𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullaah. Allah gafarta Malam pls
ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce - hukuncen takaba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam To ɗan'uwa
akwai hukunce-hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:
1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba,
har sai ta gama iddarta, wacce take wata huɗu
da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan
وَالَّذِينَ
يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ
أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا
فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ
Kuma waɗanda
suke mutuwa daga gare ku suna barin matan aure, matan suna jinkiri da kansu
wata huɗu da kwana
goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, babu laifi a kanku a cikin abin da suka
aikata game da kansu ga al´ada. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.
(suratul Bakara aya 234)
2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado,
kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan.
3. Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda
hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan,
4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba,
kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan.
5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a
hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.
6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da
rana ne ko da dare.
7. Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan
bukatar hakan ta kama, saidai ta guji sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a
suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba.
يَا نِسَاءَ
النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ ۚ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ
بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا
Ya matan Annabĩ! Ba ku zama kamar kowa ba daga mata, idan
kun yi taƙawa,
saboda haka, kada ku
sassautar da magana, har wanda ke da cũta
a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani,
kuma ku faɗi magana
ta alheri. (suratul-Ahzab 32)
8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar'anta mata
ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su.
9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba.
10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta
iya buɗe gashin
kanta, idan su duka muharramanta ne.
11. Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama
idda, saidai za a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 a
Suratul Bakara ta yi nuni zuwa hakan.
وَلَا
جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُمْ بِهِ مِنْ خِطْبَةِ النِّسَاءِ أَوْ أَكْنَنْتُمْ
فِي أَنْفُسِكُمْ ۚ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِنْ لَا تُوَاعِدُوهُنَّ
سِرًّا إِلَّا أَنْ تَقُولُوا قَوْلًا مَعْرُوفًا ۚ وَلَا تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ
حَتَّىٰ يَبْلُغَ الْكِتَابُ أَجَلَهُ ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي
أَنْفُسِكُمْ فَاحْذَرُوهُ ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ
Kuma babu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga
neman auren mata ko kuwa kuka ɓoye
a cikin zukatanku. Allah Ya san cewa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma
amma kada ku yi wa jũna alkawari da shi a ɓoye,
face dai ku faɗi
magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littafin (idda) ya kai ga
ajalinsa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin
zukatanku, saboda haka
ku ji tsoronsa. Kuma
ku sani cewa Allah Mai gafara
ne, Mai haƙuri.
(Suratul Bakara 235)
12. Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife
abin da take ɗauke
da shi.
Allah shi ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.