Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayin Da Yake Taɓa Jikin Budurwarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Menene hukuncin saurayin da yake taɓa jikin budurwarsa yana shafa mata nono da sunan Soyayya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

To wannan ba soyayyah bace kiyayyah ce, tsantsar soyayyah tana cikin yin ladabi ga Allah da Manzonsa Sallallahu alaihi Wasallam amma saurayi ya taɓa jikin budurwarsa wannan ai kiyayyah ce yake nuna mata ba soyayyah ba, wannan abinda suke aikatawa mummuna ce, Tun da Allah ya haramta taɓa jikin matar da baka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina.

Allah maɗaukakin sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da za ta kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu ne taɓa ko shafar jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsar da sha’awa zuwa ga aikata zina.

Duk macen da ta bada kanta wa wani dan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk yaudara ce, duk wanda za ki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani yazo gunki ba za ki bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa! ba wani sonki da yake kawai wani abu ya keso ya cimma akanki na mummunan aiki ya ɓata ki dajin kunyar duniya data lahira. Ki sani da zarar ya cimma mugun burinsa akanki shi ne zaifi kowa kyamarki da gudunki, koba kuɗi ba zai yarda ya aure ki ba.

Hadisi ya tabbata wanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen da bata hallata agareshi ba. Albany yace hadisine ingantacce acikin sahihul jamiul kabeer (5045).

kinji fa da ace yau gashi mutum ya taɓa matar da ba tashi ba yafi masa sauki ayi masa wancan aika-aikan kinga kuwa abin babba ne! Haka kuma babu makawa yayin wannan shafe-shafen dole ayi zinar ido, zinar kunne, zinar harshe da kuma zinar kafa.

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda dashi) Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce: ”Allah yana rubutawa ɗan Adam kasonsa na zina, zai riski wannan kason babu makawa, zinar ido itace kallo, zinar kunne saurara, zinar harshe zance, zinar kafa tafiya, zuciya ta yi buri ta yi sha’awa, farji shi zai yarda ko ya karyata”

Waɗannan hadisan kaɗai ya isa ya zama tsawa da firgitarwa ga samari da kuma ‘yan matan da ake yaudara da sunan ana sonku, ya isa kuji tsoron Allah ku tuba tun kafin lokaci ya kure muku, ku lazumci yiwa Allah biyayya cikin abunda ya haramta na dokokinsa, na daga abunda shafar mace yake haifarwa wanda yake kaiwa zuwa ga fitintunu da alfasha kala-kala.

lallai tsantsar soyayyah tana cikin bin tafarkin Allah da kuma bin Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments