Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Muh'd Aminu, Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato da Marigayi Mai Girma Limamin Masallacin Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam dake Madina

Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Muh'd Aminu, Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato, Marigayi Mai Girma Limamin Masallacin Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam dake  Madina
"Abubakar Na Amadu ya gyara Masallaci, 
Ɗibgau Bajinin Dole". 

Farko daga gefen hagu Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Muh'd Aminu, Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato, Marigayi Mai Girma Limamin Masallacin Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam dake  Madina, Marigayi Mai Girma Alƙalin Alƙalan Jihar Arewa, Sheikh Abubakar Mahmud Gummi tare da Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris kafin ya zama Sarkin Zazzau a yayin wata ziyarar aiki da Limamin Madina ya kawo a Jihar Arewa a shekarar 1964. A wannan ziyarar ce dai Limamin na Madina ya buɗe Masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da Masallacin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio  da Gwamnatin Jihar Arewa haɗin Gwiwa da Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III suka gyara a Birnin Sakkwato. Aikin ne  Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya  ya taskace a cikin ɗan Waƙar da aka buɗe wannan bayani dashi. Allah ya kyauta makwanci, amin.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments