Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yi Zina Tana Cikin Takaba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀��𝐀

Don Allah a yi mani Karin bayani akan hukuncin matan da take a cikin zaman iddar rasuwan miji (takaba) sai Shaiɗan ya rinjayeta ta yi zina da kuma ciki ya shiga kuma ta yi ikrari da bakinta cewa zina ta yi, shin za a iya jingina wannan ɗan ga mijin da ya rasu ko a’a? Allah ya yi maka jagora.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To dan’uwa tabbas wannan abin bakin ciki ne, ina rokon Allah ya kare mu daga zamewa, saboda yana daga cikin manufofin iddar takaba, kula da hakkin miji, duk matar da ta yi zina tana takaba, ba ta kula da wannan manufa ba, lokacin takaba lokaci ne na tuna miji, da nema masa gafara, da kuma neman kusanci da Allah, ba’a kwalliya a lokacin, ko da neman aure bai hallata ba ballatana Kaɗaita da namijin da ba muharrami ba, balle har aka kai ga alfasha, tabbas ya kamata mu ji tsoron Allah.

Ta aikata babban zunubi, kuma ɗan da aka samu, babu yadda za ayi a danganta shi ga mamacin, tun da maganarka tana nuna bayan ya mutu ta samu cikin.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments