𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mata ce da mijinta suke zaune, amma kuma matar ba ta da
sha'awar namiji ko kadan, zaman nasu ya zama mara dadi, tana ganin kamar tana
cutar mijinta tunda shi yana da sha'awa, shin zamansu ya halatta kuwa a addini?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan har shi mijin ya kan neme ta idan sha'awarsa ta tashi,
kuma ta biya masa, babu laifi su ci gaba da zama tare, tunda za ta kare shi
daga faɗawa cikin
haramun, sannan akwai mata da yawa da Allah ya halicce su a wannan yanayin,
zamanku zai iya zama cuta ne idan har ya kasance ba kya biya masa bukata ta
yadda zai kalli matar da ba ta hallata a gare shi ba, an shar'anta aure ne
saboda samun zuriyya da kuma katange ma'aurata daga zina kamar yadda ya tabbata
a dalilan shari'a, duk auren da ya gaza cika waɗannan
manufofi akwai matsala a cikin shi.
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.