𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalmu alaikum, Mene ne hukuncin Mutanen da sukeyin
Sex-Chat, wato hirar batsa ta hanyar rubutun Text ko ta hanyar rubutu a
Social-Media musamman ta WhatsApp? Malam wallahi na Shiga bala'i Ka taimakeni
Nidai mutum ne Wanda Allah ya jarabceni da karfin sha'awa Kuma ban taɓa yin zina ba To Amma
wannan WhatsApp ɗin
ya haɗani da mutanen
banza an shigar dani wani group na batsa hotunan banza da videos ɗin banza Duk ina ganinsu
Rana ɗaya sheɗan yayi tasiri a kaina
wlh Malam wata yarinya da muka haɗu
da ita har hoton farjinta ta turomin nima na tura mata nawa, Sai da na Riga na
aikata hakan Abin yaketa damuna Na tuba Malam Allah zaiyafemin kuwa? Sannan
kuma Malam wane abu zan dage dayi Wanda Allah ba zai kamani da laifin ba
Wallahi nayi nadama.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To itadai hirar da akeyi ta batsa atsakanin Namiji da Mace
ta hanyar Ƙiran
Waya ko rubutaccen saƙo kamar yadda akafi saninta da sunan Sex-Chatting, ko Shakka
babu wannan wata Musibace da Fitina wacce ta addabi Al'ummar wannan Zamani
damuke cikinsa, tun daga kan Maza har Mata, masu aure da marasa aure, wasuma
daga cikinsu zaka samu cewa Ɗaliban Ilimine, danhaka al'amarin dai sai
wanda Aʟʟαн(ﷻ ) Ya tsallakar kawai,
itadai wannan hirar batsa takasune gida biyu,
1-Kodai yakasance Namiji zaiyi irin wannan hirarne da
Matarsa itama Mace ta yi da Mijinta,
2-Kokuma ya kasance Mutum zaiyi irin wannan hirarne da Matar
da ba tasaba ko Mijin da ba nataba,
Idan ya zamana Mutum zaiyi irin wannan hirarne da Matarsa ko
Mace ta yi da Mijinta, to yakan iya zama Halal amma Saida Sharuɗɗa guda biyu
1-Sharaɗi
nafarko yakasance babu wani Mutum akusa dasu ta yadda zai iyajin hirar dasukeyi
atsakaninsu idan yazamana suna hirarne ta hanyar Ƙiran Waya, idan kuma ta hanyar rubutune
to ya kasance sunkiyaye ta yadda babu wani wanda zai iyaganin hirar dasukayi
acikin rubutun, kokuma yaga irin hotunan sassan jikinsu da suka aikawa junansu,
balle kuma Mutum yace zaije ya nunawa abokansa ko ita ta nunawa ƙawayenta
irin hirar da sukeyi.
2-Sharaɗi
nabiyu, ya kasance tsakanin Matar da Mijin dukkansu sun aminta da kansu cewa
wannan hirar da sukeyi baza ta kaisu ga aikata dukkan wani abu ta hanyar wasa
da jikinsu wanda hakan zai iya kaisu ga sunfitar da Maniyyinsu ba, wato abinda
da akafi sani da suna istimna'i (Masturbation) idan waɗannan Sharuɗɗa
guda biyu suka cika to ya halatta ma'aurata suyi atsakaninsu, amma idan hirar za
ta iyasa wani daga cikinsu kokuma suduka sukai ga sunkasa iya mallakar kansu
harsai Mutum yayi abinda zai sashi yafitar da Maniyyinsa to anan suma kansu
ma'auratan yazama haramun suyi irin wannan saboda wancan mummunan aikin da
hirar za ta iya kaisu ga aikatashi, domin a Shari'ance akan iya Haramta abinda
yake Halalne idan yakasance zai iya kai Mutum ga aikata Haramun, amma idan
yakasance hirace kawai sukeyi atsakaninsu har Sha'awar Mutum takai Ƙololuwa
yayi Inzalin-Maniyyi batare da yayi amfani da hannunsa ba ko wani abu dabam to
wannan babu laifi ya halatta,
Amma idan yakasance ita wannan hirar ta batsa maisuna
Sex-Chatting, tana gudanane atsakanin waɗanda
ba ma'aurataba wanda kuma dama galibi ita wannan hirar anfi yintane kodai
tsakanin Samari da 'Yammata, ko Samari da Matan aure, ko Maza masu aure da
'Yammata, kokuma Mazan aure da wasu Matan auren da ba nasuba, danhaka wannan ko
kokwanto babu akancewa yin wannan hirar Haramunne Ƙaulan-Wahidan, danhaka
wajibine akan masu wannan aiki suyi gaggawar tuba zuwa ga Aʟʟαн(ﷻ
).
Maganar yafewa Kuwa: Allah yana yafe kowanne zunubi da bawa
ya ke aikatawa, idan ya tuba, amma banda shirka wato hadashi da Wani bawansa
wajan bauta. Kamar yanda Ayoyi da hadisai ingantattu da dama Suka nuna, Amma
akwai sharudan tuba
1. Dena zuzunubi.
2. Nadama Akan saɓon.
3. Ya Qudurci niyyar, ba zai sake aikata aikin ba.
Idan
aka rasa ɗaya daka
cikin ukun nan tuba bai tabbata ba. Sannnan kuma banda hakki mutane iyaka
hankinka tsakaninka da Allah. Sannan kuma kadege da neman gafarar Allah, ka
nesanci duk abinda zai kai ka ga aikata zantukan da zasu tada maka sha'awa,
Sannan ka lizimci azumin lafila saboda sha'awa da take damunka, da yawaita
istgfari.
Allah ya tsaremu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.