Ticker

6/recent/ticker-posts

Ambassador MZ Anka Magajin Garin Anka

 

Ambassador MZ Anka Magajin Garin Anka
Allah SWT ya yi wa Ambassador MZ Anka, Magajin garin Anka, Jihar Zamfara rasuwa a Ranar Juma'a, 29/12/2023. Mai shekaru 81 a duniya, kafin rasuwar sa ya halarci Makarantar Middle ta Sakkwato (Nagarta College, Sokoto ta yanzu) da Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria inda ya samu Digirin sa na farko. 

Ya taɓa riƙe muƙaman Di'o(District Officer) a ƙarƙashin N'e(N. A /Native Authority), Jekadan Nijeriya a Libya da kuma Minista a lokacin mulkin Marigayi Janaral Sani Abacha. Shi ne Ɗantakarar Mataimakin Gwamnan  Jam'iyyar GNPP  a Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara States) Dr. Bello Haliru Mohammed a Zaɓen Shekarar 1979 wanda Marigayi Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa da Mataimakin sa Dr. Garba Nadama suka lashe. Shi ne Ɗantakarar Gwamnan Jam'iyyar PDP na Jihar Zamfara a zaɓen shekarar 1999 wanda Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura na Jam'iyyar APP ya lashe. Ya bar matan aure 2, 'yaya/ɗiya 13, Maza 7, Mata 6 da jikoki da dama. Allah ya jiƙan sa da rahama, amin. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments