Ticker

6/recent/ticker-posts

Suratul Mulk Tana Tseratarwa Daga Azabar Kabari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Suratul Mulk Tana Tseratarwa Daka Azabar Qabari, Shin Sau Nawa Akeson Karantata Sau Ɗaya Arana Ko Samada Ɗaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Daka Abu huraira Allah yakara masa yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: akwai wata sura acikin Alqur'ani tanada ayoyi talatin za ta ceci mutum harsai Angafarta masa itace (Tabarakallazi biyadihil Mulku) Turmuzi (2891) da Abu dauda (1400) da ibnu majah (3786).

Shaikul Islam ibnu taimiyyah ya ingantashi acikin maj-mu'u fatawa nasa (22/277) da shaik Albani acikin sahihu ibnu majah (3053).

Abunda ake nufi da wannan shi ne mutum yakarantata kowanne dare, yakuma yi aiki da abundake cikinta na hukunce-hukunce, yayi imani da abundake cikinta na larabai.

Daka Abdullahi Ɗan Mas'ud Allah yakara masa yarda ya ce: Wanda yakaranta (Tabarakallazi biyadihil mulku kowanne dare, Allah zai hana masa Azabar kabari saboda ita, Mun kasance azamanin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam muna kiranta da (Mani'ah) lallai acikin littafin Allah akwai wata surah mai ayoyi talatin wanda yakarantata kowanne dare madallah dashi kuma ladansa ya yawaita, Nisa'i (6/179) Albani ya ingantashi acikin Sahihu Targeeb wattar-heeb (1475).

Malaman lajnatul da'imah sukace: Abisa wannan anasan duk wanda yai imani da wannan sura yakiyaye karantata, dan neman yardar Allah, da ɗaukar izina da abundake cikinta na wa'azozi da abubuwan lura, yai aiki da abundake cikinta danta ce-ceshi.

Fatawa lajnatul da'imah (14/ 334-335).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments