Ticker

6/recent/ticker-posts

Sallah Da Tufafi Mai Najasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Tufafin Mutum Yasamu Najasa Kuma Bai Samu Ruwanda Zai Wanke Ba, Bashi Dawani Tufar Dazayi Sallah Dashi Yaya Zaiyi?.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Sallah bata ingantuwa da tufa mai najasa, Mutum zai iya sallah ne da tufafi masu tsarki, saboda faɗin Allah madaukakin sarki:

ﻭَﺛِﻴَﺎﺑَﻚَ ﻓَﻄَﻬِّﺮْ

Ka tsarkake tufafinka. (Suratul Mudasir aya 4)

Wata mata tazo wajan Annabi Sallallahu Alaihi wasallam tace: Jinin haila yana taɓa tufafin wata daka cikinmu yaya za tayi? Yace; Tawankeshi daruwa Tamatse shi sannan Tayarfe ruwan, sannan saitayi sallah da tufafin.

Bukhari (227) da Muslim (291)

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceta data tsarkake tufar kafin tai sallah da ita.

Idan najasa tasamu tufafin mutuminda bashi da wani tufafin dazai sallah sai mai najasar kawai, baya wuce halayae uku

1- Zai iya wanke wajanda najasar datake jikin tufafin yai sallah dashi, kamar najasar ajikin hannun riga ko gefen karshen riga take, wajibine wanketa yai sallah datufafin, domin yanada ikon sallah datufafi maitsarki babu uzuri akansa idan yai sallah danajasa.

2- Zai iya cire tufafin batareda Al'aurarsa tabayyana ba, kamar idan yanasa wani kayan daka ciki wanda yake rufe al'aurarsa (gajeran wando singileti, sikel diras) wajibine yacire tufar yai sallah damai tsarki, saboda hakane Annabi sallallahu Alaihi wasalla yacire takalminsa mai najasa ajikinsa yana cikin sallah lokacinda jibirilu Alaihissalamu yasanar dashi akwai najasa ajikinsu.

Abu dauda (650) Albani ya ingnatashi acikin sahihu Abu dauda

3- Bashi da wani tufafin mai tsarki dazai sallah dashi kuma ba zai iya kawarda najasar ba, magana ingantacciya cikin zantukan malamai shi ne zai sallah dawannan tufar mai najasar, saboda yazama mai uzuri, kuma sallarsa ingnatacciyace ba zai sake sallar ba bayan yayita da tufafin.

Shaikul Islma ibnu taimiyyah Allah yajikansa ya ce: Wanda baisamu tufafi ba sai masu najasa kaɗai? Wasu malamai sukace: yayi sallah tsirara, wasu sukace: yai sallah datufafin Amma yasake sallar, wasu sukace: Yai sallar dasu haka ba zai sake sallar ba, wannan shi ne ingantaccen zance cikin zantukan malamai domin Allah bai umarci bawa yayi sallar farillah sau biyu ba, saidai idan baiyi wajibinda aka dora masaba tunfarko, kamar yai sallah babu nutsuwa zai sake sallah kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya Umarci wanda yai sallah babu nutsuwa acikinta ya ce: (Koma kayi sallah danbakayi sallah ba, haka wanda yamanta tsarki yai sallah babu alwala, zai sake sallah kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi ya umarci mai lam'a akafarsa bai wankeba yasake alwala da sallah, Amma wanda ya aikata abunda aka kaddara masa gwar-gwadon ikonsa Allah madaukakin sarki yace

 ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣَﺎ ﺍﺳْﺘَﻄَﻌْﺘُﻢْ ‏.

Kuji tsoran Allah gwar-gwadon ikonku.

Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce:(Abunda na Umarceku kuzo dashi gwar-gwadon Abunda zaku iya).

Majmu'u fatawa (22/ 34-35)

Saboda haka zaiyi sallah datufafinda suke danajasar babu komai akansa domin anmasa uzuri kuma ba zai sake sallar ba, bayan uzurin yagushe daka kansa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄��𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments