Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ta Makaɗa Alhaji (Dr) Ibrahim Buhari Abdulƙadir Mai Dangwale Narambaɗa Tubali

Wannan ita ce Waƙar da Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Buhari Abdulƙadir Mai Dangwale Narambaɗa Tubali ya yi wa Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III, rerawar Halifansa Ummaru Mai Sa'a a cikin wata hira da Malam Sanda Adamu Sarkin Yaƙin Tsafe ya yi dashi Halifa Ummaru Mai Sa'a a Gidan Rediyon Nijeriya Na Kaduna, a cikin Shekarar 1974. Wannan Waƙar ta fito a Rataye dake cikin Maƙala ta da na gabatar a Taron Baje Kolin Hausa Na HIBAF Karo Na Biyu, Da Ya Gudana A Ɗakin Taro Na Arewa House, Kaduna a Watan Disambar Shekarar 2022, Mai Taken 'Da Tsohuwar Zuma.. Fasalta Narambaɗa da Shata da Ɗanƙwairo ga Matasan Yanzu. An wallafa ta ne a cikin Mujallar Zamfara International Journal Of Humanities, A Publication Of the Faculty Of Humanities, Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria Volume 2 /Issue 2, December 2023.
Jagora :
Rinjayayye Dattijo na Gatau,
Abubakar Uban Sarakuna,

Y/Amshi :
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau,
Abubakar Uban Sarakuna,

Jagora :
Garba na Alhaji sha da arna makaye,

Y/Amshi :
Garba na Alhaji tura haushi ɗan Hassan,

Jagora:
Garba na Alhaji sha da arna makaye,

Y/Amshi :
Garba na Alhaji sha da arna ɗan Hassan,

Jagora :
Namijin ƙwazo ginshimin Magajin Rwahi,

Y/Amshi :
Garba ya biya Kiɗi
Ya ban doki Abu na Amadu

Jagora:
Rinjayi maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Y/Amshi :
Da Bauchi da Kano da Katchina da Adamawa kai muka dibi, 

Y/Amshi :
Dama da hauni Shehu ad dasu, 
Shi ag gaba, shi am Mujaddadi, 
Ta tabbata Sakkwato maza suke, 
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Jagora:
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Y/Amshi :
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Jagora :
Ɗan Shehu Uban Gazobi kayi ƙwazo, 
Allah yayyi ma gudunmuwa,

Y/Amshi :
Milkin ga da Shehu yayyi kayi shi, 

Jagora : 
Ɗan Shehu Uban Gazobi kayi ƙwazo, 
Allah yayyi ma gudunmuwa, 

Y/Amshi :
Milkin  da Mu'azu yayyi 
ka yi shi, 

Jagora/Y/Amshi :
Dum milkin da Mu'azu yayyi ka yi shi, 
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Jagora :
Da kai wanga mai haƙon Giwa diba, 

Y/Amshi : 
Ta take haƙon da kayyi ta wuce, 

Jagora:
Da kai wanga mai haƙon Giwa diba, 

Y/Amshi :
Ta take haƙon da kayyi ta wuce, 

Jagora :
Kai diba kissa
Diba munahucci 
Diba wane in za ya gaisuwa, 

Y/Amshi :
In ya zamna makyarkyata ya kai 

Jagora:
Ai diba kissa
Kai ji munahucci 
Diba wane in za ya gaisuwa, 

Y/Amshi :
In ya zamna makyarkyata ya kai 
Bai san muni gyarai ba
an sani, 
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, 
Abubakar Uban Sarakuna, 

Jagora:
Garba na Alhaji sha da arna makaye, 

Y/Amshi :
Garba na Alhaji tura haushi ɗan Hassan

Jagora:
An ce mana wane ya ci ya kihe, 

Y/Amshi :
Ya dangana sai biɗaw wurin gudu. 

www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments