Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yaya Zan Gane Saurayin Da Ke Sona Ko Nake So Yana Da Dabi'u Nagari?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam ga tambaya, ya mace zata gane miji nagari? kamar a zamanin nan zakaga maza suna Neman aure idan ka nuna musu kafison miji mai addini sai su zagaye basa kokarin gyarawa su zama nagari ko kuma su dawo kamar na Allah a baki, amma da zarar an yi aure shikenan sai a koma ba tsoron Allah, meye shawara, jazakallahu khairan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله

Yar uwa muna masu jinjina da kuma yi maki murna da har kike da irin wannan tunanin na son sanin miji mai dabi'u nagari a lokacinnan da ba abinda muka budewa ido face Kuɗi, tabbas zaɓen miji nagari shi ne mafita gareku yan uwanmu mata, miji nagari shi ne zai nuna miki hanyar tsira gobe kiyama. Ba karamin dace bane ga yar uwa ta samu uban 'ya'yanta nagari mai riko da addini da dabi'u nagari.

To amma kafin sanin halaye ko dabi'un namiji nagari bari mu fara dake yar uwa.

Da farko dai a matsayinki na yarinya ko mace mai son samun mijin aure mai halaye nagari to kema dole ne ki zamo mai halaye nagarin. Ki kasance mace mai tsoron Allah, mai kamun kai, mai riko da addini da dai duk sauran halayen mutunen kirki. .. Ki kasance mai yawaita yin addu'o'in neman miji nagari da kuma bawa Allah zaɓi a karshen tahiyarki da kuma cikin sujadah.

Abubuwan Da Ya Kama Mace Ta Duba Ga Namiji

Sai halayen da ya kamata mace ta duba a wajen wanda take so ko yake son ta

Na farko kuma babba daga cikinsu shi ne; Mutum mai riko da addini, wannan shi ne yafi zama alkhairi ga mai neman aure namiji ko mace da yayi dubi zuwa gare shi, mutumin ya kasance musulmi mai riko da addini da aiki da koyarwar addinin musulunci a harkokinsa na yau da kullum. Ita macen wani daga cikin yan uwanta zasu yi mata wannan binciken saboda kaucewa fitina. Wani babban abin duba ga mutum shi ne Sallahrsa, duk wanda baya kiyaye dokokin Allah to tabbas ba zai kiyaye dokokin wasu ba. Saboda haka yar uwa kinga idan kika yi duba ga saurayi mai addini to tabbas ba zai zalunce ki ba. Mutumin kirki ba zai cuci matarsa ba, ba zai daketa ba kuma ba zai rinka quntata mata. Suratul baqarah [2:221] tana nuna mana cewa: " Bawa mumini yafi alkhairi akan kafiri ko mushriki wanda ba bawa ba

وَلَا تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ وَلَا تُنكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤْمِنُوا وَلَعَبْدٌ مُّؤْمِنٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ أُولَٰئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ وَاللَّهُ يَدْعُو إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ وَيُبَيِّنُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Kuma kada ku auri mata mushirikai sai sun yi ĩmani: Kuma lalle ne baiwa muminaita ce mafi alheri daga ɗiya kafira, kuma ko da ta ba ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmani, kuma lalle ne bawa mumini shi ne mafi alheri daga da mushiriki, kuma ko da ya ba ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gafara da izninsa. Kuma Yana bayyana ayoyinsa ga mutane; tsammaninsu suna tunawa. (Suratul baqarah aya 221)

Haka kuma a cikin suratul Hujrat aya ta 13 tana nuna mana lallai wanda yafi wani daga cikinmu a wajen Allah shi ne wanda yafi tsoron Allah.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُم مِّن ذَكَرٍ وَأُنثَىٰ وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا ۚ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِندَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ

Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabĩloli, domin ku san juna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne, Mai ƙididdigewa. (suratul Hujrat aya ta 13)

Haka kuma a suratul Noor aya ta 26, tana nuna mana cewa lallai mata nagari na maza nagari ne.

الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ أُولَٰئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ

Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma miyagun maza domin miyagun mata suke kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. waɗancan su ne waɗanda ake barrantawa daga abin da (masu ƙazafi) suke faɗa kuma suna da gafara da arziki na karimci. (suratul Noor aya ta 26)

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace; " Idan wanda kuka yarda da addinsa da dabi'unsa yazo neman aure wajenku ku aura masa. Idan baku yi hakan ba, to ɓarna mai yawa zata kasance a bayan kasa. Tirmizi ya ruwaito shi.

Wani bawan Allah ya je wajen Hasanul Basri yace, "Ina da 'ya wacce nake son ta, jama'a da yawa suna son ta. Wa zan aurarwa? Bani shawara?" Sai Hasanul Basri yace, "Ka aurar da ita ga mai tsoron Allah idan yana son ta. Sai ya karrama ta. Idan kuwa baya son ta ba zai zalunce ta ba" (Saboda tsoron Allahn sa) Taudhihul Ahkam 5/237.

To yar uwa idan kika dubi Waɗannan maganganu daga ayoyin al-qur'ani da hadisai, akwai wasu da dama da bamu kawo ba, amma Waɗannan kaɗai zaki ga cewa ana kwadaitar damu zabar mutum mai riko da addini idan za'a aure.

To sai kuma wasu dabi'u ko halaye wadanda zaki iya dubawa; ana iya duba gidan dattako, idan mutum biyu sunzo nemanki kuma duk suna da riko da addini to sai ki duba wa yafi zama daga gidan dattako. Yana da kyau ki dubi mutum wanda ya dogara da kansa wato mai abin yi wanda zai iya daukar dawainiyarki,; ciyarwa, shayarwa, tufatassuwa da sauransu. Mutum mai dabi'u nagari maras rigima. Mai ilimin qur'ani da sunnah idan an samu, amma kada kice dole sai mai tarin ilimin alhali kuma bai zo ba.

Ya halatta idan mutum zai nemi mace ya kalleta amma kuma kallo wanda bai wuce iyaka ba. Kuma ya kasance a gurin akwai muharraminta. Kuma ba koda yaushe yana wajenki ba sai da dalili, duk wadannan yawan hirace-hiracen laifi ne.

Kina iya duba zuwa ga mutanen da yake hulda dasu shin yaya suke?

To a lokacinda hankalinki ya kwanta ga saurayin sai kiyi istikhara ki nemi shawarah daga mutanen kirki, insha Allahu ba zaki yi nadama ba. Sa'annan ki sani idan kina son miji nagari to kema dole ne ki zamo tagari, saboda haka sai kiyi kokari ki zamo tagari domin samun miji nagari.

Jan Hankali Zuwa Ga Yan Uwa Mata Masu Cewa Lallai Sai Mai Kuɗi Suke Son Aura, Wasu Ko Mai Kuɗin Kuma Saurayi

Saurayi nawa suke da kuɗi a lokacinda suke samarin????

To idan har kuɗin kike so kin manta duk da wancan kiran dake a sama to kiyi nazarin wadannan tambayoyin dake a kasa

Shin wanda ke sonki ko wanda kike so, me yake yi? Wato yana karatu ko ba yayi? Yana sana'a ko ba yayi? Idan kika samu amsa to sai ki kwatanta ki gani shin kuɗi suna zuwa ne lokaci ɗaya ko yaya?

Shin nawa ne daga cikinmu muka taso a gidajenmu munsan cewa harda wayonmu iyayenmu basu da kuɗi, amma kuma daga baya sun samu kuɗin?

Shin bamu la'akari da cewa da yawa daga cikinmu mun taso munsan cewa iyayenmu suna da kuɗi amma kuma yanzu ba kuɗin?

Shin meye amfanin kin bi kuɗi, kinje kina faman shan walakanci gun mutum maras riko da addini?

Shin yar uwa kin yanke kauna kenan duk wanda baya da kuɗi a yanzu shikenan ba zai samu kuɗi ba ko? Kinsan hukuncin yanke kauna ga Alllah kuwa?

Shin me ya sa yanzu muke ganin ga 'yan mata birjit kowace tana bukatar aure kuma ga samari suma birjit suna bukatar aure kamar su kwata amma kuma ba'a auran sai dai a rinka neman 'yan matan ana lalatawa?

Shin ke yar talaka kice dole sai mai kuɗi ko ɗan babban gida zaki aura tunda dai qawarki ta auri irinsa, shin baki dubin gidansu da naku ba ɗaya ba ne halan?

Ke 'yar talaka 'yar boko ko mai kyau ki sani da yawa daga cikin 'ya'yan attajirai ko kuma masu kuɗi suna nemanku ne harkar banza ba dan aure ba saboda ki masa duk abinda yake so tunda dai yasan kin waye ko kuma dan kyaunki amma kuma baya iya aurenki saboda yana ganin ko yan uwansa suna ganin gidansu bai dace da naku ba. Saboda haka kiyiwa kanki qiyamullaili da cewa lallai sai mai kuɗi ko ɗan mai kuɗi alhali ke yar talaka ce. Ki yi hakuri ki rungumi mai sonki tsakani da Allah.

Da fatan 'yan uwana 'ya'yan talakawa irina zaku fahimce ni da kyau abinda ya sa kuke ganin nafi maida hankalina zuwa gareku shi ne saboda yawanci kune akafi lalatawa, ɓatawa da kuma gurɓatawa rayuwa a irin wannan lamarin.

Daga karshe muna addu'ar Allah subhanahu wata'ala ya haɗa mu da abokan zama nagari. Masu sonmu, tausayawa mana kuma masu riko da addini.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎��👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments