Ticker

6/recent/ticker-posts

Zuwa Wajen Saurayi Babu Hijabi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta ga mace yayinda mai nemanta da aure yazo wajenta ta je wajensa ba tare da tasa hijab ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Asali dai shari'a ta umarci Maza da Mata su rintse idanunsu ga barin yiwa junansu kallo irin na sha'awa kamar yadda Allah() ya fada

قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ....

MA'ANA

(Ya Muhammad() ka gayawa Muminai (Maza) su rintse idanunsu kuma su kiyaye farjinsu, hakan shi ne yafi tsarkaka a garesu.... (Suratul Nūr aya 30).

To amma shari'a ta yi izini ga mai neman aure ya kalli matar da ya ke so ya aura, to sai dai kuma Malamai sunyi saɓani dangane da cewa ina ne iyakar gwargwadon inda ya kamata maneminta ya kalla a jikinta? Wasu daga cikin Malamai sai suka tsananta da yawa sukace bai halatta a ga komai a jikintaba, wasu Malaman kuma sai suka sassauta da yawa, sukace ya halatta a ga komai a jikinta amma banda tsiraicinta kaɗai, daga cikin hujjarsu akwai wannan Hadisi na Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama) da ya ke cewa

إذاخطب أحدكم المرأة فإن استطاع أن ينظر إلي ما يدعوه إلي نكاحها فليفعل،

Ma'ana

Idan dayanku yana neman mace da aure, to idan ya samu ikon ya kalli abinda zai ja hankalinsa ya aureta to ya aikata (ya kalla)

Sannan kuma akwai Malaman da suka tsaya a tsakiya, wato ba su tsananta da yawa ba kuma ba su sassauta da yawa ba, wanda ko shakka babu mafi yawa daga cikin Malamai sun tafi ne a kan wannan ra'ayi na tsaka-tsakiya, daga cikin hujjarsu akwai wannan aya da Allah() ya ke cewa

وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا

Ma'ana

Ka da Mata su bayyana adonsu sai dai abinda ya ke bayyanan ne daga ciki. (Fuska da tafin Hannu) (suratul Nūr aya 31)

Danhaka Malaman da ke Mazhabobin Malikiyya, Shafi'iyya, da kuma Hanafiyya. sukace iyakar fuska da tafukan hannu kaɗai ya halatta manemin aure ya gani, su kuma Mazhabin Hanabila sukace ya halatta a kalli dukkan gurinda a bisa ga al'ada yakan bayyan a ganshi a jikinta, wato kamar wuyanta, hannayenta, kafafuwanta, da kuma gashin kanta. Musamman ma yayinda mace ta ke cikin gida tana yin wasu 'yan aikace-aikace irin na cikin gida.

To amma maganar da tafi inganci kuma tafi dalilai masu Ƙarfi kamar yadda mafi yawan Malamai suka rinjayar itace, ya halatta mai neman aure ya kalli fuskarta da tafukan hannayenta da wuyanta, da duga-duganta, da kuma gashin kanta in buƙatar hakan ta kama, sai dai wasu Malaman sukace idan ya kalla sau ɗaya shike nan ya wadatar daga nan bai halatta ba ya sake kallo. amma wasu Malamam sukace ya halatta ya mai-maita kallonta idan buƙatar hakan ta kama, ko da kuwa ba tare da tasan yana kallonta ɗin ba, sai dai bai halatta yayi mata kallo irin na sha'awa ba wanda zai sa shi yaji daɗi a ransa. Sannan wannan hukuncin yana tabbatuwa ne a kan Mutumin da yazo neman aure tsakaninsa da Allah da gaske yakeyi ba wai da wasa ko yaudara ya ke yi ba, sannan yana da tabbas ko kuma zato mai rinjaye na cewa idan ya nema za a karɓeshi a yarda da da shi.

Sannan da sharaɗin ya kasance babu wani wanda yake nemanta a baya da har suka riga amince da shi a kan ya nemeta, saboda Manzon Aʟʟāн( Sallallahu alaihi Wasallam) ya hana wani ya nemi aure a kan neman wani

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

      Mυѕтαρнα Uѕмαи

       08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments