya hana a yanka ta
Wanda ya ci kaza shi
ke da ita
Kaza a
Habaici Bahaushe
Mu aka wa sammu a
ƙ
asa, da zakara ya tono wu
ƙ
a a
ƙ
asa.
Ko ba a gwada ba
linzami ya fi
ƙ
arfin bakin kaza.
Ba samun abin duniya
ba wurin ci nai.
Da walakin tuwon ‘yan ga aiki da guraye.
Wata sabuwa kaza ta ji shi
ƙ
ar dare.
Kaza a ci a goge baki.
In fitsari banza ne kaza ta yi.
Ɗ
an kaza in ka samu
gudani dangi.
Cin dan
ƙ
o har da su kaza.
Kaza a
Salon Maganar Hausa
Yadda
ƙ
wan nan yakan yi kaza, haka kaza takan yi
ƙ
wan nan.
Kaza a Kirarin Hausa
Zakara mai neman suna
ba da
ƙ
waya ka ci tsakuwa
Kaza uwar tone-tone
Zakaran gwajin dafi
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.