𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀��𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Kwanakin takaba wata huɗu ne da kwana goma. To
ana nufin kwanaki 90 ke nan, ko kuwa watanni huɗu
na miladiyya da kwana 10?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Abin da Allaah Ta’aala ya faɗa
a kan hakan shi ne
وَالَّذِينَ
يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ
أَشْهُرٍ وَعَشْرًا
Kuma waɗanda
suke mutuwa kuma suke barin matan aure, matan suna haƙurin zama da kawunansu
na tsawon watanni huɗu
da kwanaki goma. (Surah Al-Baqarah: 234).
Kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« لاَ يَحِلُّ
لاِمْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ أَنْ تُحِدَّ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ
ثَلاَثٍ ، إِلاَّ عَلَى زَوْجٍ ، فَإِنَّهَا تُحِدُّ عَلَيْهِ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ
وَعَشْرًا »
Bai halatta ga macen da ta yi imani da Allaah da Ranar
Lahira ta yi takaba a kan rasuwar wani mamaci ba sama da kwanaki uku. Sai dai a
kan mutuwar miji, a nan kam tana yin takaba na tsawon watanni huɗu ne da kwanaki goma.
(Sahih Al-Bukhaariy: 1280).
Daga waɗannan
nassoshin da makamantansu muna iya fahimtar cewa
1. Lissafin kwanakin idda da takaba ana yi ne da lissafin
watannin musulunci, kamar dai na watannin kaffarar azumi.
2. Ba a amfani da lissafin watannin bature, domin a cikin
watanin bature akwai mai kwana talatin da ɗaya.
Akwai kuma mai kwanaki ashirin da takwas ma a wani karon.
3. Idan daga farkon wata ne aka fara takabar sai ta lissafa
watanni huɗun kawai,
ba tare da kallon ko watan ya cika ko bai cika talatin ba.
4. Idan kuwa daga tsakiyar wata ne ta fara takabar sai ta yi
lissafin kwanaki talatin sau huɗu
kawai, wato ɗari da
ashirin (30x4=120) ke nan.
5. Sai kuma ta ƙara da kwanaki goma, kamar yadda
nassoshin suka ambata. Ya zama kwanaki ɗari
da talatin (120+10=130) ke nan daidai.
6. Sannan tana fara lissafin ne daga ranar da mijin ya rasu
ko da kuwa ba ta sani ba, a marinjayiyar magana a wurin malamai.
7. Ibn Hazm (Rahimahul Laah) shi ne yake ganin mace tana
fara idda ko takaba ne daga ranar da labarin sakin aurenta ko mutuwar mijinta
ya isa gare ta. (Tamaamul Minnah: 3/227).
Don haka matar da mijinta ya rasu ran 18/10/2022 ba za ta
gama takaba ba sai a ran 26/2/2023, in shaa’al Laah.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu
Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta wadannan Links...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄��𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.