Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Sha'awata Ta Motsa Bana Samun Sukuni Sai Na Kalla Video Batsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Allah gafarta menene hukuncin Wanda sha'awa tama yawa kuma bayason kallon batsa amma zuciyarsa ta kasa masa sai da ya kalla yake samun sukuni bayan kuma daga baya yazo yai nadama. Sannan wace addu'a yakama ta ya ringa karantawa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Na farko dai wannan alama ce dake nuna Qarancin tsoron Allah azuciyar masu yin haka. Sannan kuma da alamar cewa Zuciyarta tafi Qarfinta.

Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya ma Annabinsa Dawud (alaihis salam) cewa: "... Kuma kada kabi son zuciya balle ta ɓatar dakai kan hanyar ALLAH. Hakika waɗannan da suke ɓatarwa daga kan hanyar ALLAH, garesu akwai azaba mai tsanani saboda abinda suka manta na ranar hisabi".

Kuma acikin suratu Yusuf (alaihis salam) Allah ya ce: "hakika ita zuciya lallai mai yin umurni ce ga mummunan abu".

Allah shi ne ya halicci Ɗan Adam kuma ya sanya sha'awa ajikinmu domin ya jarrabemu ya bayyanar da bayinsa masu tsoronsa da kuma waɗanda suka karkace daga kan hanyarsa. Kuma ya kafa mana dokokin da zamu bi domin mu rabauta anan duniya da kuma ranar Qiyamah. Don haka Allah yace ma Annabinsa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam)

وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ ...

"ka gaya ma muminai mata su runtse daga idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu". (Suratul Nūr aya 32)

Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga Matayen Muminai, bayan kuma ya gargadi Mazaje Muminai. Kuma Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (rta) Yace Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce: "HAKIKA SHI KALLO, WANI KIBIYA NE MAI DAFI DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BARI DON TSORONA, ZAN CHANZA MASA DA WANI HASKE (WATO HASKEN IMANI) WANDA ZAI JI DANDANONSA ACIKIN ZUCIYARSA".

(Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy juzu'i na 10 hadisi na 10,362).

Kallon batsa bai halatta ba. Kuma cewa wai sha'awa ce ta yi miki yawa ba zai zama uzuri karɓaɓɓe agun Allah ba. Don haka kiji tsoron Allah ki rika tuna ranar gamuwarki dashi. Ki kiyaye dukkan gabobin jikinki daga saɓa masa.

Allah Maɗaukakin Sarki yana bada labarin ranar Alkiyamah. Ya ce: "AWANNAN RANAR DA ZAMU YUMQE (SANYA RUFI) BISA BAKUNANSU, KUMA HANNAYENSU NE ZASU ZANYAR DAMU, KUMA QAFAFUWANSU SUNA SHAIDARWA BISA ABINDA SUKA KASANCE SUNA TATTATAWA (NA LAIFUKA)".

Kiji tsoron ranar tonon asirai, ranar da Allah zai nunoki (kamar a vedio) gaki nan sanda kike aikata ayyukan sharrin da kika aikata.

Idan za ki tuba kiyi cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake so. Ba wai tubar Mayaudara ba.

Addu'ar neman shiriya kuwa babu kamar fatiha. Ki rika karantawa tare da halarto girman Ubangiji. Allah mai gafara ne mai rahama. Shi keda ikon shiriya da kuma yin gafara ga bayinsa.

Allah ya gafarta mana baki ɗaya, Aameen.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments