Ticker

6/recent/ticker-posts

Hujjar Cewar Komai Dawafi Yake A Sararin Sama

TAMBAYA (70)

Shin menene hujjar cewar komai dawafi (Bautar Allah) yake a sama da kasa ?

AMSA

Alhamdulillah

Allah Azzawajallah yace;

( وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مِن دَابَّةٍ وَالْمَلَائِكَةُ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ )

النحل (49) An-Nahl

Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma ba su kangara."

Tabbas, ba abune baqo ba idan akace maka musulmi suna zagaye dakin ka'abah a matsayin dawafi, amman idan akace maka "Duniya, wata da rana duk dawafi suma suke" dole mamaki zai baibaye mutum tareda tambayar to me sukeyiwa dawafin su kuma ?

Ilimin kimiyya a sararin samaniya (Astronomy) ne kadai yakeda cikakkiyar amsar wannan tambaya mai cikeda sarqaqiya. Masana ilimin kasa sun gano cewar garin Makkah shi ne tsakiyar duniya, tsakiyar Makka kuma dakin Ka'abah ne wanda aka fitarda Google map dinsa wanda kamar yanda bayani ya gabata cewar latitude na coordinate dinsa shi ne 21° degree, 25' minutes wanda idan ka dauki 2 din tafarko ita ce Sura ta 2 wato Suratul Baqara sauran numbobin kuma (125) na Suratu Baqara din shi ne ayar farko a cikin Qur'ani wadda tayi magana akan dakin na Ka'abah, inda Allah SWT yace;

( وَإِذْ جَعَلْنَا الْبَيْتَ مَثَابَةً لِّلنَّاسِ

البقرة (125) Al-Baqara

Kuma a lokacin da Muka sanya dakin ya zama makoma ga mutane,

Tun shekaru wajen 1,400 anfitarda location din Ka'aba a Qur'ani kafinma Geographers su gano (Allahu Akbar!)

Kamar yanda marigayi Dr. Bashir Usman Tofa yace a cikin littafinsa mai suna "Kimiyya a sararin samaniya": da awon matsawar launin shudin birnin Andromeda (Daya daga cikin samada galaxy miliyon 100 dake maqotaka da tamu acan sama) ne aka lissafa cewar yana dosomune da saurin kilometer 300 a kowanne second, amman kada muji tsoro domin muma birninmu (Milkyway Galaxy dake jihar Virgo) ba a tsaye yake ba, kuma da akwai dayawa masu nisantarmu da sauri fiyeda kilometer 1,000 a second daya

Abin lura anan shi ne, komai a sararin samaniya tafiya yake yana zagaya wani abu "tamkar dawafi" dukkansu daga dama zuwa hagu (anticlockwise direction) yadda musulmi suke zagaya Ka'abah a doron wannan duniyar tamu ta Ard, haka wata (moon) yake zagaye duniyarmu, ita kuma tana zagaye yar Shams (Rana), ita kuma ranar tana zagaya badalar anguwarta (Suratu Yasin 36:38) da saurin kilometer 250 a kowanne second, ita kuma anguwar tana zagaya tsakiyar birnin Milky way, shikuma yana zagaya Jihar Virgo, ita kuma tana zagaya babbar jihar (Super Cluster ta hannun gefen Orion) ita kuma tana zagaya wani, shikuma yana zagaya wani abu, shikuma yana zagaya samaniya ta daya, ita kuma tana zagaya ta 2, har zuwa dai sama ta 7

Dakata da karatu, kadan duba babban dan yatsan hannunka (fingerprints) zakafi gane bayanan dalla dalla, domin kuwa zakaga alamun kamar zagayen dawafi. Allahu Akbar! Nauyin Shams yakai kokuma ya zarce tonnes 200,000,000,000,000,000, amman dukda haka tana tafiya zagayenta (dawafi) da saurin kilometer 2,150 a kowanne second. Da wannan sauri takan dauki shekaru 250 kafin tayi zagaye daya, Ita kuma duniyarmu (Ard) tana zagaye daya a cikin 23 hours 56 minutes (24hrs approximately) dakuma kewaye (dawafi) daya a cikin kwanaki 365, wato shekara daya kenan. Allahu Akbar!

Muna roqon Allah Ya tabbatardamu akan musulunci bisa bin sunnar Ma'aiki SAW, ya rusa kafirci da kafirai

Burina mu duqufa wajen binciken ilimin Astronomy domin mu kara sanin ayoyin Allah SWT dake sararin Sama'ud Dunya

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments