Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Rage Shekaru, Saboda Zuwa Bautar Kasa (NYSC) ?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mal. tambayar ita ce: shin ya halasta mutum ya yi service bayan shekarunsa na yin NYSC sun wuce, a dokar Idan mutum ya kai  shekaru (30) ba zai yi service ba, to Idan mutum ya yi, ya hukuncinsa yake? Nagode Allah ya Kara basira.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Haramun ne ya rage shekarunsa, mutukar sun wuce ka'idar da aka shata, saboda yin hakan algus ne da kuma cin alawin da mutum bai cancanci a ba shi ba.

A hadisin da Muslim ya rawaito "Duk wanda ya yi mana algus, to ba ya tare da mu".

Duk dokar kasar da ba za ta wahalar ba, Kuma ba ta ci karo da ka'idojin Musulunci ba, bin ta wajibi ne, kamar yadda ingantattun hadisai suka tabbatar.

Dukiyar Gwamnati ta 'yan Nigeria ce duka, bai halatta wani ya ci ba tare da hakki ba.

Arzikin mutum a rubuce yake ba ya canzawa, an dage alkaluman da aka rubuta kaddara da su, takardun kuma sun jima da bushewa.

Wanda ya kame Allah Zai kamar da shi, Ya azurta shi ta inda ba ya zaton, wadatar zuci, taska ce, da ba ta karewa.

Allah Ne Mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments