Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasan Kanin Miji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam menene hukuncin mai wasa da kanin miji ko kanin mata a musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam toh ba daidai bane mace ta dinga mu'amala da kanin mijinta yadda take mu'amala da mijinta, domin wannan al'adar ta maguzawace (wasan kanin miji) koh (daukan kanin miji amatsayin miji) adinga wasa da shi ana neman kuɗin kitso da kuɗin kunshi wataran ma agaban mijin ma ake kokuwa ake wasa tsakanin matarsa da kaninsa, wannan kuwa ya saɓawa musulunci domin kanin miji kuwa baya cikin mutanen da Allah ya yadda suga adon mace, wa enda Allah yajero ya ba su dama  suna iya ganin mace idantayi kwalliya to mutum goma sha biyu (12) ne aciki babu kanin miji, Allah ta'ala yace;

وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَىٰ عَوْرَاتِ النِّسَاءِ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 

Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna ƙawarsu face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mata, ko matan ƙungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai waɗanda. ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da ƙafafunsu domin a san abin da suke ɓoywa daga ƙawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo. (Suratul Nur aya 31)

Kinga anan dukka ba'a kawo kanin miji koh wanmiji ba acikin Waɗannan domin Waɗannan dukka suna iya aurenki idan miji ya sakeki, toh don haka babu alaka (koh kuyi wasa koh ya taɓa jikinki tsakaninki da kanin mijinki) duk wannan bai halattaba a muaulunci, kuma al'adace mummuna wasan kanin miji.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments