𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. An ce Allaah yana karɓan tuban bawa matuƙar bai kai gargara ba, to wai tuban yana nufin Kalmar Shahada ce?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam Ahmad da At-Tirmiziy da Ibn Maajah sun riwaito
hadisin da Al-Imaam Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Sahih At-Tirmiziy (2802)
da Sahih Ibn Maajah (3430), daga Sahabi Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa), daga
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« إِنَّ اللَّهَ يَقْبَلُ تَوْبَةَ الْعَبْدِ مَا لَمْ يُغَرْغِرْ
»
Haƙiƙa! Allaah yana karɓar tuban bawa matuƙar dai bai kai
gargara ba.
Kodayake wasu malaman Hanafiyyah sun zaɓi cewa, a kan kafiri
ne kaɗai ake magana a nan, amma dai maganar da ɗaukacin malamai suka zaɓa, kuma
wadda ita ce ta fi rinjaye ita ce: Hadisin yana nufin kowane irin bawa ne.
(Tuhfatul Ahwaziy: 9/53).
Watau: Bawan da ke aikata kowane irin zunubi babba ko ƙarami
ake nufi.
Sannan ma’anar: Matuƙar bai kai gargara ba shi ne: Ransa bai
kai ga maƙoshi a lokacin mutuwa ba. Watau: Bai kai ga ganin Mala’ikan Mutuwa
gar-da-gar ba. Kamar yadda Allaah ya ce:
وَلَیۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِینَ یَعۡمَلُونَ ٱلسَّیِّـَٔاتِ
حَتَّىٰۤ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّی تُبۡتُ ٱلۡـَٔـٰنَ
Babu tuba ga waɗanda suka yi ta aikata munanan ayyuka har
sai lokacin da mutuwa ta je wa ɗayansu sai ya ce: Yanzu kam na tuba. (Surah
An-Nisaa’: 18).
Haka ma abin da Ubangiji Ta’aala ya faɗa a kan Fir’auna a
lokacin mutuwarsa:
حَتَّىٰۤ إِذَاۤ
أَدۡرَكَهُ ٱلۡغَرَقُ قَالَ ءَامَنتُ أَنَّهُۥ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱلَّذِیۤ
ءَامَنَتۡ بِهِۦ بَنُوۤا۟ إِسۡرَ ٰۤءِیلَ
وَأَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِینَ
ءَاۤلۡـَٔـٰنَ وَقَدۡ عَصَیۡتَ قَبۡلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِینَ
Har sai lokacin da nutsewa a cikin ruwa ta riske shi sai ya
ce: Na yi Imani cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai wannan da Banu-Isra’ila
suka yi Imani da shi, kuma ni ma ina daga cikin musulmi! (Allaah ya ce): A
yanzun ne, alhali ka yi ta saɓo a baya, kuma ka kasnce a cikin maɓarnata?!!
(Surah Yuunus: 90-91).
Waɗannan duk bayanai ne a kan cewa: Tuba daga zunubi da
komawa ga Imani a lokacin mutuwa ba ya yin amfani ga mai aikata shi, matuƙar
dai ya bari har sai da ransa ya zo fita.
Faɗakarwa: Wannan bai ci-karo da hadisan da muka ambata ba a
Tambaya ta 280 ba cewa: Kalmar Shahada tana amfanar wanda ya faɗe ta a lokacin
mutuwarsa! Domin a cikin waɗancan riwayoyin rai bai kai ga maƙoshi ba ne, kuma
mutumin bai kai ga ganin Mala’ikan Mutuwa gar-da-gar ba.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.